realprincebabson

realprincebabson Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from realprincebabson, Arts and entertainment, Perth, Kano.

27/03/2024

Trying to create something special

15/10/2021

Idan wasu s**ayi abun da bai dace ba mu dinga zagi harda tsinuwa bayan mu abunda muke aikatawa ba daidai bane kuma a hakan mu dinga ikirarin cewa mu musulmai ne wlh karka ga wai Nan social media ne duk abinda ka rubuta sai a tuhumeka a bisa hakan kuma gabobinka sune abin shaidawa a ranar da baki bazai iya furta komai ba Allah yasa dai mu gane

Allahbmun tuba ka dube mu badan halin mu ba kayi mana dan alfarmar annabin ka muna tawassali da soyayyar da kake yi masa...
30/11/2020

Allahbmun tuba ka dube mu badan halin mu ba kayi mana dan alfarmar annabin ka muna tawassali da soyayyar da kake yi masa YA HAYYU YA QAYYU

.racists

08/08/2020

What did you expect to night as Barcelona plays against Napoli.?
To me
.3 .1

Soul mate
28/07/2020

Soul mate

Good morning my fb friends
16/01/2020

Good morning my fb friends

09/01/2020

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*


*Editing is not allowed📵*

*CHAPTER 80 to 81*

Kafun mintuna kaɗan dandazon mutane sun cika kan babban t**in da hatsarin yafaru, kowa salati kawai yakeyi domin kuwa duk wanda yaga yanda motar Zaid tayi ƙwatsa ƙwatsa bazai taɓa tunanin mutumin dake ciki zai fito a raye ba, gaba ɗaya mutane carko carko s**ayi kowa tsoron zuwa wajen motar yake gudun kada wuta ta tashi dashi, domin kuwa har motar tafara tashin hayaƙi, wasu daga cikin mutanen da s**a taru a wajenne s**a taimaka s**a ƙarasa wajen motar, da ƙyar s**a iya zaluƙo Zaid wanda gaba ɗaya fuskarsa ta ɓaci da jini duk jikinsa jini ne, kallon gawa kawai mutanen da s**a ciro sa s**a shiga yi masa, domin kuwa a yanda s**a gansa babu alamar rai ajikinsa, babu kuma alamar cewa zuwa nan gaba zai iya farfaɗowa, sai dai kuma ba'aja da ikon mai sama (ALLAH) Dai dai lokacin motar ƴan sanda s**a ƙaraso wajen, kai tsaye su s**a ɗauki Zaid s**a sanyasa acikin motarsu, direct aka wuce asibiti dashi, duk da suma dai basu da tabbacin cewa yana da rai ko bai da shi....

Emergency aka karɓi Zaid yayinda likitoti s**a shiga basa taimakon gagawa domin kuwa sun gano cewa akwai rai ajikinsa, kawai de yayi mummunar buguwa ne..... Saida s**a share masa jinin dake kan fuskarsa kafun Dr.Bilal ya iya shaida fuskar Zaid ɗin, take hankalinsa yaƙara tashi, tsananin tausayin Zaid ɗin ya kamasa, shin wani irin hali Alhaji Ma'aruf zai tsinci kansa idan yaji wannan mummunar labarin?,,,, haka dai s**ayi iyaka ƙoƙarinsu wajen shawo kan al'amarin sai de kuma duk yanda s**a so yadawo hayyacinsa abun yaci tura, abu ɗaya s**a dogara dashi, idan har baidawo hayyacinsa nan da 3 days ba, to fa lallai akwai matsala.... Kallon sauran abokan aikinsa Dr.Bilal yayi haɗe da soma cire safar hanunsa, ganin haka yasanya suma s**a cire nasu safan, daga nan s**a fice daga cikin ɗakin...

Kallon sauran Doctor's ɗin Dr.Bilal yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya. "Mubashi nanda 24 hour maybe zai yi farfaɗowa, sai de kuma Allah yasa buguwan da yayi bai taɓa masa lafiyan kansa ba"

"Insha Allah kansa bazai samu wata matsala ba, sai de kuma yakamata a nemi ahalinsa a sanar musu" Wani Dr. yafaɗi haka..

