ASABE

ASABE Asabe na ma maraba ga fadarta,
Rubutacciyar waƙa ce alƙiblarta,
Ilimintar da mutane muradinta,
Adabi

Big shout out to my new rising fans! Muh'd Harun Abbah
06/09/2025

Big shout out to my new rising fans! Muh'd Harun Abbah

26/08/2025

Ni dai Asalin Bahaushe ne,
Nan Zaria nan nake zaune,
Al'adun ɗan bahaushe ne -
Yau ni zan so na yo zane,
Acikin waƙen ku saurara.

Yau harshen yayi albarka,
Tamkar ranar da ta haska,
A ƙasashe duk ana ɗauka,
Kasuwa office wajen harka,
Zaka ji ta ana ta ana ƙaƙƙara.

Makarantu ma akan koya,
Ilimin ta k**ar na kimiyya,
Ƴan yaran har da ma manya,
Kowa burin shi yai koya,
Hausa tayi k**ar dabon yara.

Ko kai ɗin kai bahaushe ne,
Haka ko kai mai fahimta ne,
Wata kalmar dole kai zaune,
Ma'anarta da ƙyar k**a gane,
Tsinke ɗaya baya yin shara.

Ko ina ka ji Hausa ta kutsa,
Tsakiyar tsokar akwai tsatsa,
Tsakuwa acikin tsaki tsutsa,
Tatsar madarar ƙasan hantsa,
Kuma kan sa basshi yin kora.

© Nura Idris


26/08/2025

26/08/2025



Yau dai Hausa zan yi,
Ba tarkace babu yayi,
Ba shakka babu shayi,
Ko maƙe murya ta shayi,
Ko ko ihun ɗan shayi,
Ko gwalangwatun mashayi,
Mai bin layi yana layi.

Tuntuntuni nai tunani,
Nai duba da idandani,
Nai lura irinta gwani,
Ba tsan-tsami na raini,
Gare ni ba tsagunaguni,
Gunguni ko da gurnani,
Kai! Hausa ta wuce rini!

Yau na cire takunkumi,
Na rabu da ƴan tsegumi,
Masu kitsa ruguntsimi,
Da ke sanya mugun gumi,
Da jimami mai sa tagumi,
Har a fara gani dundumi,
Kamar an faɗo daga rimi.

Ku faɗawa mai magagi,
Yau Hausa babu hargagi,
Ba buƙatar mai kanzagi,
Yau an sanya zuga-zagi,
Ai hattara! Yau babu wargi,
Wurgi da ragi, zagi da zagi,
Rugugi k**ar an sha gadagi.

Tsaya! Kar ka hau santsi,
Ka rarratse kar sammatsi,
Ya sa asarar hatsin hantsi,
In ka ƙiya ka shiga matsi-
Matsatsin rintsin tsi-tsi,
Mai sanya ganin tartsatsi,
Har kai fatan ai watsitsi.

Meye haɗin lalle da talle?
Ina mamaki Talle yai talle?
Ai tun tale-tale an tattale,
Hausa ta wuce a dunƙule,
Maliya ta wuce a ƙwaƙule,
Walwalin-waliyo mai ƙalubale,
Bi ta a sannu kar ka shugulgule.

Gata maganin ɗan gatan kare,
Ɗaukanki sai an taƙarƙare,
Garnaƙaƙin turnuƙu ƙure,
Jarumi da yai janjami bare,
Ragon da ke rugawa ya tsere,
Ya bar ladansa ya kasa jure,
Zaunawa ai ƙiri-ƙiri ƴar ƙure.

Hausa mai sa Gwani shakku,
Yai tsuru-tsuru k**ar a kurkuku,
A matsatsen ɗaki haka tsukuku!
Cike fal! Da taskoki na tasku,
Sai yai aiki tuƙuru riɓi har uku,
Ruƙuƙu da ƙyar ya yi fitar burtu,
Ya tsatsallake zancen ƴan tsurku.

