24/12/2023
Sunan group namu. "Crypto mining and airdrops da harshen hausa"
Hmmmm rayuwa kenan ba kowa bane ya fahimta, ƙalilan ne kawai s**a fahimta. Ba lalai sai nayi muku bayani dalla-dalla ba, amma dalilin da zamu kwasa in munyi haƙuri munyi juriya bai misiltuwa.
Menene fa'idar group.
Fa'idar shine. Ayi gamayya a haɗa hannu don cinma buƙata. Misali in project ta samu sai abarma mutun ɗaya, abin da nake nufi da mutum ɗaya anan shine. Duk wanda yake wannan group ɗin zaiyi amfani ne da referral link na wannan wanda aka ayyana. Haka za'ayi ma kowa, in sha Allah.
Wlhi mu an barmu abaya sosai, misali ace matasa 1k ko sama da haka zasu buɗe group su hada kai, sannan ko wannensu ya buɗe YouTube channel, suYi gamayya ma YouTube na mutun ɗaya. Ma'ana kowa yayi subscribing channel na kowa. Sannan ayi duk abun da ya dace su yasu. To wlhi babu shakka za su samu Alkhairi mai tarin yawa a tsakaninsu. Ko da website ne.
Haka zalika harka irin ta Mining, Crypto, airdrops da sauransu. Hatta su TikTok, facebook WhatsApp duk ana biyan kuɗi in kuka haɗa kai.
Duk wani kafa, ana samun kuɗi dashi, sai dai kai baka san yaya zakayi ba.
Mai Yakamata kayi.?
Abin da Yakamata kayi shine, ka natsu kayi tunani mai zurfi game da lokaci da kuma data da kake kashewa ko wace rana.
Harka ta Crypto bata buƙatar ko sisinka , ya zamana kawai kana shiga kanayin abin da aka ce kayi a kullun kamar yadda kullun sai ka shiga facebook, TikTok twitter, telegram da sauransu..
Sannan akwai masana harkan a group, wanda zasu riƙa yin bayani da Hausa game da ko wace irin matsala.
Wasu irin jama'a muke buƙata a wannan group ɗin?
Muna buƙatar waɗanda suke da zeal a harkar domin dole sai da haƙuri, yana kuma ɗaukan lokaci.
Mun fi buƙatar mazaje awannan tafiya, sabi da lokaci. da kuma mutunci. Group ne na kowa na nan.
Ko ka san cewa mutane zasuyi maka kallon mahaukaci?
Tabbas dole kayi haƙuri da jama'a Sannan kayi murmushi, domin dole suyi maka kallo mai son banza, ko kuma mai son ɓaqas, da dai abu makamancin haka.