Jarumai24 TV

Jarumai24 TV Wannan shafine domin samun labarai da dumi-duminsa.

NADCEL 2026: Rundunar Mata ta Sojin Najeriya Ta Kaddamar da Motocin Aiki da Aka Gyara, Ta Kuma Dasa Itatuwa a AbujaRundu...
26/06/2026

NADCEL 2026: Rundunar Mata ta Sojin Najeriya Ta Kaddamar da Motocin Aiki da Aka Gyara, Ta Kuma Dasa Itatuwa a Abuja

Rundunar Mata ta Sojin Najeriya (Nigerian Army Women Command - NAWC) ta kaddamar da motocin aiki guda takwas da aka gyara tare da gudanar da bikin dashen itatuwa na farko a matsayin wani bangare na bukukuwan tunawa da Ranar Sojin Kasa ta Najeriya (NADCEL) 2026.

An gudanar da bikin ne a ranar 25 ga Yuni, 2026, a Hedikwatar Bataliya ta Mata ta 1 da ke Giri, Abuja. Shirin ya kasance ne domin kara inganta shirye-shiryen gudanar da ayyukan soji, saukaka harkokin gudanarwa da sufuri, da kuma karfafa bangaren kayan aiki. Haka kuma, yana da nufin ba da gudunmawa wajen yaki da sauyin yanayi da lalacewar muhalli a dukkanin Rundunar.

Babban Bako na Musamman, Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya (Chief of Army Staff - COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu NAM, wanda Babban Jami'in Hulda da Fararen Hula na Sojin Sama, Manjo Janar MA Etsu-Ndagi ya wakilta, ya kaddamar da motocin aiki guda shida kirar Hilux da motocin bas guda biyu kirar Coaster da aka gyara, tare da jagorantar bikin dashen itatu.

A yayin taron, wakilin Babban Hafsan Sojin ya yabawa shugabancin Rundunar Mata ta Sojin bisa wannan kyakkyawan shiri, yana mai bayyana cewa motocin da aka gyara za su kara inganta shirye-shiryen gudanar da ayyukan soji, saurin kai dauki da kuma ingancin ayyukan Rundunar baki daya.

Ya kuma yabawa shirin dashen itatu na farko, inda ya bayyana cewa ya zo a daidai lokacin da duniya ke kara mayar da hankali kan kare muhalli da tabbatar da dorewar ci gaba. A cewarsa, wannan shiri ya yi daidai da manufofin kare muhalli na duniya da kuma manufar Sojin Sama ta Najeriya ta gudanar da ayyukan da ke amfanar al'umma.

Hakazalika, ya ce wadannan ayyuka sun nuna yadda Rundunar ke amfani da albarkatu cikin hikima da kuma jajircewarta wajen inganta walwalar jami'ai da sojoji tare da kara inganta ingancin ayyukanta.

Da yake nasa jawabin, Kwamandan Rundunar Mata ta Sojin, Birgediya Janar MS Adamu, ya bayyana cewa kaddamar da motocin da aka gyara da kuma dashen itatu na farko sun nuna kudurin Rundunar na ci gaba da bunkasa kwarewa a ayyukan soji, kare muhalli da kuma kula da jin dadin jami'ai da sojoji. Ya ce hakan ya yi daidai da falsafar jagorancin Babban Hafsan Sojin Sama wadda ta mayar da hankali kan cikakken shirin ko-ta-kwana, fifita jin dadin soja da kuma goyon bayan manufofin kare muhalli na duniya.

Birgediya Janar Adamu ya bukaci jami'ai da sojojin Rundunar da su rungumi al'adar kula da muhalli ta hanyar tabbatar da cewa an kula da itatuwan da aka dasa domin su girma, yana mai jaddada cewa kare muhalli yana da matukar muhimmanci ga rayuwar al'ummomi da kuma makomar al'ummomi masu zuwa.

A nasa bangaren, wakilin Babban Jami'in Tsare-tsare da Manufofi na Sojin Sama (Chief of Policy and Plans), Manjo Janar JR Lar, tare da sauran manyan hafsoshin soji masu ritaya da masu aiki, sun yaba wa Rundunar Mata ta Sojin Sama bisa aiwatar da wadannan shirye-shirye masu anfani da hangen nesa.

Taron ya samu halartar Manyan Hafsoshin Hedikwatar Soji, shugabannin cibiyoyin Soji da ke yankin Giri, manyan hafsoshin soji masu aiki da masu ritaya, tare da sauran manyan baki.

