Huda-Huda Update

Huda-Huda Update News, entertainment, adverts and other media content

19/08/2026

Barkan mu da safiyar Laraba, ga kuma Kanun Labarun Tsakiyar Mako

YAKIN NEMAN ZABE YA FARA DAGA YAU, A HUKUMANCEBisa jaddawalin da Hukumar Zaben Najeriya ta fitar, a yau ne a ka lamincew...
19/08/2026

YAKIN NEMAN ZABE YA FARA DAGA YAU, A HUKUMANCE

Bisa jaddawalin da Hukumar Zaben Najeriya ta fitar, a yau ne a ka lamincewa jam'iyyu su fara gangamin yakin neman zabe a lungu da sako na kasar nan.

Wannan zai kunshi tallata Yan Takara da jam'iyyun su ka tsayar, da kuma bayyanawa jama'a manufofi da tanaje-tanajen da jam'iyyun ke da su domin kawo sauyi ga rayuwar da al'umma ke ciki.

Sai dai kuma tuni ma su nazarin harkokin siyasa sun fara hasashen cewa gangamin na wannan kakar zaben zai sha banban da na baya, musamman ganin yadda wasu Yan siyasar da magoya bayan su ke daukar abubuwa da zafi.

Amma har hakan, Yan Najeriya na dakon ganin sauyi wajen kalaman da a ka saba ji a lokacin gangamin yakin neman zabe, musamman ta fuskar daukar alkawurran da ba za a cika ba, da wasa da sha'anin tsaro, da kalaman tunzura jama'a da makamantan su.

SHUGABA TINUBU ZAI JAWABI GABAN ZAUREN MAJALISAR DINKIN DUNIYAShugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi...
19/08/2026

SHUGABA TINUBU ZAI JAWABI GABAN ZAUREN MAJALISAR DINKIN DUNIYA

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban na Najeriya zai jawabin ne a lokacin zaman Majalisar karo na 81 a ranar 23 ga watan Satumba.

Zai kasance daya daga cikin wakilan kasashe 193 da su ke cikin Majalisar Dinkin Duniya, wanda tattaunawar za ta karkata a kan manyan kalubale da duniya ke fuskanta, kamar su matakan kariya ga yanayi, da tanaje-tanajen yakar barkewar annoba.

Thanks to God for another Wednesday
19/08/2026

Thanks to God for another Wednesday

MASARAUTAR KATSINA TA SA RANAR NADIN SARAUTUN KARSHI DA BEBEJIMajalisar Masarautar Katsina ta sanya ranar Asabat, 29 ga ...
18/08/2026

MASARAUTAR KATSINA TA SA RANAR NADIN SARAUTUN KARSHI DA BEBEJI

Majalisar Masarautar Katsina ta sanya ranar Asabat, 29 ga watan Ogusta na shekara ta 2026 domin gudanar da bukin nadin Alhaji Sanusi Kabir Usman matsayin Karshin Katsina, Hakimin gundumar Shinkafi.

Haka zalika a ranar Asabat din dai Masarautar za ta nada Alhaji Abdulrashid Nuhu Yashe matsayin Bebejin Katsina, Hakimin gundumar Kusada.

Dukkanin wannan dai na zuwa ne bayan amincewar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dakta Abdulmumini Kabir Usman Kan wannan cigaban da a ka samu.

Wata sanarwa mai dauke da rattaba hannun Sakataren Masarautar, Isah Ali Kankia, ta bayyana cewa za a gudanar da bukin nade-naden ne da misalin karfe goma na safe.

Daga nan sai sanarwar ta taya sabbin Hakiman murna, ta kuma yi addu'ar samun lafiya da zaman lafiya a cikin al'umma baki daya.

18/08/2026

A shakata da Marigayi Narambada a cikin wakar Gulbi Ka Wuce Kwalfewa"

KATSINA NALVEJ GETS NEW LEADERSHIP Executive officers of Katsina state Chapter of National League of Veteran Journalists...
18/08/2026

KATSINA NALVEJ GETS NEW LEADERSHIP

Executive officers of Katsina state Chapter of National League of Veteran Journalists, NALVEJ, have been sworn in.

