Matasa Masu Kishin Arewa

Matasa Masu Kishin Arewa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Matasa Masu Kishin Arewa, Art, Zaria.

Assalamu Alemum Warahmatullah.Ina yiwa dukkan yan,uwa Musulmi duniya tare daku barka Da sallah.fatan AllahYakarba ibadun...
27/05/2026

Assalamu Alemum Warahmatullah.
Ina yiwa dukkan yan,uwa Musulmi duniya tare daku barka Da sallah.fatan Allah
Yakarba ibadunmu yabamu Zaman lfy da kwanciyar hankali
Tare da jan hankali karemu baki daya.
Dayawa matasa samari da yan Mata mun dauki ranar sallar idi
Ranar more rayuwa da Sharholiyace kawae
Ya yan,uwa masu albarka
Ina mana nasiha da muji tsoron
Allah.mukiyaye dokokinsa
Kada mugode masa tahanyar
Saba masa,kada mununa farin Cikinmu tahar saba masa
Kada muyi abun da mutuncin
Muzae zube,komu cutar da Wanin mu
Kada kakirawo yar wani gidanka
Ko dakinka dasunan yawon Sallah ko wata alaka.
Kema kada kibi wani gida,daki
Ko shago dasunan yawon sallah
Ko wata alaka.Lallai tarbiya,
Nagarta,kamala garkuwane
Garemu.sanarwa daga
SALMAN SALIHU UMAR(P.R.O)
Karkashin jogorancin
Wannan gungiya mai
AlbarkA(M.K.A)

Za a iya inganta zaman lafiya a cikin al’umma ta hanyar ilimin addini ta hanyoyi masu yawa, kamar haka:Koyar da tsoron A...
20/05/2026

Za a iya inganta zaman lafiya a cikin al’umma ta hanyar ilimin addini ta hanyoyi masu yawa, kamar haka:
Koyar da tsoron Allah
Ilimin addini yana koya wa mutane tsoron Allah da gujewa zalunci, wanda hakan ke rage rikici da laifi a cikin al’umma.
Karfafa ɗabi’u nagari
Addini yana koyar da gaskiya, haƙuri, yafiya, tausayi da mutunta juna. Waɗannan ɗabi’u suna kawo zaman lafiya.
Hana tashin hankali da fitina
Ilimin addini yana nuna muhimmancin zaman lafiya tare da hana faɗa, ƙiyayya da cutar da mutane.
Ƙarfafa haɗin kai
Addini yana umartar mutane su haɗa kai, su taimaki juna kuma su zauna kamar ’yan’uwa.
Wayar da kai ga matasa
Koyar da matasa ilimin addini yana taimaka musu su guji miyagun ayyuka kamar sata, shaye-shaye da rikici.
Koyar da adalci
Addini yana koyar da yin adalci tsakanin mutane ba tare da nuna bambanci ba, wanda ke kawo kwanciyar hankali.
Magance sabani cikin hikima
Ilimin addini yana koya wa mutane su sasanta cikin lumana da amfani da shawara maimakon tashin hankali.
A taƙaice, ilimin addini yana gina al’umma mai ɗabi’a ta gari, haɗin kai da zaman lafiya.

Muhimmancin zaɓe ga ɗan ƙasa yana da yawa:Zaɓen shugabanni: Zaɓe yana ba ɗan ƙasa damar zaɓar shugabannin da za su wakil...
17/05/2026

Muhimmancin zaɓe ga ɗan ƙasa yana da yawa:
Zaɓen shugabanni: Zaɓe yana ba ɗan ƙasa damar zaɓar shugabannin da za su wakilce shi.
Ƙarfafa dimokiraɗiyya: Yana tabbatar da cewa gwamnati tana samun ikon ta ne daga jama’a.
Bayar da ra’ayi: Zaɓe hanya ce ta nuna ra’ayin mutum kan yadda ake gudanar da mulki.
Kare haƙƙi: Ta hanyar zaɓe, ana iya zaɓar shugabanni masu kare muradun al’umma.
Canji mai kyau: Zaɓe yana ba da damar sauya shugabanci idan ana buƙatar ingantawa.
A taƙaice, zaɓe ginshiƙi ne na ‘yanci da ci gaban ƙasa.

🔥 DA DUMI-DUMI 🔥😂😂 Jam’iyyar APC ta kwace wa Honorable Wada takarar kujerar Majalisar Tarayya ta Sabon Gari/Zaria Federa...
14/05/2026

🔥 DA DUMI-DUMI 🔥

😂😂 Jam’iyyar APC ta kwace wa Honorable Wada takarar kujerar Majalisar Tarayya ta Sabon Gari/Zaria Federal Constituency.
Shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun tsayar da Honorable Sadiq Ango a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na Sabon Gari/Zaria Federal Constituency.

Me za ku ce game da wannan mataki?

11/05/2026

Duk ɗan ƙasa ya kamata ya mallaki katin zaɓe domin zaɓen shugaba nagari.

11/05/2026

Duk ɗan ƙasa ya kamata ya mallaki katin zaɓe domin zaɓen shugaba nagari.

04/05/2026

Ko da yake Peter Obi ba Musulmi ba ne shin kuna ganin zaku iya zaɓen sa a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027?

04/05/2026

Wane irin aiki ne Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Najeriya da zai sa talakawa su sake zaɓen sa a shekarar 2027?

04/05/2026

Wai Rabiu kwankwaso mene ne ya taba yi wa Najeriya da zai sa talaka ya dace ya zaɓe shi a 2027?

04/05/2026

Wai Atiku Abubakar mene ne ya taba yi wa Najeriya da zai sa talaka ya dace ya zaɓe shi?

Address

Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Matasa Masu Kishin Arewa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category