DNN Hausa

DNN Hausa DNN News Hausa: Sahihan Labarai Da Ɗumi-Ɗumi | Bincike | Siyasa | Shirye-Shirye Na Musamman Da Labaran Wasanni Da Na Nishaɗi.

Ku tun-tuɓemu kai tsaye: 08061341152

22/08/2026

Jami'yyar NDC zata yi nasara a jihar Kano yayin zaɓen 2027-- Hon Sunusi Yusuf Kademi

Wacce addu'a ake yi yayin da ruwan sama ke sauka ?
22/08/2026

Wacce addu'a ake yi yayin da ruwan sama ke sauka ?

Mutane huɗu daga iyali guda sun mutu bayan cin amala a garin Ihima, dake ƙaramar hukumar Okehi ta Jihar Kogi.Rahotanni s...
22/08/2026

Mutane huɗu daga iyali guda sun mutu bayan cin amala a garin Ihima, dake ƙaramar hukumar Okehi ta Jihar Kogi.

Rahotanni sun ce karen mamatan ma ya mutu bayan ya ci abincin da mutanen s**a ci, lamarin da ya sa ake zargin yiwuwar gubar abinci ko kuma gurɓacewar abincin.

Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutanen.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce an umurci Ma'aikatar Lafiya ta jihar da ta gudanar da binciken tare da hukumomin da abin ya shafa.

Ya ce za a tattara tare da binciken samfurin abincin da sauran shaidu domin tabbatar da ko abincin ne ya gurɓata ko kuma akwai wani dalilin lafiya ko muhalli da ya haddasa mutuwar.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, a matsayin Amirul Hajji na shekar...
22/08/2026

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, a matsayin Amirul Hajji na shekarar 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Fadar Masarautar Rano, bayan halartar bikin ɗaurin auren ɗan Sarkin, Muhammad Abubakar Isa, tare da bikin naɗa shi sarauta.

Gwamna Yusuf ya ce an zaɓi Sarkin Rano ne bayan Sarkin Gaya, Dakta Abdulkadir Ibrahim, wanya jagoranci tawagar mahajjatan jihar a aikin Hajjin da ya gabata.

Ya ce Sarkin Rano zai jagoranci tawagar mahajjatan Kano a Hajjin 2027, yana mai cewa hakan wani sabon nauyi ne da aka ɗora masa.

Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, da sauran jami'an masarautar sun nuna farin cikinsu kan naɗin, tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan karramawa.

Shugaban Rundunar Haɗin Gwiwa ta Yaki da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu a Kano, Muhuyi Rimingado, ya ƙaddamar da kwam...
22/08/2026

Shugaban Rundunar Haɗin Gwiwa ta Yaki da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu a Kano, Muhuyi Rimingado, ya ƙaddamar da kwamitoci tara domin ƙarfafa yaƙi da matsalar shan miyagun ƙwayoyi da safarar su a jihar.

An ƙaddamar da kwamitocin ne ranar Juma’a, 21 ga Agusta 2026, inda Rimingado ya buƙaci mambobin dake cikin kwamitocin su nuna ƙwazo, jajircewa da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukan su.

Jami'in yaɗa labaran rundunar Lamara Garba, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Asabar.

Muhyi, ya ce nasarar rundunar za ta dogara ne kan irin muhimmancin da kowanne kwamiti zai bawa aikin da aka ɗora masa, yana mai cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi na buƙatar haɗin kai, tsari da ci gaba da jajircewa.

Kwamitocin za su mayar da hankali kan fannoni daban-daban da s**a haɗa da kuɗaɗe, yaɗa bayanai, wayar da kai, lasisi da tantance kayayyaki, sa ido, tattara bayanan sirri, gyaran hali da haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya.

Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da sace masu ibada a wani masallaci da ke yankin Dekara, dake ƙaramar hukuma...
22/08/2026

Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da sace masu ibada a wani masallaci da ke yankin Dekara, dake ƙaramar hukumar Borgu.

Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na rana ranar Juma’a, 21 ga Agusta, yayin da mutanen ke gudanar da Sallar Juma’a.

Ya ce har kawo yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da aka sace ba, bayan ’yan ta’addan sun fara kai hare-hare a ƙauyukan Gidan-Zana da Kpenya kafin su shiga masallacin.

Abiodun ya tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa a harin, yayin da wasu daga cikin masu ibadar s**a tsere zuwa daji.

Ya ce an tura jami’an tsaron haɗin gwiwa zuwa yankin domin gudanar da bincike da kuma fara aikin ceto mutanen da aka sace.

Rundunar sojin Operation Fansan Yamma ta ce ta ceto wani mutum mai shekaru 43 da ’yan ta’adda s**a yi garkuwa da shi a J...
22/08/2026

Rundunar sojin Operation Fansan Yamma ta ce ta ceto wani mutum mai shekaru 43 da ’yan ta’adda s**a yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna, tare da dakile wani harin ta’addanci a Jihar Sakkwato.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya bayyana cewa a ranar 20 ga Agusta, 2026, sojoji sun kai ɗauki bayan samun rahoton sace mutumin a kusa da garin Awon, dake ƙaramar hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Ya ce sojojin sun bi sawun ’yan ta’addan zuwa cikin daji, lamarin da ya tilasta musu barin wanda s**a yi garkuwa da shi s**a tsere. Daga bisani kuma sojojin s**a mayar da mutumin ga iyalansa.

A wani samame da aka gudanar ranar 21 ga Agusta, sojojin tare da sauran jami’an tsaro sun dakile harin ’yan ta’adda a ƙauyen Kwaren Gamba da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa zaɓen shekarar 2027 ...
22/08/2026

Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa zaɓen shekarar 2027 zai zama fafatawa tsakanin ’yan Najeriya da azzalumai.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar shugabannin Kwankwaso National Network (KNN) daga shiyyar Kudu maso Gabas a gidan sa da ke Maitama, Abuja.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba, domin ganin an samu sauyi a ƙasar, yana mai cewa zaɓen 2027 bai kamata a ɗauke shi a matsayin fafatawa tsakanin jam’iyyu kawai ba.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma yi kira ga jama’a kan gujewa sayar da ƙuri’unsu tare da kare ƙuri’ar da s**a kada, yana mai cewa sakamakon zaɓen gwamnan Osun na baya-bayan nan ya nuna cewa ƙuri’u na iya yin tasiri idan jama’a s**a tsaya tsayin daka.

Ana sa ran Sakataren Sojin Ƙasa na Amurka, Dan Driscoll, zai yi murabus daga mukamin sa kafin ƙarshen shekarar 2026, bay...
22/08/2026

Ana sa ran Sakataren Sojin Ƙasa na Amurka, Dan Driscoll, zai yi murabus daga mukamin sa kafin ƙarshen shekarar 2026, bayan watanni ana samun takun-saka tsakaninsa da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth.

Rahoton ya fito ne daga mujallar Wall Street, wadda ta ce ta samu bayanan daga wasu mutane da ke da masaniya kan batun.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce har yanzu bai iya tabbatar da rahoton ba.

Driscoll, wanda ke jagorantar Sashen Sojin Ƙasa na Amurka, ya taɓa musanta cewa yana shirin barin mukaminsa, amma rahoton na baya-bayan nan ya nuna cewa ana sa ran zai bar aiki a ƙarshen wannan shekara ko ma kafin lokacin.

Wane aiki gwamnatin Tinubu ta yi wanda zai sa ku sake bata dama yayin zaɓen shekarar 2027 ?
22/08/2026

Wane aiki gwamnatin Tinubu ta yi wanda zai sa ku sake bata dama yayin zaɓen shekarar 2027 ?

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DNN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Establishment

Send a message to DNN Hausa:

Shortcuts

Share