01/08/2026
Tsohon ministan Birnin Abuja, Dr Aliyu Modibbo ya Bukaci hukumomi da su dauki matakai na gaggawa wajen yayyafa Ruwa Kan abinda ya kira "fitinar siyasa a Jihar Gombe tun kafin abubuwa su tabarbare.
Ya kara da cewa "Kalaman barazana, hargitsa tarukan lumana, da ayyukan taron motoci da jerin gwano na fitan hankali (motorcade) masu hadari da ke faruwa kafin lokacin yakin neman zabe wadda hukuma ta ayyana, sun saba wa doka kuma suna barazana ga zaman lafiyar jihar mu".
Ya lissafo wasu matakai da yace Suna da muhimmanci wajen tabbatar da doka a oda kamar yadda zan bada shawara:
• Kiran Taron Gaggawa: Dole ne Hukumar Zabe (INEC) da jami'an tsaro su tara dukkan masu neman takara. Ayi wa yan takara da magoya bayan su gargadi da jan kunne muhinmancin zaman lafiya.
• Sanya Hannu Kan Yarjejeniya: Ya kamata a tilasta wa kowane dan siyasa sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya (Peace Accord).
• Hukunta Masu Karya Doka: Kamata ya yi a hukunta dukkan wanda ya fito da ayyukan barna ko kalaman tunzura al umma ba tare da jinkiri ba.
• Tarihin Zaman Lafiya: Jihar Gombe na alfahari da tarihin zaman lafiya; bai kamata son zuciyar 'yan siyasa ya lalata wannan kyakkyawan tarihin ba.