Tufka da warwara wara-wara,
An tafi gargara kwarin gangara,
Ƙarashen ƙarshe ai dai hattara,
A tattaro a tattare inda tai tattara,
Kar zabira tai k**a da gurara,
Kun san dai iska daban sarara,
Waƙar Muntari ƴar bakwai a tara.

© Mukhtar Mudi Sipikin

26/08/2025

HAUSA!

Repost.

Ranar harshe nake zance,
Na Hausa abin fahar guna.

Allah sarki gwanin kyauta,
Shi nake yiwa dukkanin bauta,
Ya rabbi tsareni yin wauta,
Godiya nakayi da harshena.

Kai salati gur rasulillah,
Shugaban bayi Aminullah,
Sonsa baya sa a yo ƙwallah,
Na riƙeshi kakam abban Nana.

Zan bayani kansa harshena,
Bayashi kaf ni a zaɓina,
Shi nakewa so dama ƙauna,
Sai da shi nakayin rubutuna.

Shi ya zamtomin ƙashin baya,
Mai k**a da ice na minjirya,
Ba k**arshi kakaf a nashiyya,
Hausa harshena abin so na.

Ko ina kaine ka kukkutsa,
Dikka alƙarya ka rarratsa,
Ƙoshi ke sa ayo gyatsa,
Ban ƙoshiba kanka harshena.

Ba ilimi na sanin yabo gunka,
Amma kyawu da tsarinka,
Shi ya sani nake ta waƙeka,
Sannu harshen Hausa yarena.

Jama'a zanso ku mommotsa,
Ko kwiyo nuni da ɗan yatsa,
A halittu ma akwai tsutsa,
Ku fahimci abin da ke raina.

Motsi da matsi da bambanci,
Kwaɗo da kwaɗo fa ni banci,
Tsoro a tsaro da ha'inci,
Na riƙe Hausa abar so na.

Sai da shi nafi gane saƙonni,
Ko na yau ko ko na makwanni,
A hawa sama sai a sa tsani,
Jinjina yare abin ƙauna.

Hausa kullum ke ta hoɓɓasa,
In za'ai sai a numfasa,
Magana ko sai a tattausa,
Abba nan zan barku dangina.

✍️Abba Tagarji
___17=01=1443___
___26=08=2021___.

26/08/2025

!

Hausa yarena ni na riƙe,
Sonki har maganama ke nake,
Banda ke wana yare zan riƙe?
Babu shi domin ban ganshiba.

Dukka yare nima na sake,
Ko rubutuna hausa nake,
Amfi gane saƙon in dake,
Ko a daɗi banga k**arki ba.

Kin zamomin yare na uwa,
Harda al'umma duk ƴan uwa,
Ga uba kaka nai rantsuwa,
Kinga ni ba zana sakeki ba.

Har salo a cikinki na iya,
Safiya Safiyanu da safiya,
Tayi shanya kan bisa iggiya,
Tayi wanki dauɗa ta zuba.

A mutum kwai Sani Hasiya,
Dabba Akuya har Saniya,
Tsuntsu Kaza ko Kurciya,
Harda tsirraima ban barsuba.

Abba ne na Tagarji nake bara,
Gunka Allah ƙaro fikƙira,
Har basirama in shahhara,
Hausa ni dai ba zan bartaba.

✍️ Abba Tagarji.

26/08/2025

Ranar Hausa ta Hausawa,
Ku zo mu biya ba ƙosawa,

Ƙarau take ta yo narkewa,
Sharaf take ta yo bushewa,

Ƙasashe duk tayi zagawa,
Ta mutstsike yare takewa,

Da Al'adun mu na birgewa,
Bikin ran Hausa da ɗasawa,

Hausar mu da daɗin furtawa,
Ga sauƙi gun kuma koyarwa,

Idan har zaku yi dubawa,
Muna da ta'adu kyawawa.

