22/08/2025
Jiya 21 ya cika shekaru 39 inda fiye da mutane 1,700 s**a rasa rayukansu cikin barci bayan da tafkin Nyos dake arewa maso yammacin Kamaru ya fitar da gajimare mai gubar carbon dioxide a daren 21 ga watan Agustan shekarar 1986.
Mutanen kauye da s**a tsira daga bala’in sun tashi sun ga ‘yan’uwansu da makwabta da abokan arziki sun mutu. Fiye da dabbobi 3,000, da tsuntsaye da kwari, suma sun halaka.