01/07/2026
Application dinnan tsaf zai iya chanja maka rayuwa.
Wannan shine Flow Ai, wani Application ne da kamfanin Google s**a kirkira dayawan mutane suna amfani dashi wajen hada vedio comedy ko film.
Kuma suna samun followers harma da kudade da wannan Application din, Kunga Kenan zai iya zama silar chanjin rayuwar mutum
Zaku iya amfani da wannan fasahar wajen yaɗa ilimi ga mutanen da kuke rayuwa dasu kamar yadda zaku gani a kwanakin nan masu koyar da 'English/Grammer' suna yawan amfani dashi, zaku iya tallata kasuwancin ku, nishaɗi, da kuma comedies ku wallafa a social media. Ba wannan kaɗai ba, ana iya editing videos da hotuna acikin sa.
Musamman idan kuna son creating video ana amfani da ChatGPT ne wajen ya baka prompt, zaka yi masa bayanin abinda kake so, idan ChatGPT ya baka prompt, saika ɗauki prompt ɗin ka kaiwa Google Flow ya fitar maka da videon.
Idan kana so ChatGPT ya baka prompt ɗin daya dace, idan zai fidda maka prompt ɗin, kayi masa bayani kamar kana magana kuma kana so ka fahimtar da yaro ɗan shekara 7.
Ni kaina na taba aiki dashi na fara shirin wani film Hamid Da Hamida.
App din Yana nan a app store da Play store da@ zarar kayi searching Flow zaka gashi sai ka dauko shi.