®Ranar Hausa
Nura Idris

26/08/2025

26/08/2025

TSARABAR RANAR HAUSA

KAMIL (8+8)

Tsokaci: Akwai Zihafin "Ilmari" wanda yake haɗe tagwayen da'irar farko na ƙafar Takwas su zama guda ɗaya a maimakon 0 0 0-0 0 0-0 sai su koma 0-0 0-0 0 0-0 (maimakon Mutafaa'ilun sai ta koma Mustaf'ilun).

MUTAFAA'ILUN/MUTAFAA'ILUN.

Domin Sa'a domin rabo
Allah da fari na yo kira

Shi ne maƙagin Duniya
Kuma gunSa ni na ka yo bara

Daɗa taimako naSa nai biɗa
Zan zana baiti Sha-tara

In fayyace wani ɗan tsaki
Tsakuwar cikinsa na ciccira

Kan Hausa don ranarta ce
Kwai ɗan batu zan warwara

Fannin rubutu mun sake
Haka nan muke ta tulin kara

Bautar rubutun "English"
Ita ce ta sa muka gangara

Ƙasa, dole ne mu yi ƙoƙari
Sama, dan mu zam mun yunƙura

Wasu sun zata mu baya ne
Ba su san ƙiris mu yi gagara

Ba, salo da tsarin Hausa yau
Har 'yan ƙasar Sin, sun ara

Kuma yi suke sosai a can
Iliminta ba sa gargara

Sai dai anan kash mun sake!
Lamarinta zai yi taɓarɓara

Nazari na al'adunta ma
Duka ɗalibai sun hanƙura.

Haka nan rubutu sai su yi
Ba su san hawan ɗan Ƙawara

Ba suke, abun ban dariya
Tsoho da ƙyamar furfura

A ganinsu ba ta da ƙa'ida
Haka ko ta yaya a murmura

Hausar mu kam ta zarce nan
Lamarinta sai mun ɗammara

Zan dakata haka zan tsaya
Dan bani son ta yi gundura

Ni ne Hassan, mai tambayar
Waye yake wannan kira.

Hassan Auwa Tela
26/08/2025

22/05/2022



RIGA

1. Yau an buga babban tambura,
Na election din Najeriya.

2. Allah sarki su raw material,
Ma'ana ta yan Najeriya.

3. Masu iko duk sun tunzura,
Na qasata yan Najeriya.

4. Yan siyasar taku nake nufi,
Yan qasaka ta yan Najeriya.

5. Kun zame musu tamkar tsaunika,
A qasarmu ta yau Nijeriya.

6. Ku mika su duk su haye sama,
Yan qasata yan Najeriya.

7. Ba ruwanku da cancanta kurum,
Yan qasaka ta yan Najeriya.

8. Aa ku duban wani sabulu,
Yan qasaka ta yan Najeriya.

9. To ahir ba na fada muku,
Yan qasata yan Nijeriya.

10. Datti ne zafa su bar muku,
Yan qasata yan Nijeriya.

11.Sinqi ma bai wanke muku
Yan qasata yan Nijeriya.

12. Maza da Matan raw material,
Yan qasata yan Nijeriya.

13.Muyi duban cancanta kurum,
Yan qasata yan Nijeriya.

14. Jiki magayi na fada muku,
Yan qasata yan Nijeriya.

15. Da susar manjagara kurum,
Yan qasata yan Nijeriya.

16. Gargadi jan kunne nai muku,
Yan qasata yan Nijeriya.

17. Ba kyashi zan maimaita muku,
Yan qasata yan Nijeriya.

18.In kunqi tamaula ta fi muku,
Yan qasata yan Nijeriya.

