Qugiya

Qugiya Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Qugiya, Dutse Jigawa, Birnin-Kudu.

27/02/2026

Uban me Sukeyi a Abuja?

24/02/2026

Malam Ya Amsa kira

Mutanen Da suke Sukan Malamai Wajen Shiga Tsarin Shugabanci "Mutane ne waɗanda Basaso A Tsabtace  Tsarin Mulki Kuma A sa...
05/02/2026

Mutanen Da suke Sukan Malamai Wajen Shiga Tsarin Shugabanci "Mutane ne waɗanda Basaso A Tsabtace Tsarin Mulki Kuma A samu Masu ilmi Da Tsan-tsaini Da Dukiyar Al'umma A Cikin Shugabanni.

Daga Abubakar Shehu Dokoki .

SANARWAR TSINTUWAAn tsinci wannan yarinya a Bypass, kusa da babbar kotu jiha dake nan Gombe (High Court), yanzu haka yar...
19/01/2026

SANARWAR TSINTUWA
An tsinci wannan yarinya a Bypass, kusa da babbar kotu jiha dake nan Gombe (High Court), yanzu haka yarinyar ta na gidan Jauron unguwa.

Duk wanda ya san iyayenta ko danginta, a tuntuɓi wannan lamba:
📞 08167214883
Allah Ya sa a dace.

Wannan shine Umar Wanda Ake Zargi da ki*san uwa da 'ya 'yanta A Ɗorayi Dake Kano.Muna Fatan Ayi Gaggawar Kawar Da Wannan...
18/01/2026

Wannan shine Umar Wanda Ake Zargi da ki*san uwa da 'ya 'yanta A Ɗorayi Dake Kano.

Muna Fatan Ayi Gaggawar Kawar Da Wannan Tsi*nannen, ta hanyar ɗaukar mataki akansa, da zarar an kammala Bincike.

Daga Abubakar Shehu Dokoki.

Daruruwan matasa masu goyon bayan Professor Isa Ali Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya, Wazirin Pantami kuma Sarkin Mal...
06/01/2026

Daruruwan matasa masu goyon bayan Professor Isa Ali Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya, Wazirin Pantami kuma Sarkin Malaman Malala) dake karamar hukumar Dukku, sun gudanar da taro na musamman, a yau Talata.

A yayin gudanar da taron an kara wayar da kan marubutan kan abunda ya shafi harkar rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta da sauransu.

Haka zalika matasan sun jaddada kira tare da roko ga Professor Isa Ali Pantami, da ya daure ya fito takarar Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.

Mutanen Dukku sunyi dan dazo sun fito daga kowane yanki na fadin karamar hukumar, domin nuna soyayya da kaunarsu ga Majidadin Daular Usmaniyya.

Wannan yake kara nunawa da tabbatar da cewa mutanen jihar Gombe na kowane yanki a shirye suke domin bada gudummuwarsu na ganin Professor Isa Ali Pantami, ya zama zababban Gwamna a zaben 2027.

DA DUMI-DUMI: Ali Nuhu ya zama Ambasadan kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, bayan kulla yarjejeniyar Naira miliyan 30 na ts...
25/12/2025

DA DUMI-DUMI: Ali Nuhu ya zama Ambasadan kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, bayan kulla yarjejeniyar Naira miliyan 30 na tsawon shekara guda

ABBA PANTAMI DATA LTD ya sake rage muku farashin Data zuwa Naira 500 akan kowane 1GB, ku hanzarta ku sauke Application din, domin ku more garabasa.

Duk wanda ya sayi Data mai 30DAYS a Application din ABBA PANTAMI DATA LTD to sai tayi kwanaki 30 sannan za tayi Expired. Akwai bambanci tsakanin Expired da kuma karewa.

Matukar kuna amfani da Application din ABBA PANTAMI DATA LTD da zaran ka hadu da matsalar network ko makalewar kudi kana yiwa customer care dinsu magana anan take zasu gyara maka.

Idan baka taba amfani da Application din ba ka gwada, idan ka dade baka yi amfani dashi ba ka sake gwadawa a yanzu domin tabbatar da ingancin shi.

