DAN IYAN GOBIR

DAN IYAN GOBIR The Dan Iyan Gobir Is a Statistician but deeply committed to the History of Gobir Kingdom.

10/06/2026

Babba matsalar arewa itace yan arewa. Allah Ya hadamu zama da miyagun Mutane wadanda basa tsoron Allah, sunfi martaba Kabilarsu fiye da girmama rayukkan Bayin Allah. A Kasar nan Arewa itace mafi girma da yawan jama'a, amma yawan mu bai amfana mana komai ba.
Arewa ce mafi koma baya a duk fannonin rayuwa. Munfi kowane bangare jahilci, talauci da churutukka. Idan Dan Arewa ka shiga Kudu, suci mutuncinka, su tsangwame ka. Kullun idan ka dubi wasu shafukkan Jaridun Kasar nan ko Social media, Kai Dan Arewa ruwan bama-bamai na zagi da tsinuwa da la'ana ce suke zazzaga maka a kowace sa'a.
Anan Arewa gida, ta'addanci ya sami gindin zama. Duk Safiya sai ka ji yan uwanmu (yamu-yamu yan arewa) suna kashe Mutane bigairi-haqqin, ko su k**a Mutane su zuba cikin daji su daure su tamkar Dabbobi domin biyan kudin fansa. Abin ban takaici shine suna keta haddin Mata da kananan yara kuma su dora akan Social media Duniya na kallo saboda Dabbanci.
A bangaren gwamnati ta gaza a kowane mataki. Matsalar Tsaro ta koma wata hanya mafi saukin kawowa yan siyasa da jami'an gwamnati miyagun kudade kuma baza su so wannan matsalar ta kare ba.
Al'amari mafi muni ga Dan Arewa yau shine, hatta da wasu Mallaman Addini marasa imani, tausayi da tsoron Allah, suna amfana sosai da zubarda jinin Bayin Allah. A nan Arewa zaka hangi Malami akan Mimbari cikin Masallacin Allah, yasha rawani, ga gemu chike chas da hurhura, Amma ya daure yawa Allah da Manzon Allah tawaye, yana kokarin kunyata kansa, ta hanyar kokowa da Ayoyin Qur'ani da Hadissai wajen halatta haram, da goyon bayan ta'addanci, basu kariya ko nemawa yan ta'adda mafita, saboda yana amfana da kudin jini ko kuma yan ta'addar Kabilarsu ce, Kaicho!
Babu abin tausayi yau tamkar Talakkan Arewacin Nigeria. Dole kayiwa Allah da Manzonsa da'a. Doli kayiwa Gwamnati da hukumominta da'a, doli ka biya haraji ga Gwamnati da yan ta'adda. Idan Dan ta'adda ya kashe ka ya kashe banza amma idan ka kashe Dan ta'adda jami'ai su kinkimo ka su garqame wai ka dauki doka a hannunka!
Za ka chi karo da Yan gata fulani Barayin daji a social media suna dukan wadanda s**a kamo, ko selfie tare da kudade amma gwamnati bata iya maganinsu, abin dariya yau ka zagi S A Mai gajeren wando ko Kansilan Kauyenku a social media, lokacin zaka ga yadda za suyi amfani da kowane irin technology da Intelligence wajen damko ka da hukunta ka Kai tsaye.
A karshe mafi shairin Dan Arewa yau shine wanda ke kallon matsalar Tsaro ta hanyar Siyasa ko kabilanci. Shi bai amfana da ko sisi cikin matsalar, amma tun da yan Kabilarsa ke ta'addanci zai zo a social media Yana zare ido da kumfan baki wajen kariyarsu da zargin wadanda ake kashewa da k**awa don biyan kudin fansa ko masu nemar wa Mutanen su mafita dagga azzalumai.
Ina goyon bayan kalamai na hikima daga Maigirma Sarkin Kabin Argungu da cewa Mutane su tashi tsaye su tanadi Mak**ai domin kare rayuwarsu da dukiyarsu da mutuncin kansu dana iyalansu, saboda wai ance Danbun yayiwa gwamnati yawa, saboda haka ba ta iya samar mishi da Mai.
da rayuwa su ke kaika Kotu ko gidan gyaran hali.
Mai Rai zai dandani mutuwa. Kada mu zaunar wani Dan iska ya keta alfarmar iyalinka Wai saboda yana rike da Wani Makamin da N700,000.00 ke iya saye.
Ya Allah Ka taimake mu wajen kariyar rayukkan mu da mutuncin iyalan mu🤲

Wannan shine Malamina.Malami Bafaden Allah.Allah Shi kara maka son Manzon Allah. Allah Shi kara Zuhudu, kusanci da Taqaw...
17/12/2025

Wannan shine Malamina.

