Arewa Hausa Online

Arewa Hausa Online The page was establish to showcase Hausa Language to the world

Hello Nigerians
01/10/2025

Hello Nigerians

Leda Tana Daya Daga Cikin Abinda Ke Janyo Ambaliyar Ruwa a Najeriya inji Hajiya Zubaida Umar Daga Bello Ahmadu Alkammawa...
31/07/2024

Leda Tana Daya Daga Cikin Abinda Ke Janyo Ambaliyar Ruwa a Najeriya inji Hajiya Zubaida Umar
Daga Bello Ahmadu Alkammawa
Ganin damina ta fadi a mafi yawancin jihohin dake Najeriya, Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa Da Kiyaye Aukuwar Annoba Ta Kasa karkashin jagorancin Hajiya Zubaida Umar ta dauri damarar fuskantar kowacce irin barazana da matsalolin ambaliyar ruwa zai kawo a kasar, ta hanyoyin wayar da kan al'umma domin su ba da ta su gudumuwa ta hanyar yashe magudanar ruwa da kuma sanya idanu sosai wajen ganin yara da sauran mutanen dake unguwanni da karkara da kuma birane sun daina jefa ledodi a magudanar ruwa saboda yin hakan yana daya daga cikin abubuwan dake janyo ambaliyar ruwa a kasarnan.
Da take tattauna da Sashen Hausa na Gidan Rediyon BBC Landan, Hajiya Zubaida ta bayyana cewa ana hasashen cewa Jihohi 33 da Kanannan Hukumomi 135 ne za su fuskanci ambaliyar ruwa a wannan shekara da mu ke ciki. Ta bayyana cewa duk da yake ba dukkanin jihohin dake Najeriya su ke da ofisoshin hukumar ba, wannan bai hana mutane su kasance cikin shirin ta kwana musamman wuraren da s**a saba da wannan matsalar kowacce shekara, ta kuma nemi ofisoshin hukumar na jihohi da su kasance cikin shiri domin fuskantar matsalar idan ta taso ka da su yi kasa a gwiwa har sai matsalar ta riske su. Ta bayyana cewa aikin hukumar ya hada da tallafawa da kuma wayar da kawunan al'umma dangane da matsalolin ambaliyar ruwa da mak**antan haka.
Gimbiyar ta Mutanen Gwandu ta bayyana cewa tuni Hukumar ta sadu da hukomin Sojojin Ruwa da 'Yan Sandan Ruwa tare da dukkanin ofisoshin hukumar dake jihohin kasarnan inda kowa a yanzu yasan muhimmiyar rawar da zai taka domin samun nasarori akan wannan matsalar da take tafe.
"Muna karbar rahotanni daga jihohin dake da ofisoshin hukumar kowacce rana domin sanin halin da su ke ciki domin sanin irin yadda za mu mayar da su tarihi Insha Allah, bugu da kari yanzu haka muna rike da rahoton hukumomin yanayi da hasashen ambaliyar ruwa saboda haka, musan aikin dake gaban mu, muna kuma cikin shirin ta kwana domin da taimakon Allah mu mayar da matsalar tarihi", inji ta.
Domin sanin halin da su wadannan jihohi da ake hasashen za su samu Iftala'in ruwan sama a wannan shekarar su ke ciki tuni ita da jami'an ta s**a ziyarce su, hasalima sun zagaye dukkanin jihohin kasarnan inda a kowacce jiha s**a sadu da gwamnoni da sarakuna domin su wayar da kawunan al'umma dangane wannan matsalar da hanyoyin da za a bi ta zo da sauki daya daga cikin su itace daina zuba shara a magudanar ruwa, tare da kaucewa sanya ledodi wadanda ke toshe hanyoyin ruwa. Ta kuma sadu da masu sarafa jiragen Kwale-kwale da kamun kifi da dukkanin wanda ke da rawar da zai taka domin kawowa mutane daukin da ya dace domin ganin a kawar da matsalar cikin sauki ta hanyar kaiwa wadanda matsalar ta shafa agaji cikin lokaci. Yanzu haka motocin hukumar dake jihohi a cikin shiri su ke, hasalima hukumar ta samar da rigunan ruwa da sauran kayayyakin da ake nema na agaji a dukkanin jihohin kasarnan musamman inda ake da tunanin afkuwar matsalar.
Gimbiyar ta Mutanen Gwandu ta bayyana cewa tana kokari sosai tare da taimakon Allah wajen ganin ayyukan hukumar a karkashin jagorancin ta sun samar da canje-canjen da za su mayar da matsalolin ambaliyar ruwa da taimakon gaggawa ga mutane tarihi ta hanyar ba da cikakkiyar kulawa ta musamman a kowanne lokaci ba sai a lokacin damina ba, domin ganin wadanda matsalar ta rutsa da su ba su dauki dogon lokaci ba, a sansani da ake samarwa domin fakewa kafin a ciwo kan matsalar ba.
Hajiya Zubaida Umar ta nemi mutanen kasar da su hada hannu da ofisoshin hukumar dake jihohin su wajen kai rahoton da zai taimaka a samu bakin zaren matsalolin ambaliyar ruwa da mak**antan haka idan sun taso cikin sauki.
Alkammawa ya rubuta daga Titin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Kaduna Numbar Salula 07030399110