Kuyi Download din Application din ABBA PANTAMI DATA ta wannan link din a PlayStore da kuma AppStore

👇👇
Ga link din PlayStore
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.abbapantamidata.app

Ga link din AppStore
https://apps.apple.com/us/app/abba-pantami-data-ltd/id6744061271

Mai bukatan karin bayani, ya tuntubi daya daga cikin customer care ta WhatsApp;
09138275183
08126081967
07046868000
07061347599

Sulaiman kenan Daga Dutse Jihar Jigawa, ɗaya Daga cikin Yan Gwagwarmayar Da Ake Kyautatawa Zato a Jihar Jigawa, ko Kunad...
15/12/2025

Sulaiman kenan Daga Dutse Jihar Jigawa, ɗaya Daga cikin Yan Gwagwarmayar Da Ake Kyautatawa Zato a Jihar Jigawa, ko Kunada ire-iren waɗannan matasan a Jihohin ku?

Daga shafin Abubakar Shehu Dokoki

Muna Nemawa Abba Sani Pantami Sarautar Sarkin Datar Kasar Hausa, A Masarautar Daura, A Cewar Abdullahi Giggs.
14/12/2025

Muna Nemawa Abba Sani Pantami Sarautar Sarkin Datar Kasar Hausa, A Masarautar Daura, A Cewar Abdullahi Giggs.

RANAR GWAURAYE TA DUNIYA: Fáɗi Sunan Abokinka Gwauro Guda Ɗaya Daka Tuna Kuma Kake Tausaya Masa Musamman A Irin Wannan Y...
11/11/2025

RANAR GWAURAYE TA DUNIYA: Fáɗi Sunan Abokinka Gwauro Guda Ɗaya Daka Tuna Kuma Kake Tausaya Masa Musamman A Irin Wannan Yanayi.

Daga Abubakar Shehu Dokoki

DA DUMI-DUMI: Jami'an tsaro sun k**a Indabawa Imam Aliyu, kan laifin kirkirar karya, kazafi, sharri da cin mutunci da ya...
03/11/2025

DA DUMI-DUMI: Jami'an tsaro sun k**a Indabawa Imam Aliyu, kan laifin kirkirar karya, kazafi, sharri da cin mutunci da ya shafe tsawon shekaru yana yadawa akan Sheikh Professor Isa Ali Pantami CON (Majidadin Daular Usmaniyya).

Ku duba hotunan dake kasa, na wasu shafukan da yake kula dasu, tun a 2022 yake kirkirar karya da kazafi da sharri, cin mutunci, yana sakawa a shafukan nashi na yada labarai, amma aka yi shiru aka barshi domin wata kila zai gaji ya daina, amma duk da haka kwanan nan ya kara kirkiro wani labarin karyar tare da kafa source na wata jaridar karya da aka neme ta aka rasa a Facebook.

Tuni jami'an tsaro sun kamo shi a jihar Kano, inda a yau Litinin za'a gabatar dashi a gaban kotu, bayan an kammala zaman kotun zamu sanar muku.

Wa 'yan nan kadan ne daga cikin irin cin mutunci da kirkirar karya haka kawai don yasa al'umma su zagi Sheikh Professor Professor Isa Ali Pantami, mun kawo muku wannan rahoton ne ba don cin mutuncin shi ba sai-dai masu irin wannan halin su gyara.

GARGADI: Duk wanda yasan yana cin mutuncin Sheikh Professor Isa Ali Pantami, na kirkirar karya, sharri da kazafi a social media ko a gidajen Radio to tabbas ya sani wallahi doka za tayi aiki akanshi.

Siyasa da adawa ba'a hana kowa ba, kuma ba'a taba tankawa wani don yayi adawa da Malam ba, amma ba zamu taba lamunta da cin mutunci, sharri da kazafi ba, domin mutane da yawa suna ganin saukin taba Malam saboda ya kasance Malamin Addinin musulunci kuma mutumin kirki.

Yau, a jihar Gombe akwai manyan 'yan siyasar da wallahi ko zaginsu ba'a isa a yi ba, saboda kowa yana tsoron daure shi za suyi, b***e ka dinga kirkira musu karya, kazafi, sharri da cin mutuncinsu, amma kasancewar shi Pantami malamin Addinine yasa kowane kare ya tashi haushi da cin mutunci sai ya dirka kan Pantami. Ya k**ata duk wani matashin a jihar Gombe dama Najeriya ya sani, yanzu ba baya bane, doka za tayi aiki akan duk wanda yaci mutuncin Sheikh Pantami.

Shafukanshi na CNN HAUSA da VANGUARD HAUSA kullum cikin yada labaran karya da yiwa al'umma sharri suke yi, a guji yadda da abubuwan da suke ruwaitowa kasancewar shafukane na bogi.

Address

Dutse Jigawa
Birnin-Kudu
1122

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qugiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share