22/12/2025
Kungiyar GACONES Ta Gudanar Da Taron Farko a Jihar Katsina Domin Taimaka wa Matasa Samun Ilimi da Tallafin Karatu na Waje
Kungiyar Guidance and Counseling on Education and Scholarships (GACONES) ta gudanar da taronta na farko a jihar Katsina, wanda aka shirya a ɗakin taro na Pleasant Library da ke kan hanyar Umaru Musa Yar’adua Way.
Taken taron shi ne: “Neman Ilimi Ya Zama Wajibi Ga Kowane Mutum – Wannan Zai Zama Wani Mataki Na Inganta Rayuwa da Sauya Al’umma.” A taron, an gabatar da horo na musamman kan yadda ake samun damar karatu a ƙasashen waje kyauta (scholarship), tare da bayyana nasarorin da kungiyar ta samu wajen taimaka wa matasa na jihar Katsina.
Kungiyar GACONES ta bayyana yadda ta ba matasa dama su samu karatu a ƙasashe kamar Malaysia, Indonesia da Iraq, a fannoni masu muhimmanci da ke da amfani wajen ci gaban al’umma. Haka kuma, kungiyar ta bayyana babban ƙalubalen da ke fuskantar irin wannan shiri, wanda shi ne ƙarancin kuɗin jirgi da na tafiya. Sau da yawa, waɗanda s**a samu scholarship s**an gaza tafiya saboda rashin kuɗin tafiya wanda yakan kai Naira miliyan 1.5, kuma hakan yana jefa dama cikin hasara.
Saboda haka, GACONES ta mika buƙatar tallafi ga gwamnatin jihar Katsina ta hannun wakilin Katsina State Education Scholarship Board, inda s**a roƙi a tallafa musu domin a ceto irin waɗannan damammaki da kuma taimaka wa matasa su cimma burinsu na ilimi.
Taron ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban. Cikin su akwai:
Alhaji Salisu Lawal Kerau daga Scholarship Board na jihar Katsina,
Dr. Abubakar Isah daga ƙungiyar CSACEFA,
Hon. Yusuf Abubakar, shugaban ƙungiyar matasa ta NYCN,
Hon. Sabo Musa Hassan, mai ba Gwamna shawara na musamman kan wayar da kan jama’a (SSA Public Enlightenment),
Da shugabannin dalibai daga dukkan manyan jami’o’in da ke cikin jihar Katsina.
A ƙarshe, kungiyar GACONES ta yi kira ga al’umma gaba ɗaya da su goyi bayan wannan ƙungiya, domin haɗin gwiwa wajen tallafa wa matasa su samu ilimi mai zurfi, ba kawai a Najeriya ba, har ma a ƙasashen waje. Wannan ne zai iya zama ginshiƙin ceto rayuwar su da inganta makomar al’umma.