Wadannan shirye-shirye sun sake tabbatar da kudurin Rundunar Mata ta Sojin ta Najeriya na inganta shirye-shiryen gudanar da ayyukanta, kula da walwalar jami'ai da sojoji, da kuma ba da gudunmawa wajen kare muhalli domin amfanin al'umma da kasa baki daya.

Wallahi nayi tunanin cewa gilashin masu walda ne, ashe gilashin yafi ƙarfin yaro 😁😁Kudinsa $690 dollars, kusan Naira Mil...
19/04/2026

Wallahi nayi tunanin cewa gilashin masu walda ne, ashe gilashin yafi ƙarfin yaro 😁😁

Kudinsa $690 dollars, kusan Naira Miliyan Daya da Dubu Dari Daya kenan fa (₦1,100,000).

Sunan gilashin = GUCCI GG0541S AUTHENTIC Star Oversized Mask.

17/04/2026

Yadda Wasu Al'amura Ke Faruwa a Gidan Soja, Saurara Ku Samu Darasi,,,,,,,,,,,

Shin menene ra'ayinku gameda kalaman Atiku Abubakar?
15/04/2026

Shin menene ra'ayinku gameda kalaman Atiku Abubakar?

03/04/2026
Rundunar Mata ta Sojin Najeriya ta Yi Bikin Ranar Mata ta Duniya da Ziyarar Gidan Marayu, Taron Ilimi da Kuma DinnerRund...
09/03/2026

Rundunar Mata ta Sojin Najeriya ta Yi Bikin Ranar Mata ta Duniya da Ziyarar Gidan Marayu, Taron Ilimi da Kuma Dinner

Rundunar Mata ta Sojin Najeriya (NAWC) ta gudanar da bikin Ranar Mata ta Duniya ta shekarar 2026 ta hanyar ziyarar jin kai zuwa gidan marayu, gudanar da taron ilimi (seminar), da kuma liyafar cin abinci a Abuja.

An gudanar da taron ilimin mai taken “Give to Gain” a dakin taro na Lt Gen Taoreed Lagbaja Auditorium da ke Muhammadu Buhari Cantonment, Giri, Abuja. Taron ya haɗa mata sojoji masu aiki da waɗanda s**a yi ritaya, masana daga fannoni daban-daban da kuma baƙi na musamman domin tattauna rawar da mata ke takawa a fannoni na jagoranci, hidima da ci gaban ƙasa.

A cikin wata sanarwa da Mai Taimakawa Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojin Najeriya (NAWC), Manjo Nsima Essien ta fitar, ta ce wannan bikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin rundunar wajen girmama gudummawar mata da kuma ƙarfafa ci gaban su a cikin sojojin Najeriya da ma al’umma baki ɗaya.

Da take gabatar da jawabin buɗe taron, Baƙuwar girmamawa ta musamman, Birgediya Janar SW Aliyu (Rtd), ta yaba wa Sojin Najeriya kan ƙoƙarinsu na inganta jin daɗi da kuma ci gaban sana’ar mata a cikin rundunar. Ta bayyana cewa Ranar Mata ta Duniya wata muhimmiyar dama ce ta nuna girmamawa ga juriyar mata, nasarorin da s**a samu, da kuma muhimmin rawar da suke takawa a rundunar soji da ma cikin al’umma.

Ta kuma ƙarfafa gwiwar mata sojoji da su ci gaba da kasancewa masu himma, ladabi da ƙoƙarin kai wa ga nasara, tare da karya shinge da kuma bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban ƙasa.

Taron ya ƙunshi gabatar da muhimman muƙaloli guda biyu daga masana a fannoni daban-daban. Mataimakiyar Kwamandan Narcotics (DCN) Oyutu Precious Obiageli daga Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta gabatar da muƙala kan illolin shaye-shaye a cikin rundunar soji, musamman a tsakanin mata. Ta bayyana shaye-shaye a matsayin babbar barazana ga lafiyar jama’a da tsaro a duniya, tare da jaddada muhimmancin wayar da kai da matakan kariya.

A muƙala ta biyu, Dr Vivian Ogbonna ta tattauna kan yadda za a ƙarfafa jagoranci, hidima da kuma gadon alheri na mata a cikin rundunar soji. Ta nuna ci gaban da mata s**a samu a fannoni daban-daban, tare da jaddada bukatar magance kalubale k**ar ƙarancin wakilci a manyan muk**ai, matsalolin da ke cikin tsarin aiki, da kuma rashin isasshen jagoranci da horo.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Kwamandan Rundunar Mata ta Sojin Najeriya, Birgediya Janar MS Adamu, ya taya mata murnar wannan rana tare da bayyana su a matsayin ginshikin ci gaban al’umma. Ya ce bikin na bana ya kasance na musamman domin ya zo ne a ranar Lahadi, abin da ya ƙara masa armashi.

