Shaikh Hamza Musa wagini

Shaikh Hamza Musa wagini Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Shaikh Hamza Musa wagini, Art, Wagini, batsari, Katsina.

Lokacin Matasa Ne Ya Kamata A Gina Lahira Da Kyawawan Ayyuka Kafin Tsufa -Sheikh Abdulhameed Bello ZariaDaga Abubakar Sa...
10/05/2026

Lokacin Matasa Ne Ya Kamata A Gina Lahira Da Kyawawan Ayyuka Kafin Tsufa -Sheikh Abdulhameed Bello Zaria

Daga Abubakar Sani Batsari

A safiyar ranar Asabar, 9 ga Mayu, 2026, Dandalin Matasan Harkar Musulunci na Imam Husain (AS) Zone Katsina ya ci gaba da gudanar da taron ƙara wa juna sani karo na biyu, wanda ke gudana a garin Batsari da ke Jihar Katsina.

Yayin gabatar da maudu’i na farko mai taken “Hadafin Harka Islamiyya da Kuma Hadafin Halittar Ɗan Adam”, Sheikh Abdulhameed Bello Zaria ya bayyana cewa manufar gwagwarmayar addinin Musulunci ita ce ceto ɗan Adam daga azabar wuta zuwa aljanna.

Ya ce matasa su ne ƙashin bayan al’umma, don haka lokaci ne da ya dace su yi amfani da ƙarfinsu wajen gina lahirarsu da kyawawan ayyuka kafin tsufa.

“Lokacin matasantaka lokaci ne da ya kamata matashi ya fahimci ni’imar da Allah SWT Ya yi masa, tare da amfani da ita wajen bautar Allah da kyautata ayyuka,” in ji Sheikh Abdulhameed.

A maudu’i na biyu mai taken “Wajibcin Neman Ilimi da Hanyoyin Samunsa”, Dr. Shu’aibu Muhammad Gashua ya jaddada muhimmancin neman ilimi a rayuwar Musulmi.

Ya ambato maganar Imam Ali (AS) da ke cewa: “Neman ilimi ya fi zama wajibi a kanku fiye da neman dukiya.”

Dr. Gashua ya ƙara da cewa idan mutum ya haɗa ilimi da aiki da shi, hakan kan kai shi ga babban matsayi har mala’iku su riƙa ambaton sunansa a sama.

Haka kuma, a maudu’i na uku mai taken “Neman Aure da Zamantakewar Iyali a Manhajin Ɗan Gwagwarmaya”, Malama Khadija Katsina ta yi bayani kan yadda tsarin aure a Musulunci ya kamata ya kasance.

Ta ce Musulunci bai yarda a yi aure ba tare da fahimta da tattaunawa tsakanin ma’aurata ba, tare da ƙarfafa zaɓen abokin zama mai addini, kamala da ilimi.

A maudu’i na huɗu kuwa, Sheikh Hamza Musa Wagini ya gabatar da jawabi mai taken “Kyawawan Ɗabi’u Makamin Ɗan Gwagwarmaya Zuwa Ga Nasara”.

Ya bayyana cewa akwai buƙatar matashi ya suffanta kansa da kyawawan ɗabi’u har su zama jiki da jini a rayuwarsa.

“Ya zama wajibi mutum ya gyara mu’amalarsa da Allah SWT da kuma hulɗarsa da mutane, ba tare da jin cewa ya fi wani ba,” in ji shi.

Sheikh Wagini ya kuma jaddada muhimmancin kyautatawa iyaye, yana mai cewa duk wanda ya kyautata wa iyayensa, shi ma wata rana za a kyautata masa.

Tun da farko dai, bayan buɗe taron da addu’a, mawaƙan Matasan Harkar Musulunci sun gabatar da majalisi, sannan aka gudanar da salloli da liyafar cin abinci.

An bayyana cewa ana shirya taron ne domin gina shaksiyyar matasa ‘yan gwagwarmaya tare da ƙara kusanta su da harkar Musulunci.

DAGA SAFANA: Anyi saukar dalibai 23 a madarasatul fudiyya safana .Shaikh Hamza Musa wagini,ya Samu halartar wannan gagar...
18/04/2026

DAGA SAFANA: Anyi saukar dalibai 23 a madarasatul fudiyya safana .

Shaikh Hamza Musa wagini,ya Samu halartar wannan gagarumin taro Wanda aka Saba gabatarwa duk shekara .

18/4/2026.
Hamza Musa wagini #

Photos 👇👇

DAGA HAUZAR IMAM MUSAL KAZEEM (AS).:  Darussa nacigaba da gudana a wannan makaranta inda malamai suketa bada kokari waja...
13/04/2026

DAGA HAUZAR IMAM MUSAL KAZEEM (AS).:

Darussa nacigaba da gudana a wannan makaranta inda malamai suketa bada kokari wajan ganin sun bada gwargwadon abunda Allah (T) ya h**e masu na ilimi ga dalibai.