"Insha Allah" Dr.Bilal yafaɗi haka ga abokan aikin sa, bayan ya soma laluɓan Numbern Dad ɗin Zaid....

Alhaji Ma'aruf ne zaune a cikin katafaren falonsa wanda yagaji da haɗuwa, gefe dashi Hajiya Sajida ce tazuba tagumi daganinta kasan cewa tana cikin damuwa... "Menene abun ɗaga hankali har haka Hajiya? kinfasan Zaid ba yaro bane shi, kuma faɗuwar gaban nan da k**eji nima inajinsa, sai de kuma....." Maganar Alhaji Ma'aruf ne ya katse sakamakon wayarsa da ta soma ruri alaman shigowan ƙira,,, mamakine ya bayyana akan fuskar Alhaji Ma'aruf ganin cewa Dr.Bilal ne ke ƙiransa,, bayan sun gaisane Dr.Bilal yayi gyaran murya haɗe da cewa Alhaji Ma'aruf ɗin yana buƙatar ganinsa,,, murmushi Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da cewa "Kakuwa ci sa'a ina gida, sai de ka hanzarta zuwa saboda zuwa ɗan anjima zan fita"

Ajiyar zuciya Dr.Bilal ya sauƙe haɗe da cewa "Kayi haƙuri Alhaji amma maganar bata gida bace, Magana ce me matuƙar mahimmanci kuma yana da kyau kazo ɗin"

Cikin ɗaurewar kai Dad yace da Dr.Bilal gashinan zuwa..

Kallon Alhaji Ma'aruf Mom tayi haɗe da cewa "Wayene, kuma me yake faruwa?" atake Mom taje romawa Dad waƴan nan tambayoyin..

"Bansan meye bane, amma idan naje zanji koma menene, Allah yasa dai ba matsalan Zaid bane" Alhaji Ma'aruf yafaɗi haka yana me nufar hanyar fita daga cikin falon nasa..

Da "Ameen" kawai Mom ta amsa masa domin kuwa tun ɗazu takejin faɗuwar gaba, kuma duk taji jikinta yayi sanyi..

Cikin mintuna ƙalilan Dad ya iso asibitin, kallo ɗaya yayimawa fuskar Dr.Bilal ya fuskanci cewa akwae damuwa...

Bayan sun zaunane Dad yakai dubansa ga Dr.Bilal wanda yarasa ta'inama zaifara sanar da Dad ɗin abundake faruwa...

"Inajinka Bilal kaƙirani ƙira na gaggawa sai gashi nazo kuma kayi shiru"

Ajiyar zuciya Dr.Bilal yayi haɗe da gyara zamansa "Bansan ya zaka ɗauki zancen bane Alhaji, amma kuma kasan me rai baya rabuwa da ƙaddarorin rayuwa...."

"Bangane inda maganan ka ta dosa bafa Bilal, inaga zai fi kyau kamin yanda zanfahimta" Dad yafaɗi haka ta hanyar katse Dr.Bilal daga maganan da ya keyi..

Ɗan numfasawa Dr.Bilal yayi haɗe da soma cewa.

"Wato Alhj kamar dai yanda na faɗa ma, ko wani bawa da irin tasa ƙaddaran, dakuma irin yanda take zuwar masa, bazan ɓoye maka ba Alhaji Ma'aruf, ɗazu aka kawo mana Zaid yasamu haɗari, yanzu haka yana accident & emergency munyi iyaka ƙoƙarinmu sai dai haryanzu bai farfaɗo ba, amma insha Allah muna sa ran farfaɗowarsa nan bada jimawa ba"

Tuni Alhj Ma'aruf yacire hula'r dake kansa, salati kawai yakeyi, iya ƙololuwan tashin hankali ya shigesa..... "Ɗana Zaid fa kace Bilal, ɗazu ɗazu fa muka rabu dashi, amma kaduba fuskar da kyau kuwa?" Dad yatambayi Dr.Bilal cike da tashin hankali.

"Ƙwarai Alhj, amma ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai dai dai ta, muje ka gansa domin kuwa zuwa anjima babu wani wanda zamu bari yagansa, saboda yana da buƙatar hutu sosai"
Babu musu haka Dad yabi bayan Dr.Bilal har zuwa ɗakin da Zaid ke kwance tamkar gawa, yayinda aka ɗaure gaba ɗaya kansa da bandage, sannan kuma an saƙalla masa wasu irin na'urori ajikinsa..

