11/08/2025
π¨ Camavinga a Matakin Karshe: Ko Ya Yi Fice, Ko Ya Bar Madrid!
βͺπ«π· Ko dai ya gamsar da Xabi Alonso a wannan kakar, ko kuma Real Madrid za ta iya neman sayar da shi a kakar gaba β amma Ιan wasan Faransan ya kuduri aniyar nuna kwarewarsa.
βΆοΈ Bayan mummunan kakar da ya sha fama da raunuka har guda huΙu wanda ya hana shi buga wasa tsawon kwanaki 159, Camavinga ya sake samun wata matsala ta jiki wadda za ta sa ya daina wasa kusan makonni biyu, lamarin da ke barazanar hana shi halartar wasan farko na gasar lig ta bana da Osasuna.
βΆοΈ A shekaru 22, ya san wannan ita ce kakar da za ta fi yin tasiri a rayuwarsa a Madrid. Tare da yin ritayar Toni Kroos da kuma barin Modric Ζungiyar, lallai tsakiyar fili na bukatar sabon jagora β kuma Camavinga na son tabbatar da cewa shi zai zama wannan Ιan wasan.
[El Confidencial]