20/08/2026
Halin da hanyar gezawa zuwa ƴanchibi karamar hukumar Tsanyawa take ciki yanzu haka
Al'ummar ƴanchibi suna cigaba da kokawa akan rashin ingantacciyar hanya da take addabar yankin nasu shekaru da dama wannan matsala tana ƙara ta'azzara kullum
Mutanen yankin sun bayyana indai har akayi ruwa to hanyar bata biyuwa ko kaɗan har sai sun jira Kamar kwana ɗaya hanyar ta fara samuwa sannan suke fitowa Domin yin harkokin yau da kullum