Hawayene s**a cika idanun Alhj Ma'aruf alokacin da idanunsa s**ai masa tozali da Zaid kwance kamar gawa,, "wannan wace irin jarabawa ce Zaid ya haɗu dashi, daga wannan sai wannan?" Alhj Ma'aruf yayi mawa kansa tambayar da baida wani me amsa masa ita.... Ganin da Dr.Bilal yayi cewa hankalin Alhj Ma'aruf yatashi sosai, yasanya ya jasa cikin office ɗinsa yashiga ƙarfafa masa guiwa akan cewa insha Allah nanda gobe Zaid ɗin zai iya farfaɗowa, suna kuma sa ran cewa idan ya farfaɗo bazai tashi da wani matsala ba sai de ɗan abun da baza'a rasa ba... Shi dai Alhj Ma'aruf jin Dr.Bilal kawai yakeyi, amma badon yana fahimtar abun da yake faɗa ba, a yanda yaga Zaid kamar gawa shiyafi komai ɗaga masa hankali, yanzu tayaya ma zaije ya fuskanci Hajiya Sajida da wannan magana ?......

Lokacin da labarin hatsarin da Zaid yayi ya'isa cikin kunnen Hajiya Sajida da labisat baƙaramin tashin hankali s**a shiga ba, haka su kazo asibitin damuwa bayyane akan fuskarsu, da ƙyar Dad ya iya rarrashin su, amma duk da haka basu daina kuka ba....

****

Duka hannayenta ta ɗaura akan ƙuncinta, kallo ɗaya zakai mata kafuskanci cewa tana cikin damuwa, saboda lokaci ɗaya rama ta bayyana kanta ajikinta, ita kanta batasan meke damunta ba, sai dai tasan cewa zuciyarta tana ɗauke da damuwa me tarin yawa, takan tsinci kanta cikin wani irin hali idan tatuno da cewa aurenta da Dr.Sadeeq saura ƴan kwanaki ne s**a rage, haka kuma takanjin matsanancin faɗuwar gaba aduk sanda Zaid yafaɗo cikin ƙwanyanta...

Wayarta ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira yayinda sunan Dr.Sadeeq yasoma yawo akan screen ɗin wayar. Cikin sanyin jiki ta ɗaga wayan haɗe da karawa akan kunnenta, cikin muryarta me sanyi tayi masa sallama.

Fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata, tamkar yana a gabanta, "Kitaimaka ki fito ina ƙofar gida" Abun Dr.Sadeeq yafaɗa kenan..

Ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da cewa "gani nan fitowa..."

Tana aje wayar ta fidda wani irin numfashi haɗe da cije laɓɓanta, sai da tayi kusan mintuna 5 a zaune kafun ta miƙe tsaye haɗi da ɗauko wani mayafi ta sanya ajikinta..... Kaitsaye hanyar fita daga cikin gidannasu ta nufa...
Kanta duƙe a ƙasa haka take tafiya, harta ƙaraso wajen da motarsa ke fake..... Hanu tasanya ta ƙwanƙwasa glass ɗin window'n motar kasancewar yana cikin motar baifito ba. Ahankali ya sauƙe glass ɗin windo'n ƙasa, haɗe da sakar mata murmushi,, itama murmushin tayi masa haɗi da buɗe murfin motar tashiga bakinta ɗauke da sallama..

Fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa sallama'n nata, haɗe da kafeta da idanunsa, tun fitowarta agida yake kallonta, sosai kuma ya hango damuwa atattare da'ita.

"Nayi zaton bazaki fito ba kinyi fushi dani" yafaɗi haka still manyan eyes ɗinsa na kanta...

Murmushinta me kyau tayi masa haɗi da ɗan satan kallonsa, sosai yau ɗin yayi mata kyau, gashi fuskarsa taƙara haske sannan sajensa ya sha gyara,
" shima dai gaskiya kyakkyawa ne" tafaɗi haka acikin zuciyarta....

