18/07/2026
Fitacciyar jarumar Kannywood, Fatima Hussain, ta yi wannan ikirari ne a wajen liyafar (dinner) da aka shirya domin ƙaddamar da sabon fim ɗin WATA SHIDA, wanda ta kasance ɗaya daga cikin jaruman da s**a taka rawa a cikinsa.
A cewarta, ta fito a fina-finai da dama, kuma kusan duk fim ɗin da ta taka rawa a cikinsa yana samun karɓuwa da shahara a wajen masu kallo.
Kalaman nata sun jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masoya Kannywood. Wasu sun ce ikirarin nata na nuna ƙwarin gwiwa da amincewa da baiwarta, yayin da wasu ke ganin nasarar fim ba ta ta'allaka ga jarumi ko jaruma ɗaya kaɗai ba, illa haɗin gwiwar marubuci, darakta, furodusa, sauran jarumai da kuma ƙungiyar da ta shirya fim ɗin.
Kun yarda da ikirarin Fatima Hussain? Ko kuna ganin nasarar fim tana dogara ne da haɗin gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki?