Imam Documentary Hausa

Imam Documentary Hausa ๐Ÿ†• Account..

๐—ช๐—ฒ๐—ฏ๐Ÿฏ ๐—–๐—ผ๐—ป๐˜๐—ฒ๐—ป๐˜ ๐—ฉ๐—ถ๐—ฑ๐—ฒ๐—ผ ๐—–๐—ฟ๐—ฒ๐—ฎ๐˜๐—ผ๐—ฟ ๐ŸŽฅ | ๐—”๐—ถ๐—ฟ๐—ฑ๐—ฟ๐—ผ๐—ฝ ๐—›๐˜‚๐—ป๐˜๐—ฒ๐—ฟ ๐ŸŽฏ | ๐—ง๐—ฟ๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฟ ๐Ÿ“Š | ๐—•๐—น๐—ผ๐—ฐ๐—ธ๐—ฐ๐—ต๐—ฎ๐—ถ๐—ป ๐—˜๐—ฑ๐˜‚๐—ฐ๐—ฎ๐˜๐—ผ๐—ฟ ๐Ÿ”—.
(1)

05/06/2026

Ali Larijani ๐Ÿ’”๐Ÿ™ Facebook for Creators

Jami'an tsaron sun gudanar da samamen ne a Istanbul da Izmir, inda s**a yi nasarar cafke mutum bakwai da ake zargi da ba...
02/02/2024

Jami'an tsaron sun gudanar da samamen ne a Istanbul da Izmir, inda s**a yi nasarar cafke mutum bakwai da ake zargi da bayar da bayanai a fakaice ga Mossad, k**ar yadda majiyoyin tsaro s**a bayyana a ranar Juma'a.๐Ÿ‘‡

Turkiyya ta k**a mutum 7 da ake zargi 'yan leken asirin Isra'ila ne Wannan samamen na nuna gagarumar nasarar da Turikyya ta samu kan hukumar...

SALLAR DAREN BIYU GA WATAN RAJABSallah rakaโ€™a 10, Fatiha 1, Kulya-ayyuhal kafirun 1.Falalarta.Anruwaito hadisi daga Manz...
13/01/2024

SALLAR DAREN BIYU GA WATAN RAJAB
Sallah rakaโ€™a 10, Fatiha 1, Kulya-ayyuhal kafirun 1.

Falalarta.
Anruwaito hadisi daga Manzon Allah (S) yace โ€œAllah zai gafarta mashi dukkanin zunubanshi, kuma zaโ€™a rubutashi a masallata har zuwa shekara mai zuwa, kuma zai barranta daga munafunciโ€.

[ Ikbalul-Aโ€™amal ]

Daga - F-fighters Zauren A'amal ๐Ÿ‘‰๐Ÿผ
https://chat.whatsapp.com/D9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

FREEDOM FIGHTERS NG

Follow us @

๐ŸŒŽwww.freedomdomfightersng.com
๐Ÿ–ฅ๏ธ t.me/freedom_fighters_ng
๐Ÿ“ฒ www.twitter.com/f_fightersng
๐Ÿ“ธ www.instagram.com/freedom_fighters.ng/
๐Ÿ“ฑwww.facebook.cD9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

WhatsApp๐Ÿ‘‰๐Ÿฝ https://chat.whatsapp.com/D9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

Falalar Watan Rajab Daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)Rajab, idan mutum ya duba Mafatihul Jinan, a yayin da yake kawo ayyu...
12/01/2024

Falalar Watan Rajab Daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Rajab, idan mutum ya duba Mafatihul Jinan, a yayin da yake kawo ayyukan shekara ya fara da watan Rajab ne. Yana cewa; shi ne k**ar watan farko a ayyuka. Rajab, Shaโ€™aban, Ramadan, watanni masu ayyuka na ibada. Saboda haka ya k**ata mutum ya yi shirin shiga Rajab.

Akwai ayyuka na musamman na daren farko na Rajab. Kar mutum ya yi sake. Daren farko da kuma, musamman azumin farkon Rajab din. Ya tashi da azumi daya ga watan Rajab. Da Rajab da Shaโ€™aban da Ramadan, watanni ne masu darajar gaske.