"Mezai sa nayi fushi dakai? nasan cewa hidima ne yayi maka yawa, kuma ae bani kaɗai bace, itama kuma waccar ɗin tana buƙatar kulawa daga gareka, kaga kenan bakayi laifin da zai sanya nayi fushi dakai ba" tafaɗi haka da iyaka gaskiyarta...

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da sake maida hankali da kuma idanunsa a kanta,, tabbas wannan abun da Zahrah keyi kishine, "to idan dai hartana kishinsa kenan tana son sa kamar yanda yake sonta?" tambayar da baiyi da amsarta, bazai yaudari kansa ba, yasani ƙwarai Zahrah batayi masa so me tsanani kamar yanda shi yake mata, amma kuma hakan bazai zamo wani babban abun damuwa a garesa ba, saboda yasani da yardan Allah watarana zata sosa zakumayi tayi masa SON SO...

"Ya aiki?" Zahrah ta faɗi haka ta hanyar katse masa tunanin dayakeyi gashi kuma yasanyata agaba sai kallonta yake kamar yasamu hoto..
Ajiyar zuciya ya sauƙe..... "Aiki babu sauƙi Princess yanzuma cancel ɗin wani aiki nayi nazo, saboda inaga yakamata ace nasan duk wani tsare tsaren da zakiyi, kingafa lokaci yana ƙara matsowa, banaso ayi komai a ƙurarren lokaci"

Murmushi kawai tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, cikin murya me sanyi tace "aini ba wani tsare tsaren da zanyi"

"Meyasa?" yatambayeta ataƙaice.

"Kawai"
itama tabashi amsa ataƙaice, domin ita har ga Allah bata da niyar yin ko wani irin program's ne, ko walima batasa aranta cewa zatayi ba.

"Shikenan to, amma dai nikam zan shirya mana diner, saboda haka ki shirya, zankuma samu Husnah muyi magana da'ita akan yanda tsare tsaren bikin zai kasance sbd na lura kamar ke bason auren nan k**e ba"

Saurin ɗago da kanta tayi ta kalleshi, giransa ɗaya yaɗaga mata yana murmushi..

Turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tayi haɗe da cewa "Nifa bance banason auren nan ba, kawai de banshiryawa program's ɗin bane!" taƙare maganar cike da shagwaɓa ...

Kallonta yashigayi na tsawon wasu mintuna kafun yayi murmushi....

"Meke damunki ne kwana biyu, ko baki da lafiya ne?" ya jefo mata tambayar da bata tsammata ba.

Kallon kanta tashigayi domin tambayartasa ta bata mamaki sosai, "me ka gani?" ta tambaya cike da tsarguwa.

"Naga kin rame ne, ko ba kya cin abinci ne? Ya kuma tambaya cike da kulawa.

Ɗan murmushi tayi haɗe da cewa "inaci"

"To ko dai aure k**eso ne?" yakuma tambayarta.

Saurin ɗago da kanta tayi takallesa saikuma tayi saurin maida kanta tsakan kanun cinyoyinta, wannan magana tasa da matuƙar sanya mutum jin kunya take..

Murmushi yayi har saida haƙwaransa s**a bayyana, dama yafaɗi hakane don yaga kunyarta to gashinan yagani cikin sauƙi...

"Kunyan me k**eji, dan natambaya ko aure k**e so? ae dai naga kamar kin matsu da a ɗaura aurenne" wannan karon cike da zolaya yaƙare maganar..

Murmushi Zahrah tayi haɗe da sake cusa kanta a tsakankanun cinyoyinta, shi dai halinsa ne sanya mutum yaji kunya...

"Ya zamuyi da maganar ɗinkin kine?" yafaɗi haka don son kawar da wancan zancen..

Sai alokacin Zahrah ta'iya ɗago kanta, sai dai kuma bata iya kallonsa ba.

Wani ɗan abu dake manne acikin motar kamar drower yajawo haɗe da ciro wani babban envelop dake aje ciki...
"Kiyi manage da wannan kafun nasake dawowa" yafaɗi haka yana me ɗaura mata envelop ɗin akan cinyarta... Kallon mamaki tashiga yi masa saboda bata fahimci menene acikin envelop ɗin ba. Kansa ya jinjina haɗe da sakar mata murmushi,, ta buɗe baki zatayi magana kenan yayi saurin sanya hanunsa akan laɓɓansa haɗe da cewa "Shiiiii banson kice komai, kije gida zamuyi waya, kinji my beutiful Wife!" yaƙare maganar yana me kashe mata idanunsa ɗaya.