FASSARAR JAWABIN SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU NA MURNAR CIKAN NAJERIYA SHEKARU 25 A MULKIN DEMOKARADIYA RANAR DEMOKAR...
12/06/2024

FASSARAR JAWABIN SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU NA MURNAR CIKAN NAJERIYA SHEKARU 25 A MULKIN DEMOKARADIYA

RANAR DEMOKARADIYA.12/JUNE/2024.

Ya ku `yan uwana `yan Najeriya bari mu fara da taya juna murnar sake ganin zagayowar ranar Demokaradiya a yau, ranar sha biyu ga watan Yunin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Wannan ranar ta zo dai dai da cikar kasar mu shekaru Ashirin da biyar a cikin mulkin Demokaradiya ba tare da katsewa ba.

A rana irin ta yau, shekaru talatin da daya baya, muka kaddamar da kudirin mu na zamowa al`ummar da ta yi cikakkiyar amincewa da Demokaradiya.

Ba abu ne mai sauki ba, kusan ma cike yake da had`arin gaske ta inda cikin shekaru shida da s**a biyo baya sai da duk muka rikide muka zamo `yan gwagwarmayar kwatan `yancin kanmu a matsayin mu na `yan kasa kuma halittun Allah a ban kasa.

A cikin wannan gwagwarmayar, mun rasa rayukan gwaraza maza da mata. Ciki kuwa har da wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na ranar goma sha biyu ga watan Yunin shekara ta dubu daya da dari tara da casa`in da uku kuma ya zamo tambarin dimukradiyya, wato Cif MKO Abiola, da mai d`akinsa Hajiya Kudirat, da sauran wasu gwarazan irinsu janaral Shehu Musa `Yar Adua da Pa Afred Rewane, duka sun sadaukar da rayuwar su wajen samar wa Najeriya makoma mafi dacewa.

Mu yi jinjinar ban-girma ga mutanen da ba za a manta da su ba, irin su Cif Anthony Enahoro da Chif Abrahama Adesanya da Comando Dan Suleiman da chif Arthur Nwankwo da chif Chukwuemeka Ezeife da Admiral Ndubuisi Kanu da Chif Frank Kokori da Chif Bola Ige da chif Adekunle Ajasin da chif Ganiwu Dawodu da chif Ayo Fasanni da Chif Gani Fawehinmi da chif Olabiyi Durojaiye da Dakta Beko Ransome-Kuti da Chima Ubani da dai sauransu da s**a riga mu gidan gaskiya.

