25/11/2023
Wasu mutanen (kamar) haka rayuwarsu take a yau (cikin hoton ƙasa), amma ba su sani ba. Bini-bini, an ɗauko waya, cikin tafiya, lokacin cin abinci, aiki, karatu, bacci, shiga banɗaki... wani (ma) da zarar an idar da sallar maimakon ya fara zikiri, sai ya taɓa 'screen' ɗin waya tukun.
'Behavioral addiction' kenan, wannan matsala ce babba kuma tana da illar sosai ga rayuwar yau da kullum musamman ga matasa, amma ana magancewa.
Masu irin wannan matsalar a yau, za su ce ma, suna 'busy-busy', nan kuwa ba wani 'busy', social media ce; ba su maida hankali kan abin da ke gabansu (na aiki, ko karatu, dss), wasu har su haɗu da matsalolin 'nomophobia', 'FOMO' da yawan shiga damuwa. Wani lokacin idan kana son maida hankali kan rayuwarka da aiyukanka, sai ka rage amfani da social media.
Za ka iya ɓata 2hrs - 5hrs online (non-stop), amma ba za ka iya zama ka iya yin wani aikin kirki na cikekkekiyar 1hr ba, ba tare da wayarka ta zame ma distraction ba.
Yanzu daga tashi sallar asuba, wani ba zai iya zama ya yi zikirin 15mins ba, amma zai iya scrolling feeds a Facebook har gari ya waye (sama da 2hrs).
Gaskiya, akwai matuƙar buƙatar ka yi 'detox' (ƙauracewa social media na ɗan lokaci). Ka kuma sanya iya adadin awowin da za kana ɓatawa online (matuƙar ba kasuwa kake da ita ba). A lokacin da kake aiki kuma, ka ajiye wayarka nesa da kai.
Idan kana da irin wannan matsalar, ka gwada 'digital/social media detox', ma'ana ƙauracewa amfani da waya na ɗan wani lokaci mai tsayi, ko kuma ka riƙa ware iya lokuta ko awannin da za ka riƙa yi a social media, matuƙar ba kasuwanci kake a 'social media' ba. Kamar a Facebook, za ka iya saita 'Quite Mode' kan iya lokacin da za kake ɓatawa; shiga 'Setting & Privacy' > 'Settings' > 'Your Time on Facebook' > 'Manage Your Time' > 'Quite Mode', sai ka saita 'Quite Mode Timer'