Murmushi kawai tayi masa haɗe da buɗe murfin motar tafice bayan ta riƙe envelop ɗin a hanunta,, yana ganin shigewarta gida shima yaja motarsa yabar ƙofar gidan nasu..

Ajiyar zuciya Zahrah tasauƙe sakamakon ganin irin maƙudan kuɗaɗen da Dr.Sadeeq ya bata,, wayarta tajawo haɗe da dannawa number'n Husnah ƙira, bugu ɗaya Husnah taɗauki wayar haɗe da cewa "Bride"

Murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa "ina buƙatar ganinki Husnah"

"Okay wannan ae ba'abun damuwa bane, bani nan da 30 minute inazuwa"

Cike da jin daɗi Zahrah ta kashe wayan, taji daɗi da Husnah tace gatanan zuwa, domin tabbas tana buƙatar taimakon Husnah.

Kamar yanda Husnah ta faɗa kuwa bawani ɓata lokaci ta iso gidan su Zahrah, Kuɗin da Dr.Sadeeq yabata ta miƙo mawa Husnah,, murmushi Husnah tayi bayan ta gama ƙirga duka kuɗaɗen, domin dai ita dama ƙirga kuɗi baya wani bata wahala, "200,000" Husnah tafaɗa tana kallon Zahrah.

Murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa " Gaskiya ƙawata kin iya ƙirga kuɗi sharp-sharp saikace wata ma'aikaciyar banki!" cike da zolaya ta ƙare maganar,,, dariya s**a sanya su duka biyu...

"Yanzu dai kamata yayi mufara ƴan shirye shiryen da zamuyi, kuma kinga yakamata ace tun yanzu kinfara gyaran jiki" Husnah tafaɗi haka.

"Gyaran jiki kuma Husnah ? to ae ni banga wani aebu ba ajikina da zan gyara" Zahrah tafaɗi haka tana me ƙarewa fatar jikinta kallo..

"Ae basai kinga wani aibu ajikinkiba zaki gyara Zahrah, ke dai yanzu tashi zakiyi muje gidan Auntie Amina takaimu wajen wannan me gyaran amaryan, kinsan tace mana 100,000 ne kuɗin aikinta, so kuma gashi yanzu munsamu kinga babu amfanin yin jinkiri, tashi maza muje" Husnah tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye.

Zahrah ma miƙewa tayi haɗe da janyo mayafinta ta yafa.... Sai da s**a fita har bakin t**i kafun s**a samu taxi s**a shiga direct gidan Aunti Amina (ƙanwar Maman Husnah) s**a nufa, suna zuwa kuwa Auntie Amina tasa babbar ƴarta Suhaima wanda suke sa'anni da Husnah tayi musu rakiya zuwa gidan Hajiya Shuwa wanda itace me gyaran amarya, Hajiya Shuwa dai ƙwararriyar megyaran jiki ne, sosai take gayara mace daga uwar gida har amarya, sosai ta shahara a wannan ɓangaren ta iya gyaran jiki, sannan kuma ingantattun magunguna take haɗawa wanda idan kikasha saikin bada labari, Husnah ce taja Hajiya Shuwa gefe tace tayi mawa Zahrah gyara me kyau sbd ƙaddara yasa tarasa budurcinta, aikuwa babu cutarwa Hajiya Shuwa tace zata gyarata sosai da sosai, duk da abune wanda bazai taɓa yiwuwaba ace tadawo virgin, amma zatayi iyaka ƙoƙarinta taga ta haɗeta ciki da waje.... Hajiya Shuwa ta yankawa Zahrah rana cewa sati uku zasuyi suna gyarata, daga randa aka fara gyarata kuwa to fa fita ya ƙare mata sai dai idan da dare, domin ba'aso rana yataɓa ta... Haka s**a baro gidan Hajiya Shuwa, daga nan Shoprite Husnah taja Zahrah s**a nufa, 100k ɗin da yayi saura Husnah ta ɗauki 50k aciki ta jidawa Zahrah english wears masu kyau da nuna tsiraici, hatta kayan bacci sai da Husnah ta zaɓawa Zahrah, nagani na faɗa irin wanda ake ƙira dashi gwamma babu,, ita dai Zahrah kallon Husnah kawai take, amma takasa cewa komai, haka s**a gama ƴan sayayyansu s**a koma gida, sai da akayi sallan Magrib kafun Husnah tayiwa Zahrah sallama tatafi gida.......