Ya kuma jaddada cewa gudummawar da mata ke bayarwa wajen bunƙasa ƙasa da tabbatar da zaman lafiya na da matuƙar muhimmanci.

Birgediya Janar Adamu ya kuma nuna matuƙar godiya ga Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar W Shaibu, bisa amincewa da bayar da kuɗaɗe domin gudanar da bikin cikin nasara, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai kula da daidaito tsakanin maza da mata wanda ke goyon bayan shirye-shiryen inganta jin daɗi da ci gaban mata a cikin sojoji.

A wani ɓangare na ayyukan bikin, Kwamandan NAWC tare da manyan jami’an rundunar da sojoji sun ziyarci Gidan Marayu na ANAWIM da ke Gwagwalada, Abuja, inda s**a kai tallafin kayan agaji musamman kayan abinci domin tallafa wa yaran da ke zaune a gidan.

A lokacin da s**a isa, Sister Augustina Balogun, Babbar Shugabar gidan marayun, ta tarbe su tare da gabatar da sauran ‘yan’uwa mata masu kula da gidan da kuma bayanin tarihin cibiyar. Ta bayyana cewa kalmar “ANAWIM” ta fito ne daga harshen Ibrananci wadda ke nufin “mafi talaucin talakawa”, tana kuma kula da yara marayu da sauran masu rauni a cikin al’umma.

A nasa jawabin, Birgediya Janar Adamu ya nuna godiya bisa damar da aka ba su na ziyartar gidan marayun da kuma kai tallafin, yana mai cewa wannan alheri ya samu ne da taimakon Babban Hafsan Sojin Ƙasa. Ziyarar ta kuma ƙunshi raye-raye da wakoki da yara s**a gabatar domin nishadantar da baƙin.

Hakazalika, Bataliyar Mata ta 2 ta Sojin Najeriya da ke Nkwagu, Abakaliki, Jihar Ebonyi, ita ma ta gudanar da ayyuka na musamman domin bikin Ranar Mata ta Duniya ta 2026, ciki har da shirin duba lafiyar jama’a da sauran ayyuka da s**a haɗa da mata sojoji, wakilai daga 24 Supply and Transport Regiment, 82 Records Office, 72 Provost Regimental Detachment, matan bariki da kuma ‘yan NYSC.

Bikin ya kammala da liyafar cin abinci (dinner) da Kwamandan NAWC ya shirya domin rufe bikin cikin nasara. Daga cikin abubuwan da s**a faru akwai bai wa masu gabatar da muƙaloli da kuma shugabar gidan marayun kyaututtuka, da kuma ɗaukar hotunan haɗin gwiwa a gidan marayu da wajen taron.








Rundunar Matan Soja ta Najeriya Sun Samu Ƙarin Horaswa kan Jagoranci da Haƙƙin Dan AdamRundunar Matan Sojan Nijeriya (NA...
20/02/2026

Rundunar Matan Soja ta Najeriya Sun Samu Ƙarin Horaswa kan Jagoranci da Haƙƙin Dan Adam

Rundunar Matan Sojan Nijeriya (NAWC) ta kammala cikin nasara Taron Kwata na Farko na shekarar 2026, tare da sabunta kudurinta na ƙarfafa ƙwarewa, bin ƙa’idojin ɗabi’a da inganta tasirin ayyukan mata a rundunar.

A cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Matan Soja, Manjo Nsima Essien ta fitar, ta bayyana cewa ranar ƙarshe ta taron ta kunshi jerin muhimman laccoci daga manyan hafsoshin soja da ƙwararrun masana, inda aka mayar da hankali kan ɗabi’ar aiki, kare haƙƙin ɗan Adam, haɓaka jagoranci da kuma shigar da batun jinsi a ayyukan soja.

Tsohon Manjo Janar MJ Wambai ya gabatar da lacca mai taken “Operational Ethics, Human Rights, and Professional Conduct.” A cikin gabatarwarsa, ya jaddada muhimmancin ladabi, bin ƙa’idojin hulɗa a fagen aiki da kuma kare haƙƙin ɗan Adam yayin gudanar da ayyukan soja. Ya bayyana cewa jagoranci na gari da kyawawan halaye su ne ginshiƙai na tabbatar da amincewar al’umma da samun nasara mai ɗorewa a ayyukan soja.

