Taskar Nishadi

Taskar Nishadi Tashar dake baku nishaɗi ba kakkautawa

22/05/2026
01/04/2026

Tsohon dan takarar gwamnan Kano kuma dan jam'iyyar ADC a yanzu, Salihu Tanko Yakasai, ya kalubalanci zargin cewa shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na kokarin mayar da Kano jiha mai jam’iyya daya ta hanyar dabarun siyasa.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Yakasai ya ce wannan fahimta kuskure ce, yana mai jaddada cewa Kano ba ta taba zama jiha mai jam’iyya daya ba tun daga zamanin NEPU har zuwa lokacin Santsi da Tabo, acewarsa Kano ba irin Lagos ba ce.

Ya ci gaba da cewa al’ummar Kano sun ginu ne kan siyasar kishin al’umma da tsayawa akan gaskiya, wanda ya danganta hakan da koyarwar MalamvAminu Kano.

Salihu Tanko, ya soki yadda aka rika karkatar da aiyukan raya kasa da nade-naden manyan mukaman gwamnatin ga wata Kabila guda daya, inda ya ce me aka yi wa Kano da zaisa Tinubu yayi tunanin kowa sai ya goyi bayansa?.

A cewarsa, biyayya ga shugabanci na samuwa ne ta hanyar adalci da kyautatawa, ba ta hanyar dabaru ko tilasci ba.

Yakasai ya yi gargadin cewa idan aka ci gaba da watsi da bukatun al’ummar Kano, za su mayar da martani ne ta hanyar akwatin zabe.

27/03/2026

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo yayi murabus daga kan muƙaminsa.

Ƙungiyar Kwankwasiyya ce ta sanar da hakan, inda ta ce mataimakin gwamnan jihar Kano ya miƙa takardat murabus din nasa.

Sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar, Dr. Habibu Sale Mohammed ya fitar, ta ce an ɗauki matakin ne saboda tabbatar da zaman lafiya da kuma bai wa ofishin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Shin menene ra'ayinku?

23/03/2026

Matashi a tafiyar Kwankwasiyya, Alh. Musbahu Baffa, da ake kira da Na Yar Talla, ya ce akwai rashin hankali da rashin tunani kayi tunanin wani zai rike maka amana, a daidai lokacin da kai kaci amanar wanda ya amince maka.

Shin ko me matashin yake nufi?

Address

Kano

Telephone

+2347035831091

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskar Nishadi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Establishment

Send a message to Taskar Nishadi:

Share