*****

Ƙarfe 3 na yammacin yau kenan amma har yanzu Zaid bai farfaɗo ba, tun da safe ake sa ran farfaɗowarsa amma shiru har zuwa yanzu, gaba ɗaya hankalin Mom atashe yake, gani takeyi tamkar Zaid ɗin ya mutu ne, domin kuwa tun safe take tacewa abarsu su gansa, amma sam likitotin nan sun hanata ganinsa, saboda ba a buƙatar kowa yaje kusa dashi, sai dai idan harshi yafarfaɗo yabuƙaci hakan....

*****

Abu kamar wasa yau kwanan Zaid biyu acikin asibitin amma koda ɗan yatsarsa ne bai motsaba, wannan ne yaƙara jefa ƴan uwansa cikin tashin hankali, bama kamar Alhaji Ma'aruf domin kuwa Dr.Bilal yasanar masa cewa Zaid yakamu da wata irin ciwon zuciya me tsanani, wanda idan har ba'akiyaye ba to tabbas rayuwarsa tana cikin hatsari...

Sama sama yake fitar da numfashi ta bakinsa, yayinda ya soma buɗe manya manyan idanunsa a hankali. gaba ɗaya abun da yafaru dashi yadawo masa cikin kansa, saurin ɗago hanunsa yayi yashafi kansa wanda gaba ɗaya aka ɗaure masa shi da bandage,, dai dai lokacin Dr.Bilal yashigo cikin ɗakin,,, fari'a ne ya faɗaɗa akan fuskar Dr.Bilal sakamakon ganin da yayi Zaid yafarfaɗo....."Alhmdlh sannu yajikin naka?" Dr.Bilal yatambayi Zaid daya kafesa da'idanu.

Bai iya amsa masa ba, sai kansa kawai daya ƙaɗa, lokaci guda kuma yasoma yunƙurin tashi zaune, "Auuushhhhh!" Zaid yafaɗi haka da ƙarfi yana mesanya hanunsa akan ƙafarsa na dama da take masa wani irin raɗaɗi..

"Sannu, kwanta ae basai ka tashiba akwai rauni sosai ajikin ka, musamman ma aƙafarka, saboda haka ka kwanta kawai" Dr.Bilal yafaɗi haka bayan ya ɗaga ƙafar Zaid ɗin na dama ya maida ita gefe saboda akwai ciwuka sosai ajikinta, ko kyakkyawan motsi ba'aso tayi, saboda ciwukan zasuji kamar ana ƙaiƙayasune...

Dr.Bilal yana fita bai jima ba saigasu Alhaji Ma'aruf da Mom sun faɗo cikin ɗakin,,, Mom na ganin Zaid ta fashe da kuka haɗe da ƙarasawa garesa ta kamo duka hannayensa,,, sannu kawai taketa aikin jero masa saikace wanda ya tafito a labour room.Lol...... Da kai kawai yake iya amsa musu sannun da suke yi masa,,, Dr.Bilal ne yakuma shigowa cikin ɗakin. hanunsa ɗauke da wasu magunguna haɗe da allurai... Kallon Mom yayi haɗi da cewa "Hajiya inaga yakamata ace anhaɗa masa ko tea ne saboda akwai allurai da magungunan daya kamata ace yasha, zakuma su iyayi masa illa idan har baici abinci ba,,, jikin Mom harrawa yake tace "Akwai ma abinci likita ae sainabashi yaci ko"

