10/05/2026
โYan Sanda Sun K**a Karin Mutane Biyar da Ake Nema a Mubi.
Rundunar โyan sandan Jihar Adamawa ta sanar da sake samun nasara a ci gaba da aikin tsaro na "Operation Sanity" da ake gudanarwa a Mubi, inda aka k**a karin wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a ayyukan taโaddanci, fashi, safarar miyagun kwayoyi da rikice-rikicen daba.
Waษanda aka k**a sun hada da Ismail Jauro Musa, wanda ake zargi da hannu a hare-haren daba da s**a jikkata mutane, da Saidu Abdullahi, wanda ake zargin yana safarar miyagun kwayoyi tare da amfani da katin shaidar ษan sanda na bogi domin kauce wa binciken jamiโan tsaro. Sauran sun hada da Adamu Isah, da ake zargi da shiga kungiyoyin daba da rarraba miyagun kwayoyi, sai Wala da Charoki, wadanda tuni suke cikin jerin mutanen da rundunar ke nema.
Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin gano karin masu hannu a lamarin tare da kwato wasu kayayyakin da ke da alaka da laifukan. Haka kuma jamiโan tsaro sun rushe maboyar masu laifi guda tara a yankunan Mubi North da Mubi South.
Kwamishinan โyan sandan jihar, CP. Kabir Umar Hassan, ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da laifuka a fadin jihar.