19. A wurin passing da shan bugu,
Yan qasata yan Nijeriya.

20. Waazi ne,na sauke nai muku
Yan qasata yan Nijeriya.

Safiyya Ya'u Abdullahi✍️

18/05/2022
16/10/1443AD

10:04PM

09/03/2022


CIWON SO

Yanayi ne mai saka dimuwa.
Tafiyarsa k**a da ta kaguwa.
Surarsa hada da ta zabuwa.
Mai shiga dukkanin rayuwa.
Bai barin yaro ko tsohuwa.
Farko kai kace tsintuwa.
Karshe fa k**ar kai tsinuwa.
Domin ta sa maka mantuwa.
Kaji kai kullum kebentuwa.
Zuciya don ta shiga dimuwa.
Kai dai kai ta magantuwa.
Ta saka bisa tsaunin ganuwa.
A cikin rana mai haskuwa.
Ta saka ka kishi na azabtuwa.
Don ba me baka makon ruwa.
Ta saka ka gujewa rayuwa.
Kwakwalwa tayi ta dimuwa.
Zuciya Kuma tai ta azabtuwa.
Idanu suyi ta zubar ruwa.
Jiki Kuma zai rasa garkuwa.
Hakuri Kai kace tsintsuwa.
Ba kunya ka yi kaskantuwa.
Kar kuce min nayo zautuwa.
Cuta ce mai jikkantuwa.
Ba Gambji basu tafarnuwa.
Addu'a ce dukkan garkuwa.
Mai tsai da ido saga soyuwa.
Mai debe dukkan dimuwa.
Mai yaye dukkan damuwa.
Mai haskaka dukkan rayuwa.

©️Safiyya Ya'u Abdullahi✍️
09/03/2022
05/08/1443
1:20pm

  (Hausa duet)ILIMISulaimanDa sunan sa sarki a garemu,Wanda yayyo ilimi a garemu,Don mu kori jahilcin kammu,Don mu koyi ...
21/08/2021

(Hausa duet)

ILIMI

Sulaiman
Da sunan sa sarki a garemu,
Wanda yayyo ilimi a garemu,
Don mu kori jahilcin kammu,
Don mu koyi hulɗa a tsakanimmu,
Sarki mahalicci ga kowa.

Idris
Nai salati ga habibi na,
Manzo mai makka da Madina,
Mujin khadija da maimuna,
Jibrilu yace yi karatu ga kaliƙi na,
To ya zan tsaya dole na zabura kowa.

Sulaiman
Kunsan fa shi Muhammadu,
Shi aka saukar wa da ilmu,
Sannan ya koyar a garemu,
Don mu gyara dukkan rayuwar mu,
Kunji Annabi uba na kowa.

Idris
Yace mu nemi ilmu har sin,
Neman kunga kuwa babu sin,
Dan haka nai Kira ga matasa ku san sin,
Ilmu shine hasken rayuwa har a sin,
Mai ilmi daban yake murya tai babu tsawa.

Sulaiman
Ilimi daɗi da yawa gareshi,
Yana kore jahilci da ƙyashi,
Yana kawo haske ga mai shi,
Ga imani da kore fushi,
Shi ilimi bashi haska wawa.

Idris
Kusan ilimi gishirin rayuwa,
Da shi naga an canza rayuwa,
Ko babu ko sisi ana tsayuwa,
Haba ace baka neman sa'ar wannan rayuwa!
Maza tashi ka nemi ginshi ƙin rayuwa...

Sulaiman
Shi ilimi da kuke ganin sa,
Ba a yin ƙarya da yin sa,
Don bashi ɓuya ga masu yin sa,
In ko kun yo ƙarya da yin sa,
To lalle zaku zamo tiƙewa.

Idris
In Kai karyar za a ƙure ka a can gaba,
In kai kwazo lallai zaka fito sahun gaba,
Zan yi Kira ga ƴan'uwa matasa a nan gaba,
Su dage neman ilmu ba faɗa b***e gaba,
In kabi wannan lallai zaka dacewa.

Sulaiman
Shi ilimi da kuke ganin sa,
In kayo shi ya nuna kansa,
In ka ƙishi ya ɓoye kansa,
Don bashi barin wasa a kansa,
Don haka mu zam masu dagewa.