Muna fatan Allah ya sakawa kowa da alkhairy

Shaikh Hamza Musa wagini #
12/03/2026

Daga hauzar Imam musal kazeem (As) wagini.Shaikh Hamza Musa wagini nacigaba da bada karatu a wannan makaranta mai albark...
11/04/2026

Daga hauzar Imam musal kazeem (As) wagini.

Shaikh Hamza Musa wagini nacigaba da bada karatu a wannan makaranta mai albarka da take cikin garin wagini,muna fatan allah ya amfanar damu.

Hamza Musa wagini #
11/03/2026

Daga Masallacin juma'a na garin wagini.Shaikh Hamza Musa wagini ya gabatar da free khudba a masallacin juma'a na garin w...
10/04/2026

Daga Masallacin juma'a na garin wagini.

Shaikh Hamza Musa wagini ya gabatar da free khudba a masallacin juma'a na garin wagini,batsari, katsina state.

Yayin free khudba shaikh ya bayyana nasarorin Muslunci sakamakon jajircewar kasar Iran akan maqiya (America da isra'el ).yayin da shaikh ya bukaci acigaba da saka Iran Cikin addu'a .

Daga karshe sheikh yayi Kira Akan al'ummar Nigeria Akan marawa mujahidai Baya anan kasa nigeria domin Samar da tsayuwar Kalmar Allah ,kamar yadda Iran ta tsayar.

Allah ya karfafi muslunci da musulmi ya kaskantar da kafirci da kafirai.

Hamza Musa wagini #
10/03/2026

😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
30/03/2026

😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

إنا لله وإنا إليه راجعونAn sake samun Rashi a gidan su Malam Ahmad Muhammad sabon gari.A yayin da mahaifinsu Malam Ahmad...
30/03/2026

إنا لله وإنا إليه راجعون
An sake samun Rashi a gidan su Malam Ahmad Muhammad sabon gari.

A yayin da mahaifinsu Malam Ahmad s/gari yake cika kwana 3 da rasuwa ,Allah ya kaddara rasuwar kanwarsu Malam Ahmad a wannan Rana ta litinin 10/10/1446, 30/3/2026,muna fatan Allah yayi Mata Rahman ita da mahaifinta da sauran al'ummar musulmi.

30/3/2026
10/10/1446
Hamza Musa wagini.

إنا لله وإنا إليه راجعون10/10/1446.Shaikh Hamza Musa wagini.
30/03/2026

إنا لله وإنا إليه راجعون

10/10/1446.
Shaikh Hamza Musa wagini.

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.Allah yayiwa mahaifin wakilin hurras na da'irar wagini (Malam Ahmad Muhammad sabon ga...
27/03/2026

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN.

Allah yayiwa mahaifin wakilin hurras na da'irar wagini (Malam Ahmad Muhammad sabon gari )Rasuwa.

Malam Muhammad sabon gari ya rasu a yau juma'a 27/3/2026, 07/10/1446,muna fatan Allah yayi masa Rahma.

27/03/2026.

01/03/2026
Sheikh Sayyid Hamza Musa Wagini ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar matar Malam Sada Imam Wagini.Sheikh sayyid Hamza Musa ...
21/02/2026

Sheikh Sayyid Hamza Musa Wagini ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar matar Malam Sada Imam Wagini.

Sheikh sayyid Hamza Musa Wagini ya kai ziyarar ta’aziyya ga Malam Sada Imam Wagini bisa rasuwar matarsa da ta rasu bayan fama da jinya.

Ziyarar ta gudana ne a ranar Alhamis 19/02/2025, inda Sheikh Sayyid Hamza Musa Wagini ya kai ta’aziyyar ga Malam Sada Imam da sauran iyalan mamaciyar, domin jajanta musu kan wannan babban rashi da ya same su.

Yayin ziyarar, Sheikh Hamza Musa Wagini ya bayyana alhininsa kan rasuwar mamaciyar, inda ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarta.

Haka kuma, ya yi kira ga iyalai da ‘yan uwa da su ci gaba da yin addu’a da sadaqa a madadin mamaciyar, yana mai tunatar da su cewa mutuwa hakki ce ga kowane rai.

Ziyarar ta samu halartar ‘yan uwa da abokan arziki, inda s**a nuna alhini tare da addu’ar Allah Ya bai wa iyalan mamaciyar hakurin jure wannan rashi.

Allah Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata, Ya ba iyalanta hakuri. 🤲

sheikh hamza musa wagini.
21/2/2026.

Address

Wagini, Batsari
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shaikh Hamza Musa wagini posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category