"A'a Hajiya tea yakamata ace yasha idan yaso daga baya saiyaci abincin" kafun ma Dr.Bilal yaƙare maganar Mom tanufi wani ɗaki da aka basu, wanda anan ma s**a kwana, kuma dama akwai kayan haɗa tea wanda Labisat ta ɗauko musu a gida s**ayi breakfast,,, mintuna kaɗan Mom tahaɗowa Zaid tea me kauri, da taimakon Dad Zaid yatashi ya zauna,, Mom dakanta take bashi tea ɗin saboda tsabar soyayya, shikuwa sai wani jan aji yake, idan takawo cup ɗin bakinsa sai yaɗan ɓata lokaci kafun yake buɗe baki yasha.... Ko rabin cup ɗin baishaba yakawar da kansa gefe alaman ya ƙoshi...
Duk yanda s**a so yasha tea ɗin sosai hakan ya gagara, Zaid yana da taurin kan tsiya, idan baiso abuba babu wanda ya'isa sanyasa yayi dole.. Allurai guda biyu Dr.Bilal yayi masa, haɗe da basa magunguna masu kashe raɗaɗi da zafin ciwo.... Jin gina bayansa yayi da jikin pillow haɗe da lumshe idanunsa,, imagine fuskar Zahrah kawai yakeyi acikin idanunsa, kowani bugu ɗaya na zuciyarsa tare da soyayyarta yake tafiya, soyayyar Zahrah yazame masa rayuwa da numfashinsa, soyayyar Zahrah yazame masa jini acikin jikinsa, sai dai kuma baisan meyasa duk kwanan duniya Zahrah take ƙarayi masa nisa ba...

Labisat dake zaune a gefensa taɗan saci kallonsa, akaro na barkatai, tabbas ta fuskanci cewa yayanta yana cikin tarin damuwa, wanda damuwar ita ke haddasa masa faɗawa cikin matsala, amma kuma a iya zurfin hankali da tunanin ta tagano cewa SOYAYYA ita kaɗaice damuwar da take ɗaiɗaita nutsuwar ɗan adam alokaci guda, itace abu mafi saurin ruguza rayuwar ɗan adam, SOYAYYA bata da daɗi ko kaɗan, domin kuwa itama Soyayya ta ɗaiɗaita mata rayuwa batare da ƴan uwanta sun sani ba, har yau abun na ranta, takuma bunnesa acikin zuciyarta, sai dai kuma tana tsoron ranarda asirinta zai tonu, batasan wani kallo iyayenta zasu mata ba...

"Labisat!" Zaid yaƙira sunanta.

Saurin dawowa daga duniyar tunanin da take tayi haɗe da amsa ƙiran da yayi mata.

"Ina wayana?"

Idanu Labisat tashiga warewa ko zata hango wayartasa acikin ɗakin amma bataga ko alamar taba..

"Bro bangantaba sai dai idan su Dad s**a dawo saina tambayesu ko......."
"Enough" Zaid yafaɗa ataƙaice bayan yaɗaga mata hannu.. saboda yasanta yanzu saita cika masa kunne da cakwaikwaiwa.

Gum Labisat tayi da bakinta, haɗe da komawa mazauninta ta zauna, azuciyarta kuwa cewa take "Jarabansa baya taɓa ƙarewa yana a halin rashin lafiya ma amma baifasa gwada halin nasa ba"........

*******

"Gaskiya Doctor yana ƙoƙari sosai Zahrah, kinga yanzufa yakuma turo dubu ɗari da hamsin a account ɗina, kuma kinsan shekaran jiya yaturo dubu ɗari wai kuɗin lalle, nidai nagama gane Doctor ɗin kinnan so kawai yake yajiki a hanunsa"

Murmushi Husnah tayi haɗe da cewa "Nima narasa yazanyi dashi Husnah two days ɗinnan yana min ɓarin kuɗi, idan nayi masa magana kuma sai yace wai amarya dole saida kuɗi"

"Ae kumafa gaskia yafaɗa, kinga dole sai akwai money abubuwa zasufi zama mana dai dai, yanzu kinga gobe nefa za'afara miki gyara yakamata mu kammala abubuwan mu tun ayau.." Husnah tafaɗi haka tana me yafa mayafi ajikinta. Zahrah batakai ga bata amsa ba Momyn Husnah tashigo hanunta ɗauke da wani ƙaton baƙin leda.

