12/08/2021
Gwamnati ta fara binciken yadda fuskokin fatara suke a Nijeriya
Ma'aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana wani safiyo da ta ke yi kan yadda fatara ta ke ta fuskoki daban-daban a ƙasar nan (Multidimensional Poverty Index (MPI) Survey).
Minista Sadiya Umar Farouq ce ta ƙaddamar da safiyon na MPI ta hanyar yanar gizo a ranar Talata.
A lokacin ƙaddamarwar, ministar ta ce Nijeriya ta bi sahun ƙasashe da su ka fara inganta hanyoyin su na yanke shawarar gudanar da shirye-shirye ta hanyar amfani da bayanan da aka samu daga binciken na MPI.
Ta ce, “Kowa ya amince a yi aiki da tsarin MPI ne saboda hanyoyi daban-daban da kuma yarjejeniyoyin ƙasashen duniya da aka yi, ciki har da Muradan Cigaban Ƙarni na Duniya, wato 'Millennium Development Goals' (MDGs), waɗanda an maye gurbin su da Muradan Cigaba Masu Ɗorewa, wato 'Sustainable Development Goals' (SDGs) domin su shafo sassa daban-daban na rashi wanda shi ne ruhin fatara da abubuwa masu alaƙa da ita.
“Saboda haka abin farin ciki ne mu tafi tare da sauran muryoyi masu ƙarfi wajen hasko muhimmancin aiki da masu ruwa da tsaki daban-daban a kan yaƙi da fatara, kawar da yunwa, bada nagartaccen ilimi, matakan yanayin ƙasa da kuma rungumar kowa, waɗanda dukkan su muhimman abubuwa ne wajen shaidar da MPI ke samarwa.”
Sadiya Umar Farouq ta lura da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu nasarar inganta rayuwar sama da mutum miliyan 10 ta hanyar fidda su daga matsananciyar fatara ta hanyar ɗimbin shirye-shiryen gwamnatin, waɗanda su ka haɗa da shirin inganta rayuwa na ƙasa, wato 'National Social Investment Programme' (NSIP), da GEEP, Npower, NHGSFP da wasu da dama.
Ta ce, “Wannan muradin ya na yin la'akari da yawan jama'ar da ƙasar nan ta ke da shi yanzu wanda ya kai kimanin mutum miliyan 200, da kuma buƙatar samar da ingantacciyar shaida don tsara shiri.
“Don haka Ma'aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta tsaya tsayin daka wajen yin haɗin gwiwa da hukumomin gwamnati daban-daban, d