Zai zama an yi tuya an mance da albasa idan aka manta da sadaukawar gwaraza irinsu Alani Akinrinade da farfesa Bolaji Akinyemi da farfesa Wole Soyinka da chif Ralph Obioha da chif Cornelius Adebayo ba, da dai sauran su, mutane ne da s**a jure wa radadi da wahalhalun rayuwar `yan gudun hijira.

A yayinda gwarazan `yan gudun hijirar ke aiki daga nesa don tabbatar da diga-digin dimukradiyya, takwaroroinsu da ke gida Najeriya sun ci gaba da nuna juriya ga matsin mulkin sojoji. Cikin su akwai Olisa Agbakoba da Femi Falana da Abdul Oroh da Sanata Shehu Sani da Gwmna Uba sani da chif Olu Falae da saura jagororin tabbatar da ganin cewa an samar da demokaradiya irin su Chif Ayo Adebanjo da Chif Ayo Opadokun.

Sadaukarwa da gudunmuwar da wadannan hazikai s**a bayar a wannan muhimmin fage, abu ne da ba za a ta6a iya biya ko a manta da shi ba.

Da babu gudumuwar jajirtattun `yan jaridar Najeriya da s**a sadaukar da kafafen yada labaransu wajen isar da amon `yan rajin samar da dimukaradiyya ga duniya, da ba mu yi nasara a akan `yan mulkin k**a-karya ba. Wannan ya sanya a yau za mu mika jinjinar mu ga kafafen yada labarai irin Jaridan Punch da Guardian da National Concord da Tribun da News Tempo da kuma Tell wadanda s**a fusaknci katsalandan din gwamnatocin mulkin-danniya a aiyukansu har ta kai ga daure wasu `yan jaridunsu, ba don komai ba sai don sun nuna dagiya kan `yancin fadin-albarkacin baki ga `yan kasa da kuma tabbatar da nasarar za6en sha biyu ga watan yuni.

Sarkin yawa ya fi sarkin karfi! Duk da tarin karfin mulkin k**a-karya, sannu a hankali sai da aka ci karfinsu har s**a zama tarihi. A nan ne karfin ra`ayi da zabin al`umma s**a nuna cewa suna sama da karfin bindigogi da tankokin yaki da ma duk wata barazanar masu karfi.

A shekarar 1999 Kasar nan ta samu kwato kanta daga hannun `yan k**a-karya hakan ya sa ta zamo kasar Africa mafi yawan al`umma, daya daga cikin kasashe mafi yawan al`umma a duniya, kuma hasken kasashen bakar fata da ke kan turbar Demokaradiya.

Wannan sauyi ya zama wani juyin-juya-hali mai muhimmanci ga tarihin Dan Adam da ba za a taba mantawa da shi ba b***e a ce ya zama kashin-yadawa.

A yau, bayan shekara ashirin da biyar, ga shi muna murnar dawowa wannan gwadabe na mulkinn
demokaradiya.

Bayan dogon nazari da hange, mun tabbatar da cewa Demokaradiya ba kayan aro ko bakon abu ba ce gare mu, don haka ba za mu yi sakaci da ita ko mu tsuke ta zuwa wani abu da ake yi daga lokaci zuwa lokaci ba, ko mu bar ta ta zamo zallar zabe da nsarar wata jam`iya a kan wata ba.

Duk da a wani sa`in, harkokin zabe kan yi k**a da wasan kwaikwayo, sai dai ya k**ata mu sani cewa zabe wani bangare ne na demokaradiya, amma ba dukkanta ba, Demokaradiya wani tsari ne rayuwa da ke nuna yadda ake da zaben ra`ayi ko makoma, don haka, kasa tana iya gudanar da zabe ba tare da tana demokaradiya ba, amma babu yadda za a yi kasa ta yi demokaradiya ba tare yin zabe ba.