An samo hadisai daban-daban a kan falalolinsu. A cikin Ikbal Aโ€™amal, na ga shi Sayyid bn Dawus ya kawo wani dogon magana a kan cewa; ka sani dangane da falala an samo ruwayoyi da yawan gaske. To, ko da a โ€˜kaโ€™idatul man balagahโ€™. Idan ka san wata kaโ€™ida ana ce ma ta โ€˜kaโ€™idatul man balagah,โ€™ hadisi ne aka samu daga Aโ€™imma daban-daban ma.

An samu daga Imam Bakir da Imam Jaโ€™afar da Aiโ€™mma (AS) daban-daban cewa; idan ruwaya ta zo maka dangane da wani aikin alheri, in ka aikata, kana da ladan wannan abin da ka ji an gaya maka din, ko da ba haka Annabi ya fada ba. Saboda ita falalar Allah tana da yawan gaske.

Wato a babin falala ana amfani da hadisi, ko da bai inganta ba, ko da mai rauni ne. Hadisin da ba za a yi amfani da shi ba a babin falala kawai shi ne, ya tabbata kirkirarre ne. Hadisi Mauduโ€™i, za a iya amfani da shi? Sam! Amma hadisi mai rauni, ba wani damuwa. In dai ya ce; wanda ya karanta kaza, za a ba shi kaza. Khalas! Karanta kawai, insha Allahu ka ma samu ka gama.

Saboda Allah (T) abin da yake da shi yana da yawan gaske. Bisa yalwar Rahamarsa zai ba ka wannan din. Yawwa! In dai aka samu ruwayar. Ballantana mu muna da ruwayoyi ma, wadanda suke ba a babin โ€˜kaโ€™idu man balagahโ€™ ba. Ainihin ma sun inganta ne ruwayoyin.

To, hatta ko ba su inganta ba a babin falala. Don wasu ka ga ni ban san abin da ya same su ba, da zaran watan wannan Azumin ya k**a, su kuma sun fara waโ€™azi ke nan, kar a yi azumi. Wai azumin ana ce masa na tsofaffi. Wannan azumi ne na tsoho? Sun fara wannan abin ke nan. Ye-ye-ye, su yi ta ihu. Wai a daina yi. Wai Annabi bai yi ba.

Kuma sai su zo su ce; to, Annabi bai yi Rajab ba dai, amma ya yi Shaโ€™aban. To, su kuma ba za su yi Rajab din ba, ba za su yi Shaโ€™aban din ba. Amma sun dunga ke nan, suna cewa wadansu mutane sun kirkira ma kansu, suna yin azumin wata uku. Duk wanda ya yi haka nan, ya sabi Allah. Annabi bai taba wata uku yana azumi ba.

To, โ€˜falyakunโ€™. Wa ya ce maka azumin ba kyau ne? Da Annabin bai yi ba, sai ya ce maka kada ka yi? Uhm? Da kake shan fura da nono, Annabi ne ya sha Fura da nono din? Da kake cin tuwo miyar kuka din nan, shi ma Annabi ne ya ci? To, ya ce maka kada ka ci ne? Ehen! Cewa Annabi bai yi ba, ba shi ne magana ba. Annabi ya ce; kada a yi?

To, ballantana an samu ruwaya. Su suna da ruwayar cewa; Annabi ya kasance ya kan yi azumin Shaโ€™aban duk cikarsa, ya sada shi da Ramadan. Amma ba dayansu da zai yi. Yana nan yana s**an kar a yi Rajab. Amma Annabi yana Shaโ€™aban. To, tunda yana s**ar kar a yi Rajab, sai ya bar Rajab din, sai ya yi mene? Sai ya yi Shaโ€™aban din. Amma ba zai yi wannan ba, ba zai yi wancan ba. To, wannan buzines dinsu ne. Su s**a dauka ma kansu.

