10/04/2026
Minene mafitar dan Talaka a fage na siyasa a wannan lokaci wannane shine goron juma'armu na yau
Dukkan yabo, godiya da jinjina sun tabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai mai yanda yaso a lokacin da yaso a wajen da yaso. Cikakken Salati ya tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad S A W.
Bayan haka yan uwa matasa diyan talakawa nayi wannan rubutune musamman domin mu, a yau dan talaka shine kuka mai dadin hawa awajen 'yan siyasar mu, kuma mu diyan talakawa munkasa gane cewa ana amfani damu wajen samun damar kaiwa wani matsayi daga baya sai a manta damu har sai wani kakar zaben yazo, ana amfani damu domin cin moriyar demokaradiyya amma sai abarmu a wajen kada kuri'a har sai wani kakar zaben ya zagayo minene dalilin hakan ga kadan daga ciki.
1. Babu samun cikakkiyar tarbiya daga mahaifanmu:- Domin idan da iyayenmu sun bamu tarbiya cikakkiya tabbas da 'yan siyasa basu rika amfani da muba wajen cin zabensu ba sannan su yadar damu bayan biyan bukatarsu, don haka yanada kyau iyaye mu tsare diyanmu sannan mu kulada tarbiyarsu.
Wani zaice miyasa nayi wannan maganar bayan matsan da suke shiga siyasa duk sun shiga ko mallaki hankalinsu, hakane amma idan mukayi la'akari diyan manyan 'yan siyasa basa saka diyansu wajen bangar siyasa sai diyan talakawa miye dalilin hakan, idan diyan nasu s**a shiga wajen hidimarsu zasuce ne kar azabesu saboda bazasuyi maku adalci ba ko kuwa. Amsar itace a'a domin sun san awajen yawon 'yan siyasa sai wanda iyayensa s**a barshi sakaka a tunaninsu fa amma, kuma idan mukayi lura da abinda yake faruwa wajen yawon kamfen zakaga har kudin 'yan g***a ake warewa ma'ana yan shaye-shaye kuma wallahi galibinsu matasane.
2. Babu cikakkun dattawa wanda zasu zama uwayen kasa wanda s**a dauki diyansu da sauran diyan mutanen gari dayane awajensu:- Mai karatu sai yayi tunanin cewa kamar banida kunya ko kuma wata fahimtar tashi ta daban amma fa wannan shine gaskiya, miye dalilin fadan hakan, to gashi:- Duk wani wanda muke tunanin cewa shine amatsayin dattijon gari idan yasamu abu ko kasonsa ne ko ba kasonsa bane tofa sai yayi son kai aciki, bara nabaku wani karamin misali tayadda zaku fahimce ni, kun taba samun labarin wani yabiyawa wani dan talaka kudin makaranta acikin wadannan dattawan garin ko kuma kun tabajin a wajen neman taimako ana cewa akwai yaron gidan wane yanada ilimi yakamata akaishi karatu domin gari ya amfana ko kun tabajin sunje gidan gwamnati walau ta jaha ko karamar hukuma sun nemowa wani dan talaka taimako domin fara karatu ko kuma cigaban karatunsa, babu daya duk sai diyansu ko ba kahaba?
3. Rashin Tunanin matasa akan rayuwarsu da kuma neman mafita akan gobensu:- Matashi musamman wanda yayi karatu wanda akoda yaushe gurinsa shine yasamu aiki kuma neman aikin ya ta'alakan tashi samun nasarar wannan dan siyasa wanda yakeb tallatawa, kuma wannan babban kuskurene mai girma, kuma dalili mai sauki:- ka nema wajen Allah domin shike bayarwa ka saki wannan mutane domin suma mafita suke nema kodayaushe.
Daga karshe ina kira yan uwana matasa diyan talakawa damuyi taka tsantsan waye yake mana soyayya ta gaskiya sannan kuma waye yake mana soyayya ta biyan bukata.
Nagode