Idris
Duk da haka mu dage mu neme shi,
Wanda baida sani rayuwar nan sai ai babu shi,
In ko aka ce kai kallon ka babu arashi,
Kamar Sulaiman ya bada himma shi,
Kuzo muyi koyi da irin wannan rayuwa.

Sulaiman
Tabbas Jama'a sai mu farka,
Mu nemi ilimi banda shirka,
Mu kori jahilci har da hauka,
Malam idris shi ma fa yayi girka,
Na neman ilimi har da dagewa.

Idris
A fagen neman sai mun dage,
Mu sa naci sai mun dage,
Ta haka har aka san daage,
Mui aiki tukuru kar muce zamui ɗage,
Wakar na tafiya ta taho karewa.

Sulaiman
Nan zan tsaya da baituka na,
Dana rero babu bajin ta na,
Sai tunatarwa ga abokai na,
Kai har ma dasu ƴan'uwa na,
Har ga ɗauka cin jama'a nawa.

Idris
Mu dage gun neman ilimu,
Matasa a cikin mu akwai imamu,
Baitukan namu kenan cikin jammu,
Sai wata Rana zaku sake jin mu,
Allah yasa kun ƙaru da baitukan nawa.

✍️ Sulaiman Da Idris

 # ASABEAREWA Iliyasu 1Sunan ilahu farkon farawa,Sai saka shi kan komai nawa,Don sai dashi nake  iya cimmawa-Dukkan abun...
21/08/2021

# ASABE

AREWA

Iliyasu
1
Sunan ilahu farkon farawa,
Sai saka shi kan komai nawa,
Don sai dashi nake iya cimmawa-
Dukkan abun nayi nufin tsawa.

aibmatawalle303:
2
Dubun salati ilahu Allah,
Kayo agunsa manzo rasula,
Alai kasanya dukansu jumla,
As'habihima asasu jumla.

Iliyasu:
3
Abunda ni da ɗa ruɗani,
lardin mu ko ina babu sukuni,
yawan mu ya zamo maras amfani,
ana kashemu mun gaza ganewa.

aibmatawalle303:
4
Yak**ata arewa mufarka,
Matakai dukka mudauka,
Rayukanmu mukare dukka,
Shawagabanni sunyi gazawa.

Iliyasu:
5
kullum abun yana da ɗa ban tsoro,
ko raidiyo idan nayi sauraro,
dukkan batun da zanji sun jero,
wai ɗaliban mu ne aka kwashewa.

aibmatawalle303:
6
Mutum yazama k**ar wani jari,
Wanda inkasamu kazama tajiri,
Sai kaji ana kubada miliyan dari,
Cikin Dan Adam ne ake yowa.

Iliyasu:
7
kaga abunda ke da ɗa damuna,
boko haram suna nan lardina,
'yen bindiga akwaisu a yankina,
'yen garkuwa ko suke kwashewa.

aibmatawalle303:
8
Ya k**ata dai muyi nazari,
A arewa kadai abin yaka k**ari,
Can kudu bakajin wani labari,
Ansace wane ko kuma harbewa.

Iliyasu:
9
dole sai mun kauda ƙabilanci,
mun hau kan turbar adalci,
sannan mu fice azaman ƙunci,
sai zaman lafiya yayi ɗorewa.

aibmatawalle303:
10
Lamarinfa da mamaki ne,
Shugaban kasar fa namu ne,
Manyan hafsoshin namu ne,
Kodai lauje anadi aka kullawa?

Iliyasu:
11
Ni har yanzu abunda ban ganeba,
ɗalibai a school ba a ƙyale ba,
masu kudin gari ba a ƙyale ba,
ni lamarin fa na gaza ganewa.


