07/01/2025
Idan akace Blockchain inza a ma gwari-gwari shine wani tsarin ãdana bayanai neh. Faqat!
Idan akace ãdana bayanai, abinda ke zuwa ma mutum shine a Ajiye bayanan a guri daya.
Toh anan neh Blockchain ya ba bambanta:
Wato A blockchain bayanan ba
~a guji daya ake ajewa bah
~ba mutum daya ke ajewa bah. Idan za'a chanza duk wanda ke riqe da bayanan za'a bi a chanza gun shi.
Saɓani yadda muka saba ajiye/tattara bayanai wanda
~a guji ɗaya ake ajewa
~mafiya yawan lokuta wani ko wa'insu tsirarun mutane neh ke ajiyewa.
To a takaice Blockchain wani tsarin ãdana bayanai neh wanda ba wanda zai iya chanza shi.
Tayaya ba za'a iya chanza wa bah?
Wannan a matsayin shimfiɗa ce, InshaAllah zamu qara fayyacewa a rubutu na gaba.
Yanzun dai kawai in akace ma blockchain, ana nufin ãdana bayanai a dunqulle.