23/06/2026
Cikin Hotuna: Yadda Tawagar Shugaban Kasa Ta Gabatar Da Ta'aziyya Ga Farfesa Pakistan.
Mai Girma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aiko da wata babbar tawaga karkashin jagorancin Babban Mai Taimaka Masa na Musamman, H.E. Ibrahim Kabir Masari.
Sauran membobin tawagar sun hada da Ministan Gidaje da Raya Birane, Engr. Muttaqha Rabe Darma; Shugaban Hukumar Ilimin Almajirai, Dr. Muhammad Sani Idris; da kuma Jami'in Gudanarwa na Hukumar NEPAD na Kasa, Malam Jabiri Salisu Abdullahi. Sun zo ne domin su mika ta'aziyya ta musamman ga Farfesa Abdullahi Sale Pakistan, bisa ga rasuwar matarsa.
A jawabin Shugaban Kasa da Babban Mai Taimaka Masa kan Harkokin Siyasa da Sauran Al'amura, H.E. Ibrahim Kabir Masari, ya gabatar, ya bayyana cewa: "Mai Girma Shugaban Kasa ya turo mu ne domin mu jajantawa daukacin al'ummar Jihar Kano, ba wai Farfesa Pakistan kadai ba, tare da yi wa marigayiyar addu'a ta musamman."
Yayin wannan ziyara, tawagar shugaban kasa ta samu kyakkyawar tarba daga manyan malamanmu na Jihar Kano, da masu ruke sarauta, da sauran masoya.
An kammala ziyarar ta'aziyyar da yi wa kasa addu'ar Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya, kuma ya magance mana abubuwan da s**a fi karfinmu.
Muna addu'ar Allah ya mayar da wannan tawagar gida cikin koshin lafiya, ya ba su nasara a dukkan al'amuransu. Allah ya ba kasarmu lafiya da zaman lafiya, ya kuma yi mana maganin duk abin da ya fi karfinmu. Amin.