Komai Da Komai TV

Komai Da Komai TV Shafin da yake kawo muku komai daga fadakarwa, wa'azi, nishadi, kasuwanci da rayuwar yau da kullum

And the salary is too small for workers,This is Nigeria for you
25/07/2025

And the salary is too small for workers,
This is Nigeria for you

Allah ya jikan musulmi
13/07/2025

Allah ya jikan musulmi

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci al’umma da su kasance cikin shiri da himma wajen kare kansu daga hare-haren ƴan daba da m...
02/07/2025

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci al’umma da su kasance cikin shiri da himma wajen kare kansu daga hare-haren ƴan daba da masu ƙwacen waya da ke cigaba da addabar wasu sassan jihar.

An ruwaito cewa Kwamishinan Tsaro na jihar Kano, Air Vice-Marshal Ibrahim Umaru (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi.

Kwamishinan ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ƙara samun yawaitar aikata laifukan ƴan daba da masu ƙwacen waya a wasu yankunan birnin Kano, yana mai jan hankalin al’umma da kada su zura ido, ko su kasance cikin fargaba har su kasa kare kansu.

Ya kuma ce yanzu ba lokaci bane da matasa da ƴan bijilanti za su rika jin tsoro ko gujewa ƴan daba da masu ƙwacen waya ba, yana mai cewa dole matasa su tashi tsaye su kare kansu da iyalansu daga wannan barazana.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, kamata yayi kowa ya bayar da tasa gudunmawa wajen magance matsalar, ba wai a tsaya ana zagin gwamna a kafafen sada zumunta ba, inda ya ce lokaci ne da za a fuskanci ƴan daba da takamaiman mataki in har sun kawo farmaki.

Haka zalika, ya buƙaci al’umma da su riƙa bayar da bayanai ga hukumomin tsaro kan duk wani motsin da s**a ga yana iya zama barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunansu.

Innalillahi wa inna ilaihi RajiunMun samu labarin rasuwar, Alhaji Aminu Dantata Margayin ya rasu yana da shekara 94.Alla...
28/06/2025

Innalillahi wa inna ilaihi Rajiun

Mun samu labarin rasuwar, Alhaji Aminu Dantata
Margayin ya rasu yana da shekara 94.
Allah ya jikansa da sauran mamatanmu!!!
28th June 2025
3rd Al_Muharram 1447

Ranar Dimokuraɗiyya: Zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa ta ɓarke yanzu haka, a jihar Legas, duk da yawan jami'an tsaron...
12/06/2025

Ranar Dimokuraɗiyya: Zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa ta ɓarke yanzu haka, a jihar Legas, duk da yawan jami'an tsaron da aka jibge.

Wannan shi ake kira Zankala Koki (Praying Mantises)
10/06/2025

Wannan shi ake kira Zankala Koki (Praying Mantises)

06/06/2025

is beautiful
Follow for more

ME AKE FADA YAYIN YANKA DABBAR LAYYA?Assalamu alaikum. mallam dan Allah ina son sanin addu'ar da ake yi lokacin yan kan ...
31/05/2025

ME AKE FADA YAYIN YANKA DABBAR LAYYA?

Assalamu alaikum. mallam dan Allah ina son sanin addu'ar da ake yi lokacin yan kan dabbar layya. Nagode.
__________________________________________________

الحمد لله

AMSA: Addu'ar da ake yi yayin yanka dabbar layya itace. Bayan mai yan kan ya dora kafarsa akan wuyan dabbar sai yace:

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻨﻲ ‏. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ مني .
__________________________________________________

Idan kuma zai hada layyar da iya lansa. Sai yace:

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻨﻲ ‏. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ مني و آل بيتي.
__________________________________________________

Idan kuma wani ne ya wakilta mai yan kan ya yan ka masa dabbar sai yace:

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ( ﻋﻦ ﻓﻼﻥ ‏) ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻦ (ﻓﻼﻥ) ﻭﺁﻝ (ﻓﻼﻥ)
__________________________________________________


A duk inda aka ga an saka wannan fulaan (فلان) din sai a kira sunan mai layyar. "Fulaan" yana nufin "WANE"

TARJAMA
___________👇

Bismillaah, WALLAHU akbar, ALLAHUMMA haaza min ka wa laka, haaza ‘anni. ALLAAHUMMA taqabbal minni wa aali baiti.
__________________________________________________

Ko kuma a maimakon cewa _ ALLAAHUMMA taqabbal minni wa aali baiti.

Mutum yana iya ambatar sunansa wato misali idan sunansa *MUS'AB* sai yace _ ALLAAHUMMA taqabbal min mus'ab wa aali mus'ab_Kamar yan da( ANNABIﷺ)ya ambaci sunansa da iyalansa da kuma al'ummarsa.
__________________________________________________

Idan kuma wani ne ya wakilta mai yan kan ya yanka masa sai yace.👇

BISMILLAAH, WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMA haaza min ka wa laka, haaza ‘an [ fulaan], ALLAAHUMMA taqabbal min [fulaan] wa aali [sai kira sunan mai layyar].
__________________________________________________

Amma fa abin lura anan shine cewa (BISMILLAAH) kadai ne wajibi. Sauran duk mustahabbi ne ba dole bane.
__________________________________________________

Idan ka sanar da al'umma kaima ALLAH zai saka ka acikin ladan. Dan ALLAH a yada sosai sako yaje wa kowa.duk wanda ya gani yai like ya tura don sakon yaje inda ake so.
__________________________________________________

Domin qarin bayani: Al- Bukhaari (5565), Muslim (1966), Muslim (1967), Al-Tirmizi (1521), Sharhul Mumti (7/492). WALLAHU a'alam.
__________________________________________________

ALLAH ya h**e mana abin layya.👏

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

Address

Kano
Kano
700251

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Komai Da Komai TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category