Haka kuma, tsohon Birgediya Janar BET Bello ya gabatar da lacca mai taken “Leadership, Career Pathways, and Command Opportunities for Female Personnel.” Ya ƙarfafa mahalarta taron da su dage wajen neman ƙwarewa, su jajirce a ci gaban aikinsu tare da shirya kansu domin ɗaukar manyan nauyin jagoranci a tsarin Sojan Nijeriya. Ya jaddada cewa ƙwarewa, gaskiya da juriyar aiki su ne muhimman siffofin da ake buƙata domin samun nasarar jagoranci.

Haka zalika, Dakta Temilola George ta gabatar da lacca mai taken “From Policy to Practice: Applying Gender Mainstreaming Tools in Military Operations.” Ta bayyana muhimmancin aiwatar da dabarun da s**a yi la’akari da batun jinsi wajen tsarawa da gudanar da ayyukan soja. Ta nuna cewa haɗa hangen nesa na jinsi na taimakawa wajen inganta tasirin aiki, kyakkyawar hulɗa da al’umma da kuma kare masu rauni.

A jawabin rufewa, Kwamandan Rundunar Matan Sojan Nijeriya, Birgediya Janar MS Adamu, ya nuna matuƙar godiyarsa ga duk mahalarta taron bisa jajircewarsu da rawar da s**a taka. Ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin dandali da ya haɗa manyan hafsoshin soja da na hukumomin tsaro daban-daban, inda ƙwarewarsu da ladabinsu s**a taka rawa wajen nasarar taron.

Birgediya Janar Adamu ya yaba da haɗin kai da gudummawar mahalarta taron, yana mai cewa ingancin tattaunawa da jajircewar da aka nuna sun nuna ƙudurin NAWC na ƙarfafa haɗin gwiwa, haɓaka ƙwarewa da kuma shirin aiki.

Ya kuma miƙa godiya ta musamman ga kwamitin shirya taron da masu gabatar da laccoci bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da an gudanar da taro cikin tsari da tasiri.

Kwamandan ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ilimin da aka samu da haɗin gwiwar da aka ƙarfafa a yayin taron za su taimaka wajen inganta ayyuka da ƙara tasiri a rundunoni da hukumomin da ke aiki tare da NAWC.








Rundunar Mata ta Sojojin Najeriya Ta Fara Taron Kwana Biyar a Hedikwatar Runduna ta 6 Dake Port HarcourtRundunar Mata ta...
18/02/2026

Rundunar Mata ta Sojojin Najeriya Ta Fara Taron Kwana Biyar a Hedikwatar Runduna ta 6 Dake Port Harcourt

Rundunar Mata ta Sojojin Najeriya (NAWC) ta fara taron horaswa na Kwata na Farko na shekarar 2026 a Hedikwatar Runduna ta 6 ta Sojojin Najeriya, da nufin ƙarfafa rawar da jami’an mata ke takawa a yanayin tsaron ƙasa na zamani.

A wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Sojojin Najeriya, Manjo Nsima Essien ta fitar, ta bayyana cewa taron na kwanaki biyar wanda zai gudana daga 16 zuwa 20 ga Fabrairu 2026, yana ɗauke da taken: “Amfani da Jami’an Mata na Sojojin Najeriya a Yanayin Tsaro na Zamani: Rundunar Mata a Mahanga.”

Da yake buɗe taron a madadin Babban Hafsan Sojojin Najeriya (COAS), Babban Kwamandan Runduna ta 6, Manjo Janar EE Emekah, ya jaddada ƙudirin shugabancin Sojojin Najeriya wajen inganta daidaito tsakanin jinsi, ƙwarewa, da ci gaba da horaswa.

Ya bayyana cewa jami’an mata suna taka muhimmiyar rawa wajen tattara bayanan sirri, hulɗa da al’umma, haɗin gwiwar sojoji da fararen hula, da sauran ayyukan tsaro da ke da matuƙar muhimmanci wajen cimma nasarar aiki, musamman a yanayin ayyukan tsaron cikin gida.

A nasa jawabin maraba, Kwamandan Rundunar Mata ta Sojojin Najeriya, Birgediya Janar MS Adamu, ya ce an tsara taron ne domin ƙarfafa ƙwarewa, ƙarfin guiwa da shirin aiki na jami’an mata a dukkan rundunoni.