An ruwaito Manzon Allah (S) yana cewa; Rajab watan Allah ne, Shaโ€™aban watana, Ramadan kuma watan alโ€™ummata. Yana cewa; โ€œwanda ya yi azumin yini guda na Rajab, zai cancanci yardar Allah. Kuma za a nesanta fushin Allah gare shi. Za a dode masa kofa daga kofofin wuta.โ€

Daga Imam Musa bn Jaโ€™afar (AS) yana cewa, โ€œwanda ya azumci yini guda na Rajab, wuta za ta yi nesa da shi shekara guda. Wanda ya yi azumin kwana uku a Rajab, Aljanna ta wajaba gare shi.โ€ To, ga su nan dai (ruwayoyi daban-daban).

Akwai kuma ruwayar da ke cewa; โ€œshi Rajab din nan wata korama ce a Aljanna, ta fi nono fari ta fi zuma zaki. Wanda ya azumci yini guda na Rajab, Allah zai shayar da shi daga wannan korama din.โ€ Ga su nan, ga su nan, ruwayoyi daban-daban. Saboda haka mutum ya fara kaimi. Insha Allahu ya shiga Rajab da ayyuka na alheri da tuba ya zuwa ga Allah.

Wasallallahu Ala Muhammadin waโ€™alihid dahirin.

โ€” Shaikh Zakzaky (H) ya yi wannan jawabin a karshen wata watan Jimadal Thani, a shekarun baya a Husainiyya Baqiyyatullah.

Domin samun ayyukan ibada na wannan wata mai alfarma ku kasance da ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ
F-fighters Zauren A'amal ๐Ÿ‘‰๐Ÿผ
https://chat.whatsapp.com/D9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

FREEDOM FIGHTERS NG

Follow us @

๐ŸŒŽwww.freedomdomfightersng.com
๐Ÿ–ฅ๏ธ t.me/freedom_fighters_ng
๐Ÿ“ฒ www.twitter.com/f_fightersng
๐Ÿ“ธ www.instagram.com/freedom_fighters.ng/
๐Ÿ“ฑwww.facebook.cD9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

WhatsApp๐Ÿ‘‰๐Ÿฝ https://chat.whatsapp.com/D9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

AYYUKAN DAREN FARKO NA WATAN RAJAB.1 - Addu'o'in ganin watan Rajab aduba mafatihu.2 -  Wanka: anayin wanka a wannan dare...
12/01/2024

AYYUKAN DAREN FARKO NA WATAN RAJAB.

1 - Addu'o'in ganin watan Rajab aduba mafatihu.

2 - Wanka: anayin wanka a wannan dare an ruwaito hadisi daga Manzon Rahama (S) yace " Wanda ya riski watan Rajab mai alfarma to yayi wanka a farkon shi da tsakiyar shi da ฦ™arshen shi, idan mutum yayi haka Allah zai tsarkaka daga zunubanshi k**ar ranar da mahaifiyar shi ta haifeshi".

3 - Ziyarar Imam Husain (A.S) : Anruwaito hadisi daga Imam Ja'afarus-Sadik (s.a) yace " wanda ya Ziyarci Imam Husain A ranar daya ga watan Rajab Allah (T) zai gafartamashi Zunubanshi"

SALLOLIN WANNAN DARE NA FARKON WATAN RAJAB.

- Sallah Ya Farko
Sallah raka'a 20 bayan sallar magrib, a karanta Fatiha 1, da ฦ˜ulhuwallahu 1 a kowace raka'a yayi sallama a bayan kowace raka'a biyu.

Falalar Wannan Sallah.

An ruwaito cewa " Wanda yayi wannan Sallah Allah (T) zai kare Iyalinshi da dukiyarshi da iyayen shi, kuma kuma zai kuษ“uta daga azabar kabari, kuma zai wuce kan siraษ—i k**ar walฦ™iya.

- Salla Ta Biyu
Sallah raka'a biyu bayan sallar isha'i, a raka'ar farko a karanta Fatiha 1, Alamnashraha 1, ฦ˜ulhuwallahu 3, a raka'a ta biyu a karanta Fatiha 1, Alamnashraha 1, ฦ˜ulhuwallahu 1 sai a karanta Falaฦ™i da Nasi, idan anyi sallama sai ayi wannan zikirin " Laa ilaha illallah " sau 30, Salatin Annabi 30.