"Yanaga duk kunyi carko carko badai harkun gama hutawan ba?" Momyn Husnah ta tambaya, domin dama daga wajen me ɗinki suke shine s**a biyo ta gidan su Husnah akan zasu ɗan huta..

"Eh Momy wlhy kinga yanzu Doctor yaturo mana da kuɗi Banki zamuje mu cire" Husnah tafaɗi haka ga mamanta.

"Ummm zancenki dai baya wuce na kuɗi ako da yaushe, wato shine Zahrah kika biyewa wannan mai idon kuɗin kuketa ƙwaƙule wa bawan Allah aljihun sa ko?"

Dariya Husnah da Zahrah s**a sanya ƙwarai maganar Momy'n tabasu dariya.

"Momy wllhy ba haka bane, shine ma yake turowa ko tambayansa ma bamuyi ba" Zahrah tafaɗi haka tana murmushi..

Murmushi kawai Momy tayi haɗe da cewa "Aekuwa kun dai haɗu da ɗan arziƙi ne, amma angwayen yanzu ae basa ba da wani kuɗi me yawa,,, ungo wannan saikiyi maleji ko" Momy tafaɗi haka tana me miƙowa Zahrah ƙatuwar ledan dake riƙe a hanunta..

Idanu Zahrah ta waro ganin irin girman ledan amma kuma Momy tana cewa wai tayi maleji...

Husnah ce tayi saurin karɓan ledan haɗe da soma fito da kayan ciki, wasu tsala tsalan laces ne guda uku masu kyau da tsadar gaske, sai kuma wasu haɗaɗɗun kuloli masu kyau har guda uku, kuloline irin wanda s**a amsa sunansu kula wanda gidan masu da akwai suke amfani dasu, dagani kai kasan kulolin sunja naira.. Daɗine yakama Zahrah har batasan sanda ta faɗa jikin Momy ta rungumeta ba, sai kuma ta saki kuka.

"Kuka kuma Zahrah? share hawayenki wannan ai ba wani abubane da zai sanyaki kuka ba, kamar ɗiyata Husnah haka na ɗaukeki, share hawayen kinji" Momy takare maganar cike da lallashi.. Godiya sosai Zahrah tayimawa Momy wanda bazai faɗuba, sosai kyautan momy'n yafaranta ranta domin kuwa kayane na alfarama daga kan laces ɗin har zuwa kan kulolin....

Momy nafita Zahrah ta rungume Husnah cike da jin daɗi..

Murmushi Husnah tayi haɗe da cewa "Ƙawata yanzu ba lokacin godia bane, dare zai mana idan bamuje bank ɗinnan ba" dariya Zahrah tasanya, domin ita wani lokacin Husnah daria take bata, komai yinsa take a gaggauce gaba ɗaya tafi kowa ƙosawa ayi auren...

Koda s**aje Bank basu wani shawahala ba s**a cire kuɗin, daganan kuma gidan su Zahrah s**a dawo,,,, suna dawowa s**a samu Inna tamusu ɗan wake, aikuwa ba ɓata lokaci s**a shiga loda mawa cikinsu. suna gamawa kuwa Zahrah tashiga haɗa abubuwan buƙatanta domin gobe da sassafe zata je gidan Hajiya Shuwa bakuma zata dawoba sai 7 na dare, haka ƙa'idan gyaran nasu yake sam ba'aso rana yana dukanka, saboda zafin rana zai iya ɓata gyaran da s**a soma batare da sun kammala ba..........

*8/january/2020*

*Follow me on Whatsapp and Wattpad*

*(Kutaimaka kusani a addu'arku please)*

*Fatymasardauna*

Za ku iya samun litattafan da Marubutan Kainuwa s**a rubuta a wannan feji

09/01/2020
To get hot latest music acros.nigerian follow our page Or youtub chanelhttps://youtu.be/HPtPBvZLGDI
09/01/2020

To get hot latest music acros.nigerian follow our page
Or youtub chanelhttps://youtu.be/HPtPBvZLGDI

Ku kalli sabuwar wakar breaker Karku manta pls ku danna mana subscribe domin samun sabbin wakoki

Address

Perth
Kano

Telephone

+2348062707048

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when realprincebabson posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Establishment

Send a message to realprincebabson:

Share