Ta hanyar dimukradiyar ne muka raya al`adar gudanar da sahihin zabe a kasar nan, kuma wannan al`adar ta gudanar da zabe a bayyane ita ce ta tabbatar da cewa mun aminta da demokaradiya, kasancewar muna ganin yadda aka mika mulki daga gwamnati zuwa wata zababbiyar ta hanyar demokaradiya ya nuna cewa demokaradiya ta zame mana jini da tsoka.

Ya ku `yan uwana `yan Najeriya, sahihiyar demokaradiya wata fitila ce da take haskaka rayuwar al`ummar da ke karkashinta ta hanyar ba su damar yin `yantaccen tunani, da rayuwar da suke so,ta hanyar da s**a zaɓa muddin bata saɓawa doka ba.

Wasu daga ababen da Demokaradiya ke kyama da inkari sun hada da yaudara ko tilasta wani ra`ayi ga masu mabambanta ra`ayoyi da hange, hasali ma ita demokaradiya a kullum tana maraba da banbance-banbancen ra`ayi da samun saɓanin fahimta, kasancewar Allah Ya halicci mutane daban daban, dole ne kowa akwai yadda yake fahimtar abu.

Demokaradiya ta fi amincewa da yi amfani da tattaunawa da musayar ra`ayoyi a matsayin hanyoyin warware saɓani, maimakon amfani da salon tursasawa.

A yayin da wasu gwamnatocin da ba na dimukradiyya ba ke tilasta wa al’ummar da suke jagoranta ra’ayoyi da manufofin da s**a saɓa da buƙatunsu, ita demokaradiya tana dasa ruhin bauta wa talakawa ne a zukatan shuwagabanni na-gari, ba wai ta mai she su wasu gumaka ababen bautar talakawa ba.

Ya ku ƴan uwana masu kishin kasa. A shekaru ashirin da biyar da s**a shuɗe, Najeriya ta tsinci kanta a tsakanin zaɓin ɗayan-biyu na ko dai ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ƴan mulkin k**a-karya ko kuma ta zaɓi tafarkin da ya fi dacewa da ita. A wancan lokacin mun zaɓi matakin da ya fi dacewa, kuma ya wajaba mu ci gaba da bin wannan mataki a yanzu.

A matsayin mu na ƴan kasa, dole ne mu cigaba da tunatar da kawunan mu cewa, duk rintsi da tsananin da ke cunkushe a demokaradiya, ita din ce dai tsarin mulki ɗaya tilo da ya fi dacewa, dole ne mu san cewa a cikin mu akwai wasu ɓata-gari da ke hanƙoron ganin sun yi amfani da ƙalubalen da ƙasarmu ke fuskanta don su samar da koma-baya ga tafarkin demokaradiyar da muka sadaukar da rayukan mu a dominta, idan ma fa ba su rusa shi baki ɗaya ba.

Wannan shine babban yaƙin da ke gabanmu a yanzu, kuma shine dalilin da ya sa muke bikin Ranar demokaradiya.

Babban makasudin bikin wanan rana bai takaita ga tuna-baya ko kyawawan abubuwan da s**a kawo mu war-haka ba. Eh! Tabbas muna girmama rayuka da dukiyoyin da da aka sadaukar domin dora kasar nan a turbar da ta dace. Ni kaina zakaran-gwajin dafi ne a wannan shafin, tunda da ni aka dauki duk wata kasada ta ganin cewa Dimukradiya ta haifar da da-mai-ido a kasar nan, kuma a yau ni ne kan gaba cikin wadanda s**a girbi abinda s**a shuka a tsagin dimukradiyya.

A matsayina na shugaban wannan ƙasa mai albarka, a dabi`a da dokar kasa duka sun wajabta min tsare mutuncin wannan tafarki na gwamnatin dimukradiyya, kuma na lashi takobin kare `yancinku da walwalar ku a matsayin ku na `yan Najeriya. Kai! A shirye nake na taka duk wata rawar da ta dace wajen yin duk mai yiwuwa domin ganin demokaradiya ta cigaba da zama hanyar rayuwar mu.

