Sarakunan arewa

Sarakunan arewa Wannan group anbude shine domin muringa kawo muku labarai akan masarautunmu na arewa
(1)

SARKIN MISAU
18/07/2026

SARKIN MISAU

18/07/2026
18/07/2026

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

WARAKA DAGA YAWUN BAKINSA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)

Imamun Nisa'iy ya ruwaito hadisi ta hanyar. Muhammad bn Ha'dib (radhiyalLahu anhu) yace :

"Lokacin ina yaro tukunya ta ta'ba kifewa ajikina har sai da fatar jikina ta ƙone baki ɗaya. Sai babana ya daukeni ya kaini wajen Manzon Allah (S.A.W). Sai Manzon Allah (S.A.W) yayi mun tofi akan fatar jikina kuma ya sanya hannunsa mai albarka ya shafi duk wajen konewar sannan yace :

أذهب البأس رب الناس

(Ya Ubangijin mutane ka tafiyar da wannan ciwon)

Nan take na warke na dawo kalau babu sauran ciwo ko ƙuna atare dani.

Imam Allamatuz Zarqaniy da yazo sharhin wannan hadisin acikin sunanut Nisa'iy sai yace :

"Hakika wutar nan ta mutanen Farisa ta mace saboda albarkar Annabinmu (S.A.W) alhali ta kasance sama da shekaru dubu (1,000) bata ta'ba mutuwa ba.

Aduba :

- MUSNAD NA TAYYALISIY (juzu'i na 2 shafi na 518 hadisi na 1290).

- SUNANUL KUBRA TA NISA'IY (juzu'i na 9 shafi na 81 hadisi na 9944).

- MU'JAMUL KABIR NA TABARANIY (juzu'i na 14 shafi na 134).

- ALMUSANNAF NA IBNU ABI SHAIBAH (juzu'i na 7 shafi na 407).

- MAJMA'UZ ZAWA'ID NA HAITHAMIY (juzu'i na 5 shafi na 135 hadisi na 8453)

- Hafizul 'Iraqiy da Hafiz Ibnu Hajr Al Asqalaniy sun ingantashi kamar yadda Hafiz ibn Hajr Al Haithamiy ya fada.

Salatin Allah da amincinsa dawwmammu su Qara tabbata bisa Jagoran Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da mabiya bayansu da kyautatawa hae zuwa ranar sakamako. Ameen.

Ya Allah albarkacin wannan salatin ka sanya wannan sabuwar shekarar ta zamto shekarar yayewar damuwa garemu, da samun waraka daga chutattuka, da yayewar bala'o'i da daukakar darajoji da gyaruwar al'amuran rayuwa baki daya.

Ameen YA HAYYU YA QAYYUM.🙏

18/07/2026
18/07/2026

Address

Kano Bichi
Kano

Telephone

+2348060000000

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sarakunan arewa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share