Birgediya Janar Adamu ya ƙara da cewa yanayin tsaro mai sauyawa na buƙatar ci gaba da horaswa, daidaitawa da kuma fahimtar rawar da mata ke takawa a tsarin ayyukan Sojojin Najeriya. Ya kuma ƙarfafa mahalarta taron da su yi amfani da damar da aka ba su domin inganta ƙwarewarsu da gudunmawar da suke bayarwa a ayyukan tsaron cikin gida.

Daga cikin muhimman abubuwan da aka gabatar a taron akwai laccoci guda uku masu taken: “Rawar Mata a Samun Bayanai Don Gargaɗin Farko,” “Shirin Aikin Jami’an Mata a Ayyukan Tsaron Cikin Gida na Zamani,” da kuma “Haɗin Gwiwar Sojoji da Fararen Hula da Kare Fararen Hula,” waɗanda manyan hafsoshin soja da s**a yi ritaya – Birgediya Janar TJ Kareem, Kanal OI Mosugu da Birgediya Janar BET Bello – s**a gabatar.

Har ila yau, Manjo Janar A Oyebade (Rtd) ya gabatar da muhimmin jawabi inda ya jaddada muhimmancin shugabanci nagari, ladabtarwa da ƙwarewa a matsayin ginshiƙai wajen ƙarfafa Rundunar Mata. Ya kuma ƙarfafa mahalarta da su rungumi gaskiya, aminci da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu.

Ana sa ran taron Kwata na Farko 2026 zai ƙara ƙarfafa ƙudirin Sojojin Najeriya na gina runduna mai haɗin kai, ƙwarewa da shirin aiki domin tinkarar ƙalubalen tsaro na ƙasa.

Daga cikin abubuwan da s**a kayatar a taron akwai musayar kyaututtuka da ɗaukar hoton ƙungiya.










Taskforce Ta Yi Babban Kamu a Kasuwar Dangwaro Jihar Kano, Ta Kwace Magungunan Bogi na Naira Biliyan 1.5Kwamitin Taskfor...
13/02/2026

Taskforce Ta Yi Babban Kamu a Kasuwar Dangwaro Jihar Kano, Ta Kwace Magungunan Bogi na Naira Biliyan 1.5

Kwamitin Taskforce na Jihar Kano kan Tashoshin Mota da Sauran Wuraren Jama’a ya mika magungunan haram da aka kwace da kudinsu ya kai kimanin naira biliyan 1.5 ga Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti ta Jihar Kano (DMCSA) domin ajiya cikin tsaro kafin a lalata su.

Yayin mika kayayyakin, Shugaban Kwamitin, Manjo Adamu Abubakar Usman (Rtd), ya bayyana cewa an kwace magungunan ne daga hannun masu sayar da su a Kasuwar Dangwaro. Ya ce kayayyakin sun hada da magungunan bogi, wadanda aka gauraya ba bisa ka’ida ba, na jabu, wadanda s**a kare wa’adinsu, da sauran magunguna masu illa ga lafiyar al’umma.

Manjo Usman ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa kwamitin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kare lafiyar jama’a da tabbatar da bin ka’idojin lafiya. Ya kara da cewa suna aiki kafada da kafada da shugabannin kasuwanni da sauran masu ruwa da tsaki domin gano da kuma kwace irin wadannan magunguna.

“Wannan wata babbar shaida ce cewa tsarin sa ido namu yana aiki yadda ya k**ata, kuma duk wanda ke kokarin jefa lafiyar jama’a cikin hadari ba za a kyale shi ba,” in ji shi, yana mai gargadin ‘yan kasuwa da masu harkar magunguna da su bi dokoki da ka’idoji, tare da kira ga jama’a da su rika sayen magunguna daga wuraren da aka amince da su kawai.

A nasa bangaren, yayin karbar kayayyakin, Darakta-Janar na DMCSA, Pharm. Gali Sule, ya jaddada kudirin Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da kare lafiyar da rayuwar al’ummar jihar.

“Wadannan magunguna masu hatsari ba kawai haramtattun kayayyaki ba ne — barazana ce ta boye. Suna lalata sak**akon magani, suna kara janyo juriya ga magunguna, suna rage amincewar jama’a da tsarin lafiyarmu, kuma a mafi muni, suna janyo asarar rayuka,” in ji shi.

Ya kara da cewa wannan k**a ya zama gargadi ga duk masu safarar magungunan jabu, yana mai cewa DMCSA tare da Kwamitin Taskforce da jami’an tsaro za su ci gaba da bin diddigi, tona asiri da kuma gurfanar da duk masu hannu a rarraba magungunan da ba su da izini.