@⁨aibmatallawa303⁩

21_augusta_2021...✍🏻

 Ja ni in ja ka (Duet) Abu ShukuraRabbi Allah khalikinaZul jalal arraxiƙinaMai dare harma da ranaBani dama khaliƙinaDon ...
21/08/2021



Ja ni in ja ka (Duet)



Abu Shukura
Rabbi Allah khalikina
Zul jalal arraxiƙina
Mai dare harma da rana
Bani dama khaliƙina
Don nayo waƙar ƙasa ta.

Hassan
Fari zan yabi Annabina
Gaskiya da ruƙon amana
Ko ina shi ne ka nuna
Shi ya sa ni sonsa raina
Ya game duk zuciyata

Abu Shukura
Ƴan uwa munzo da haja
Ɗa wa Gombe da ɗan Haɗeja
Mun haɗe yau munyi maja
zamuyo magana da hujja
Kan hali na zaman ƙasata.

Hassan
Kan tsaro ne za mu tauna
Kuskuren da ake mu nuna
Mafita mu faɗa a auna
In muna fatan mu zauna
Lafiya, a cikin nagarta.

Abu shukura.
Kuskuren mu rashin amana
Gun riƙon da mukewa juna
Maffitar itace mu auna
shin hakan riba ya nuna
Koko cigaba ƴan ƙasata ?

Hassan
Na ji Hausa suna faɗin ai
Walwala ko kwanciyar rai
Ta fi taka dukan matakai
Ko ka zamma ɗiyan sarakai
Masu yin burga da mota

Abu shukura
Fank**a da gida da mota
Koko kalachi da hanta
Wadda kegun ƴan sarauta
Basuyi nine na furta
In ƙasar sam ba nagarta.

Hassan
Na tuno da kan mu taɓe
Kan ƙasar komai ya kwaɓe
Ba a yin rikici na zaɓe,
Babu masu kisa su raɓe
Wai ibada za su saita.

Abu Shukura
Na tino da amalgamation
North da South anyo connection
Lokacin sam ba corruption
Duk tsakani babu tension
Lokacin munsamu gata.

Hassan
Ga abinci yana ta yawo
Da muna noma da kiwo
Shugabanni ba ɓarawo
Rayuwarmu muna ta ƙawo
Babu mummunar fahimta

Abu Shukura.
Ga halayyar girmamawa
Babu duk mai raina kowa
Ƴan uwa na taimakawa
Babu ƙoro gun ciyarwa
Lokacin da akwai zumunta.

Hassan
Yanzu kam duk babu wannan
Ko'ina a cikin ƙasarnan
Ya ƙi daɗi kai abunnan
Sai du'ai, dan ko wannan
Waƙi'ah da akwai ƙazanta.

Abu Shukura.
Zahiri mun kauda ɗa'a
Mun zamanto ba ƙana'a
Gashi bamu riƙon sana'a
Can a loton baya a'a
Ba kasala ƴan ƙasata.

Hassan
Masu laifi na ta gasa
Babu aiki gun matasa
Shaye-shaye ana marisa
Ya zamo sana'ar matasa
Wanda har da maza da mata

Abu Shukura.
To abun kan babu option
Ko a ƴan mata abortion
Shayshaye da shafa lotion
Shiyake jefan a tension
Inna dubi maza da mata.

Hassan
Ga yawan karɓan corruption
Gun hukuma of the nation
Sun ƙware gun percecution
On their masses, assumption!
Ka ga dole mu yo makanta.

Abu Shukura.
Kai tsaro kan ya ƙazanta
dukka kowa ya jigata
Rayuwar mu ake farauta
Kai bara dai in taƙaita
ƴan arewa fa babu gata.

Hassan
Masu laifi yau hukuma
Ba ta horo kansu amma
Wanda ko s**a ba da himma
Gu tsare daraja da kima
Su ka shan wahala ƙasata.

©Ibrahim Isa Abushukura da Hassan Auwa Tela
21-08-2021

Address

Hadejia

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ASABE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category