Duk da cewa ƙalubalen suna da yawa da tsanani, hakan ba zai hana ni nuna farin cikina na zamowa jagoran kasar nan a wannan lokaci mai muhimmanci ga tarihin demukaradiyar ta ba.

Na gurfana a gabanku ne don na jaddada muku mahimmancin aikin da ke gaban mu a yanzu, hakika aikinmu bai takaita ga jure radadi ko iya tunkaran kalubale da makircin `yan mulkin-k**a-karya ba. Ainihin aikin mu shine tunkarar jarabawar da ke gabanmu ta ganin ko za mu yi kasa a gwiwa mu kasa kare demokaradiya kawai don muna zaton inuwar mulkin- k**a karya ta shude.

A nan, kuma a yanzu da muke tsaka da bikin demokaradiyan mu, ina kira a gare mu da mu sake zage dantse wajen ganin mun cika wani sabon buri wanda shi ma yake da matukar mahimmanci. Wannan buri shi ne cinma nasara a yakin bunkasa tattalin Arizikin Najeriya.

Na san muna fuskantar kalubalen tattalin arzikin mai tsanani.

Tattalin arzikin mu ya yi shekaru da dama yana bukatar garanbawul saboda shiga tsaka mai wuya da ya yi sak**akon an gina shi ne akan tubalin toka har ta kai ya kasa samun daidaito saboda dagaro da ya yi a kan kudaden shiga na man fetur kadai.

Mun bullo da sabbin tsare-tsare da za su gina tattalin arzikinmu a kan kwakkwaran tubali da zai kawo ci gaba mai dorewa, ba shakka, sabon tsarin ya haifar da radadi da matsi, sai dai ba mu da wani zabi da ya rage na gyara ga tattalin arzkin kasa wanda amfaninsa zai karade kowa da kowa nan gaba kadan sai ta wannan hanyar.

A yayin da muka dukufa kan gyaran tattalin arzikin kasa,ina mai jaddada muku cewa na dauki alwashin ci gaba da sauraron ra`ayoyin al`ummar Najeriya kuma ba zan taba juya musu baya ba.

Domin samun mafita mun tattauna da kungiyar kwadago da zuciya daya kuma a shirye muke da mu biya mafi karancin albashi. Kuma nan ba da dadewa ba za mu aike da sabon tsarin zuwa ga majalisar dokoki kasar nan domin su sanya hannu kan matsayar da aka cimma ta zama doka na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

A yayin da kungiyar kwadago ta yi kiran yajin aikin gama-gari, idan kun lura ba mu dauki matakan muzganawa ko kawo sabani a tsakanin kungiyoyin kwadagon k**ar yadda aka saba gani a gwamnatocin `yan mulkin-mulaka`u ba, maimakon hakan sai muka zabi hanyar samin fahimtar juna. Babu wadda aka k**a ko aka yi wa barazana, maimakon haka an gayyaci shuwagabannin kungiyar kwadago inda aka tattauna da su domin samun maslaha ta bai-daya.

Yin amfani da tattaunawa da hawa teburin sulhu sune tambarin demokaradiya, kuma su ne za su ciga ba da zama tsari na wajen mu`amalantar `yan kasa a a siyasar mu ta inganta tattalin arziki.

Na rungumi wannan tafarki ba tare da jin shayi ko son zuciya ba,kuma zan ci gaba da sadaukar da kai na a wannan bangaren har sai mun gina Najeriya mai iya yin adalci ga kowa.

A karshe ya k**a mu sani cewa ba za mu iya isa ga nasara ta hanya mai sauki ba sai ta hanyar da ta fi dacewa.

Tsohon shugaban kasar Amurka Franklin Roosevelt ya yi gaskiya a shahararriyar maganarsa mai cewa: “Tabbas akwai hanyoyi da dama na samin cigaba, amma daya ce a cikinsu mai dorewa”.

Mu tashi tsaye mu hana idanuwanmu bacci, mu cigaba da tafiya kada mu tsaya a tsakiyar hanya har sai mun shaida cikar burin mu na cigaban Najeriya.