The oath of office and pledge was administered on the new officials by a state Counsel, Hussain Musa Yandoma at a brief ceremony held at the conference room of the Department of Chieftaincy Affairs in Katsina.

Officers sworn in are Mansir Lawal Kaware as Chairman and Hassan Muhammad Tukur as Secretary.

Others include Rabi'u Ibrahim as Vice Chairman, Hassan Bako as Assistant Secretary, Umar Isyaku as Treasurer, Muntari Abba Usman as Financial Secretary, Sani Ahmed Fago as Auditor while Ma'aruf Zubairu become the Public Relations Officer of the association.

The rest are Lawal Gwanda as Ex-officio one, Bello Mamman as Ex-officio two and Nana Lili as Ex-officio three.

Speaking shortly after the swearing in, the new State Chairman, Mansir Lawal Kaware assured to discharge the duties entrusted in him with honesty and high sense of responsibility.

He asked members to uphold professionalism for the emerging journalists to emulate the Veterans with the zeal to serve the communities.

KUNGIYAR KWADAGO TA NADA SHUGABAN RIKO A JIHAR KATSINA Kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Katsina ta nada Kwamared Na...
17/08/2026

KUNGIYAR KWADAGO TA NADA SHUGABAN RIKO A JIHAR KATSINA

Kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Katsina ta nada Kwamared Nasiru Wada Mai'adua a matsayin Shugaban Riko na jiha.

Wannan kuwa na zuwa ne sakamakon saukar Shugaban Kungiyar, Hussaini Hamisu Yanduna, wanda ya samu matsayin Babban Sakatare a cikin gwamnatin jihar Katsina.

Kafin wannan chanjin, Kwamared Nasiru Wada Mai'adua shi ne Shugaban Kungiyar Ma'aikatan Kananan Hukumomi (NULGE) na jihar Katsina.

MALAMAN JAMI'AR KADUNA FIYE DA 200 SUN AJIYE AIKIRahotanni na nuni da cewar kusan Farfesoshi da sauran Malamai 200 ne su...
17/08/2026

MALAMAN JAMI'AR KADUNA FIYE DA 200 SUN AJIYE AIKI

Rahotanni na nuni da cewar kusan Farfesoshi da sauran Malamai 200 ne su ka bar koyarwa a Jami'ar jihar Kaduna, saboda tarbarbrewar tsari da yanayin gudanar da aiki.

Kari bisa ga lalacewar yanayin aikin, Malaman kuma na kokawa da rashin aiwatar da yarjejeniyar da a ka kulla tsakanin Kungiyar Malaman Jami'a, ASUU, da Gwamnatin Tarayya a shekara ta 2025.

Tuni dai har Kungiyar Malaman Jami'a, reshen Jami'ar ta jihar Kaduna, ta bayar da wa'adin makonni biyu ga Hukumomin Jami'ar da sauran ma su ruwa da tsaki na a aiwatar da yarjejeniyar ko kuma za su tsunduma yajin aiki na sai mama-ta-gani.

Shugaban Kungiyar Malaman Jami'ar (ASUU) reshen Jami'ar jihar Kaduna, Abubakar Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labaru da a ka gudanar a Sakatariyar Kungiyar da ke farfajiyar Jami'ar.

17/08/2026

Shugaban Kungiyar Gangamin Goyon Bayan Jam'iyyar APC daga Kananan matakai, Honorable Nuhu Umar Sani Kankara, ya ce nera miliyan goma goma da za a ba Kwamitocin Al'umma, kudi ne na bunkasa rayuwar al'umma, ba siyasa ba.

Address

No. 04, Estate Staff Quarters, Hassan Usman Katsina Polytechnic
Katsina
820102

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Huda-Huda Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category