Falalar Wannan Sallah.
Duk wanda yayi wannan Sallah Allah zai gafarta mashi zunubanshi k**ar ranar da mahaifiyarshi ta haifeshi.

Allah (T) yakarษ“i Ibadu.
A duba "Mafatihul-Jinan domin ganin sauran Ayyukan wannan dare.

Daga - F-fighters Zauren A'amal ๐Ÿ‘‰๐Ÿผ
https://chat.whatsapp.com/D9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

FREEDOM FIGHTERS NG

Follow us @

๐ŸŒŽwww.freedomdomfightersng.com
๐Ÿ–ฅ๏ธ t.me/freedom_fighters_ng
๐Ÿ“ฒ www.twitter.com/f_fightersng
๐Ÿ“ธ www.instagram.com/freedom_fighters.ng/
๐Ÿ“ฑwww.facebook.cD9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

WhatsApp๐Ÿ‘‰๐Ÿฝ https://chat.whatsapp.com/D9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp

โ€œDubi abin da suke yi a Siriya. Dubi Libya, sun kafa yaki, sun wargaza, daga baya kuma s**a kashe Gaddafi. Dubi abin da ...
12/01/2024

โ€œDubi abin da suke yi a Siriya. Dubi Libya, sun kafa yaki, sun wargaza, daga baya kuma s**a kashe Gaddafi. Dubi abin da s**a yi wa Somaliya wanda s**a mayar da su ba ta da mulki tsawon shekaru da s**a wuce. Wannan shi ne abin da suke kullawa a Najeriya.โ€

โ€“Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).

ยฉ๏ธ ๐Ÿ“ธFREEDOM FIGHTERS NG

Follow us @

๐ŸŒŽwww.freedomfightersng.com
๐Ÿ–ฅ๏ธ https://t.me/freedom_fighters_ng
๐Ÿ“ฒ www.twitter.com/f_fightersng
๐Ÿ“ธ www.instagram.com/freedom_fighters.ng/
๐Ÿ“ฑwww.facebook.com/109221621639457/
๐Ÿ“žhttps://chat.whatsapp.com/LW41Y9UlF583rVvs0gVEDg

10/01/2024

A watan Disamba hukumar EFCC ta ayyana tsohon ministan a matsayin wanda take nema ruwa-a-jallo kan zargin badakalar dala biliyan shida a kwangilar tashar samar da hasken lantarki ta Mambila. Karin bayani ๐Ÿ‘‡

An tura tsohon Ministan Lantarki gidan yarin Kuje kan badakalar kwangilar Mambila. A watan Disamba hukumar EFCC ta ayyana tsohon ministan a...

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne bayan jami'an tsaro sun hango wasu 'yan bindiga a kan babura suna tsara yadda za su ka...
07/01/2024

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne bayan jami'an tsaro sun hango wasu 'yan bindiga a kan babura suna tsara yadda za su kai hare-hare a yankin Libiri Bulangiga da Garbunwa ranar Juma'a da daddare zuwa safiyar Asabar. Karin bayani ๐Ÿ‘‡

Jirgin yakin Nijar ya kashe fararen-hula 'bisa kuskure' Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne bayan jami'an tsaro sun hango wasu 'yan bindiga a ...

Bayan shafe kusan watanni tara ana yaki a Sudan, shugaban sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya lashi takobin ci gaba da...
06/01/2024

Bayan shafe kusan watanni tara ana yaki a Sudan, shugaban sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya lashi takobin ci gaba da yakar rundunar RSF. Karin bayani ๐Ÿ‘‡

Al-Burhan ya ce ba zai sasanta da rundunar RSF ta Sudan ba. Bayan shafe kusan watanni tara ana yaki a Sudan, shugaban sojin kasar Abdel Fa...

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam Documentary Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Establishment

Send a message to Imam Documentary Hausa:

Share