Darakta-Janar din ya yaba wa Kwamitin Taskforce kan jajircewa da kwarewa, yana mai cewa kokarinsu ya hana faruwar mummunar illa ga iyalai da dama.

Daga cikin magungunan da aka kwace akwai kwali 199 na Benzhexol Hydrochloride BP 5mg, kwali 5 na CINBUL, Levofloxacin 500mg da sauran magunguna daban-daban.

Mika wadannan kayayyaki ya nuna karfin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano wajen yaki da magungunan jabu da kuma kare lafiyar jama’a a fadin jihar.




'a

NAWC Ta Ci Gaba Da Ziyara Ta Musamman Don Ƙarfafa Haɗin Kai da NAHFC da NAOWAKwamandan Rundunar Mata ta Sojin Najeriya (...
11/02/2026

NAWC Ta Ci Gaba Da Ziyara Ta Musamman Don Ƙarfafa Haɗin Kai da NAHFC da NAOWA

Kwamandan Rundunar Mata ta Sojin Najeriya (NAWC), Brigediya Janar MS Adamu, a ci gaba da ziyarce-ziyarcen da yake yi domin sanin aiki da mu’amala tun bayan karɓar ragamar jagoranci a ranar 29 Janairu 2026, ya kai ziyarar girmamawa ga Cibiyar Tarihi da Makomar Sojin Najeriya (NAHFC) sannan daga bisani ya ziyarci Ƙungiyar Matan Hafsoshin Sojin Najeriya (NAOWA) a ranar Talata, 10 Fabrairu 2026, a Abuja.

A cikin wata sanarwa da Major Nsima Essien, Mataimakiyar Daraktan Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Mata ta Sojin Najeriya, ta fitar, ta bayyana cewa Brigediya Janar Adamu tare da tawagarsa sun samu kyakkyawar tarba daga Manjo Janar TE Gagariga da manyan hafsoshin cibiyar.

A jawabin da ya gabatar, Kwamandan NAWC ya yaba wa Darakta Janar da tawagarsa bisa jajircewarsu wajen adana tarihi da al’adun Sojin Najeriya tare da kiyaye tarihin rundunar. Ya jaddada muhimmancin tarihi da al’ada wajen inganta ƙwarewa, haɗin kai da alfahari a tsakanin jami’ai masu aiki, musamman mata da ke cikin rundunar.

Da yake mayar da martani, Manjo Janar Gagariga ya gode da ziyarar, yana mai cewa irin wannan ziyara na taimakawa wajen koyar da ladabi da bin ƙa’idoji ga ƙananan hafsoshi. Haka kuma ya jaddada muhimmancin bin dokokin Sojin Najeriya kan amfani da kafafen sada zumunta, musamman ga jami’an mata. Ya kuma sake tabbatar da shirye-shiryen NAHFC na yin haɗin gwiwa da NAWC domin inganta wayar da kai kan tarihi, haɓaka shugabanci da ƙarfafa kishin ƙasa, yana mai bayyana cibiyar a matsayin gada tsakanin jiya, yau da gobe na rundunar.

Bayan kammala ziyarar a NAHFC, Kwamandan NAWC ya kai ziyararsa ta farko ta sanin aiki ga Shugabar NAOWA, Hajiya Safiyyah Hassan Shaibu. Manufar ziyarar ita ce ƙarfafa kyakkyawar alaƙa da haɗin kai, musamman a fannoni da s**a shafi harkokin mata, ƙarfafa su da tallafa wa jami’an mata.

Brigediya Janar Adamu ya nuna jin daɗinsa kan yadda NAOWA ke ci gaba da tallafa wa jami’an mata, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin NAWC da NAOWA domin inganta haɗin kai, ƙara kwarin gwiwa da samar da yanayi mai kyau ga jami’an mata.

A nata ɓangaren, Shugabar NAOWA ta yaba da ziyarar Kwamandan NAWC tare da sake tabbatar da aniyar ƙungiyar na yin aiki tare da NAWC musamman a harkokin jin daɗi da shirye-shiryen ƙarfafa mata.

An kammala ziyarce-ziyarcen biyu da musayar kyaututtuka da ɗaukar hotunan tunawa.










Address

No 1, Mogadishu Layout Kaduna
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jarumai24 TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Establishment

Send a message to Jarumai24 TV:

Shortcuts

Share