Mun san tudun-mun-tsirar mu tsaf, kuma can za mu dosa. Mu hada ƙarfi da ƙarfe wajen ganin mun ɗora Najeriya da ƴaƴanta a jirgin tsira.

Ya Allah Ka ci gaba da yi wa najeriya albarka, Ka kare mana ita da demokaradiyar mu

Ina yi muku murnar zagoyowar ranar demokaradiya!

Ƙungiyar 'Yan Jarida Ta Nada Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Kaduma  Muqamin Uban KungiyaDaga SHEHU YAHAYAKungiyar w...
04/05/2024

Ƙungiyar 'Yan Jarida Ta Nada Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Kaduma Muqamin Uban Kungiya

Daga SHEHU YAHAYA

Kungiyar wakilan gidajen jaridu na ƙasa reshen jihar Kaduna (Correspondents Chapel) ta naɗa shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Alhaji Sani Liman Kila a matsayin uban Ƙungiyar.

Da yake jawabi a wajen taron nadin da ya gudana a ofishin Shugaban ma'aikatan a fadar gwamnatin jihar Kaduna, shugaban kungiyar wakilan 'Yan Jaridar Alhaji Abdulghaffar Alabelewa yace la'akari da irin kauna da gudummuwa da Sani Kila ke ba 'yan jarida a faɗin jihar ne ya sa kungiyar ta karrama shi da mukamin uban Ƙungiyar.

Shugaban 'yan jaridar ya ƙara da cewar 'yan jarida a Jihar Kaduna a yanzu suna gudanar da ayyukan su cikin walwala da natsuwa saɓanin yadda abubuwa suke a baya inda ya bayyana hakan a matsayin kokari na shugaban Ma'aikatan fadar gwamnatin.

A jawabin sa shugaban Ma'aikatan fadar gwamnatin Alhaji Sani Liman Kila ya godewa Ƙungiyar 'yan jaridar bisa ga wannan karramawa da s**a yi mishi, inda ya bada tabbacin yin aiki kafada da kafada dasu.

"Yan jarida mutane masu muhimmanci a cikin al'umma waɗanda suna iya buɗewa da rufewa duk lokacin da s**a ga dama, wannan karramawa da s**a yi mini ta zama abin alfahari a gareni kasancewata mutum na farko da ya samu irin wannan matsayi, ina baku tabbacin kofofin mu za su kasance a buɗe gareku a kowane lokaci".

Wa zai gane wannan hoton?
17/08/2023

Wa zai gane wannan hoton?

10/08/2023

Zuwaga mutanen Arewa

11/07/2023

Slm ya jama'ar Annabi muhammadu SAW

Address

Sultan Bello Road
Kaduna

Telephone

+2348155092812

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Hausa Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Establishment

Send a message to Arewa Hausa Online:

Share

//iconSize: [32, 32], //html: '' }) .bindTooltip(name, { //permanent: true, direction: 'bottom', //offset: L.point(12, 25), //opacity: 0.88, interactive: true }) .bindPopup(name); markersLayer.addLayer(marker); } function getMore() { if (gettingMore) { return; } gettingMore = true; var center = map.getCenter(); $.ajax({ url: "/vicinitysearch", data: { lat: center.lat, lng: center.lng, country: "NIGERIA" } }) .done(function(data) { var added = 0; data.forEach(function(loc) { if (!locationIds.includes(loc.id)) { var mapLoc = {id:loc.id,lat:loc.latitude,lng:loc.longitude,title:trunc20(loc.name),popupHtml:loc.popupHtml,urlPath:loc.urlPath,pictureUrl:loc.pictureUrl}; locations.push(mapLoc); locationIds.push(loc.id); map._addMarker(mapLoc); added++; } }); }) .always(function() { gettingMore = false; }); } map._clearMarkers = function() { markersLayer.clearLayers(); } }); }, 4000); });