04/18/2026
SIRRIN RABUWA DA TALAUCI DA IZNIN ALLAH.
Assalamu Alaikum 🤝
Duk irin yadda rayuwa ta yi, maka ƙunci ɗan-uwa ga sirrin da za ayi domin ALLAH ya kawomaka buɗi da wadata ya raba ka da ƙuncin rayuwa
Wannan sirrin yana da, matuƙar sosai. In dai buɗi ka ke so, ga sirrin izawaƙa da sunayen ALLAH ɗari ba ɗaya. Kowa yaje ya yi za aga haske sosai in sha Allahu.
YADDA ZA AYI.
👇👇👇
Ana farawa kowacce rana. Amma sai an kammala komai za a kwanta bacci ake yin wannan sirrin. Za a ɗauro alwala a zauna ba sai lallai an yi nafila ba. Amma idan an yi abun da ake so ma kenan.
Za a yiwa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati ƙafa 100
Sai karanta ayar farko ta suratul waƙi'a ƙafa 99 sai a ɗauki sunan ALLAH na farko a karanta ƙafa 99
Sai a sake ɗaukar ayar ta biyu a karanta ƙafa 99 sai a ɗauki sunan ALLAH na biyu a karanta ƙafa 99
Haka za ayi har a kammala. Dama adadin ayoyin suratul waƙi'a a warshu 99 ne. Sannan sunayen ALLAH su ma 99 ne.
Kullum za a ɗauki da za a iya. Wanda kuma zai iya yi a zama ɗaya sai ya yi. A ranar da aka kammala ayi sadaka da abun da ALLAH ya h**e. Ana yin wannan sirrin sau ɗaya a wata.
In sha Allahu duk irin yadda rayuwa tayi maka ƙunci da ikon ALLAH komai zai warware. ALLAH ya ƙara buɗa mana a kan hanyar neman mu Ameen.
Sadakar wannan sirrin shi ne ayi comment da salatin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ayi share da like domin ƴan-uwa su amfana.