Malami Bafaden Allah.
Allah Shi kara maka son Manzon Allah. Allah Shi kara Zuhudu, kusanci da Taqawa. Allah Shi Dora kyawawan Ayukkan alkhairinka a Mizanin Hasanati.

Sheikh Dr Muhammad Isah Talata Mafara ya himmatu sosai wajen karantarwar addini tsantsa bisa tafarkin Annabin Rahama.
Mallam Ba girman Kai, Mallam baya Fadanci gidan kowa. Mallam baya boye Gaskiya domin neman yardar wani ko yabon mai yabo.

Yau shekara goma sha biyu Ina karatu wajensa ban taba Jin Sheikh yayi zagi ko s**a, ko cin zarafi ko batanci ga wani ba, matukar dai ba addinin Allah ka taba ba.

Mallam ina yima fatan alkhairin Allah.
Allah Shi tsare mutuncinka Allah Shi kara maka rufin asiri, lafiya da rayuwa Mai albarka.

Su Kuma Masu Neman yardar wanin Allah, Fadawa, Mallaman Social Media, Maciya amanar ilimi, masu Goyon bayan Ta'addanci da zubda Jinin Bayin Allah, tareda nemarwa Yan Ta'adda mafita domin bidar kudi ko Muqami Ido rufe: Ya Allah Ka barsu da Dubarar Kansu.

Ya Allah Ka Isamma Yan uwanmu Marayi, Zawarawa, Yan gudun Hijira da Dubban Mutane da ke yanzu haka hannun Azzalumai daure a cikin Daji.

07/12/2025

Adamu Bashir Gobir wrote.

A Rebuttal: On Victims' Rights, Islamic Integrity of Negotiations, and the Minister's Constitutional Oath
A REJOINDER TO MIKA'IL BARAU'S
"Reaction to Kperogi's WHY MATAWALLE IS STILL DEFENCE MINISTER: AN ISLAMIC AND POLICY PERSPECTIVE"

MIKAI BARAU's previous defense of Minister Matawalle, while draped in Islamic legalism and strategic talk, collapses under the weight of three fundamental omissions:
The rights of the victims, the Islamic preconditions for legitimate negotiation, and the sacred constitutional oath of office. It is a defense that is disturbingly silent on justice for the aggrieved and lopsided applications of the principles it claims to uphold. Let me treat each here under:

1. The Asymmetric Morality: Defending Alleged Criminals While Ignoring Victims
The article engages in a profound ethical imbalance.It vigorously applies the Islamic principle of "innocent until proven guilty" and the need for "evidence" to protect the honor of an accused official. But, simultaneously, it ignores the most foundational Islamic imperative: the right to justice, security, and protection for the victims.

The victims of banditry—the murdered, the abducted, the orphaned, the displaced—are not "claimants" in a hypothetical court case against the minister. They are the primary constituency of the state's security apparatus. Their rights (Huquq al-'Ibad) are paramount in Islam. A defense that meticulously constructs a theological shield for a powerful official while offering no equivalent vigorous demand for justice for the powerless victims is not justice; it is selective justice masquerading as piety. The Quranic command (4:135) to "stand firmly for justice, as witnesses to Allah, even against yourselves or your parents and relatives" applies foremost to protecting the weak from the strong.

2. The Islamic Invalidity of "Negotiations" That Negate Justice
The article loosely advocates"dialogue" as a strategic tool, invoking examples from ot

Address

Bado New Layout Sokoto
Sokoto
810321

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DAN IYAN GOBIR posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share