Kannywood Trendy

Kannywood Trendy Your #1 source for the latest Kannywood news, movie releases, and behind-the-scenes gists from the heart of Northern Nigeria’s vibrant film industry.

Labarai, Gulmammaki, Ance-Kace da Yayi a masanaantar Kannywood dake Arewacin Najeriya. Kukasancedamu🙏!

24/08/2026

Namamajo: na bar aikin 😂😂

A wata hira da kafar internet DCL Hausa, Jarumar ta bukaci bangaren Rarara da kungiyarsa ta Tripple R da su zu a yi tafi...
23/08/2026

A wata hira da kafar internet DCL Hausa, Jarumar ta bukaci bangaren Rarara da kungiyarsa ta Tripple R da su zu a yi tafiya tare tunda duk tallata Bola Tinubu suke yi.

Mansura tayi nuni da cewa dukda ba a baiwa Dauda Rarara wata mukami a kwamitin yakin zaben APC lokaci yayi da shi da yaransa dake zagin mutane a kafafen sada zumunta da zasu watsi da makamai domin nasarar Tinubu.

Menene raayoyinku?

31/07/2026

Yadda Garzali Miko yayi hidima a wurin dinner na auren darakta Aminu Saira.

Wasu na zargin sa da rashin aji a matsayinsa na celebrity wato sanannen mutum.

Menene ra’ayoyinku?

31/07/2026

Wani bidiyon jarumin kannywood, Garzali Miko, a wurin bikin Aminu Saira na ta nishadantar da maabota kafefen sada zumunta a Arewa. 😂😂😂

29/07/2026

Jarumin kannywood Nakowa ya samu kyauta sabuwar Babur daga Nuhu Abdullahi.

Tuni aka fara tayasa murna.

Mene ne fatanku gareshi?

28/07/2026

Amaren da idan za a yi aurensu suke rungume mazajensu wallahi ni haushe suke ban cewar jarumar kannywood, Asmee Wakili.

Wai ya abun yake ne kam? Kuma suna baku haushi?

Jarumar Kannywood, Mansura Isah, ta yi kira ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da ya sa b...
23/07/2026

Jarumar Kannywood, Mansura Isah, ta yi kira ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da ya sa baki kan abin da ta bayyana a matsayin matsalar amfani da matasa wajen cin mutuncin manyan mutane a kafafen sada zumunta.

A cikin saƙon da ta wallafa, Mansura ta yi zargin cewa ana bai wa wasu matasa miyagun ƙwayoyi domin su riƙa yin kalaman batanci, tare da roƙon Sanata Barau da kada ya janye duk wani mataki da ake ɗauka kan lamarin.

Ta ce matsalar ta fi shafar makomar matasan Arewa, inda ta yi kira da a ɗauki matakan da za su taimaka wajen ceto rayuwarsu da kuma dawo da su kan hanya madaidaiciya.

Mansura Isah ce ta yi waɗannan zarge-zarge a cikin saƙonta. Babu wata shaida mai zaman kanta da aka gabatar da ke tabbatar da zargin nata a lokacin wallafa wannan labari, kuma waɗanda aka ambata ba su mayar da martani kan zargin ba.

22/07/2026

Jarumin Kannywood, KB International, yayi watsi da gwagwarmayar kwato yancin yan Arewa, ya shiga tafiyar Triple R domin tallata zaben Tinubu da APC a zabe mai zuwa.

Wasu jerin bidiyoyi da shi da Garzali Miko s**a wallafa sunce gwagwarmaya ma sai da tallafi shi kuma baya samun hakan.

Menene ra’ayoyinku?

13/07/2026

Wakar da jarumin kannywood, Sani Danja, yayi na cigaba da trending a TikTok.

Wasu abokan aikinsa kamar Maryam KK da Bashir Maishadda da TY Shaaba ma sun dana.

Jarumar Kannywood Aisha Najamu ta bayyana cewa rayuwar aure tana cike da darussa, inda ta ce ta fuskanci jarabawa masu t...
11/07/2026

Jarumar Kannywood Aisha Najamu ta bayyana cewa rayuwar aure tana cike da darussa, inda ta ce ta fuskanci jarabawa masu tsanani fiye da yadda ta taɓa zato.

A cikin wani dogon saƙo da ta wallafa a shafinta na TikTok, ta ce ta fi godiya ga Allah, iyayenta da kuma ‘ya’yanta, waɗanda ta bayyana a matsayin babban dalilin da ya sa ta jure wahalhalun rayuwar aure.

Jarumar ta kuma ce akwai wani lokaci da aka raba ta da ‘ya’yanta har s**a daina gane ta, lamarin da ta bayyana a matsayin mafi girman jarabawar da ta taɓa fuskanta.

Ta ƙare da jaddada cewa yanzu tana cikin godiya ga Allah tare da fatan ba za ta sake shiga irin wannan jarabawa ba.

Address

Kannywood
Jos

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kannywood Trendy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share