JARIDAR ZAMANI

JARIDAR ZAMANI Kafar sadarwa ta Zamani da zamu dinga kawo maku labarai na halin da yankunanku ke ciki da ma kasa da Kuma Duniya baki daya

SANARWAR MANEMA LABARAIKaramar Hukumar Kumbotso06/08/2026“Haƙƙin al’umma ne mu tabbatar musu da tsaron rayukansu da duki...
06/08/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI
Karamar Hukumar Kumbotso
06/08/2026

“Haƙƙin al’umma ne mu tabbatar musu da tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.”

Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Jihar Kano sun kai wa Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso ziyara tare da ba shi lambar yabo.

Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Jihar Kano sun kai wannan ziyara ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kamfanin Danfodio Islamic Health Center da ke Ɗorayi, Malam Abdullahi Idris Ɗanfodio, domin gabatar da ƙudirorinsu da kuma irin ayyukan da suke gudanarwa, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da shugabancin Karamar Hukumar Kumbotso.

A jawabinsa, mai magana da yawun ƙungiyar ya bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne domin daƙile yawaitar faɗan daba da kuma ƙwacen waya da ake samu a unguwanni 28 da ke faɗin Jihar Kano, musamman a ƙananan hukumomin Kumbotso, Kano Municipal, Gwale da Ungogo. Ya ƙara da cewa babban manufarsu ita ce yaƙi da faɗan daba da masu aikata ƙwacen waya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma.

Shi ma Shugaban ƙungiyar, Dr. Abdullahi Idris Ɗanfodio, ya bayyana cewa sun kawo wannan ziyara ne domin ƙarfafa alaƙa da Karamar Hukumar Kumbotso, tare da neman goyon bayanta wajen yaƙi da ayyukan bata-gari da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso, Hon. Ali Musa Danmaliki Hardworker, ya bayyana matuƙar farin cikinsa da yadda ƙungiyar ke jajircewa wajen gudanar da wannan aiki mai amfani ga al’umma. Ya ce gwamnatin ƙaramar hukumar a shirye take ta ba ƙungiyar dukkan goyon bayan da take buƙata domin a daƙile duk wani nau’in ta’addanci da aikata laifuka, tare da tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban ya ƙara da cewa tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba tun daga hawanta mulki. Saboda haka, ya bayyana ƙungiyar a matsayin abokiyar aiki mai muhimmanci wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce:

“Haƙƙin al’umma ne mu tabbatar musu da tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.”

A ƙarshen taron, Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Jihar Kano sun karrama Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso da lambar yabo, bisa gudummawar da yake bayarwa musamman a fannin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Signed: ✍️
Alawiyya Wada Isah
Information Officer
Kumbotso LG

03/08/2026

Shugaban ƙaramar hukumar kumbotso Hon Ali musa Ɗanmaliki Hardworker yayin ƙaddamar da shirin SMC na rabon magani kyauta.

SANARWAR MANEMA LABARAIKumbotso LG03/08/2026Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker, Ya Ƙa...
03/08/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI
Kumbotso LG
03/08/2026

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker, Ya Ƙaddamar da Ɗaukar Ma'aikatan Rabon Maganin SMC Su 510

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker, ya ƙaddamar da shirin ɗaukar ma'aikatan rabon maganin Seasonal Malaria Chemoprevention (SMC) guda 510, domin gudanar da rabon maganin rigakafin zazzabin cizon sauro ga yara a faɗin ƙaramar hukumar.

Kamar yadda Jami'ar Yaɗa Labarai ta Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Alawiyya Wada Isah, ta bayyana wa manema labarai, shugaban sashen lafiya na ƙaramar hukumar, Malam Lawan Ahmed Getso, ya yi kira ga ma'aikatan da aka ɗauka da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, ƙwarewa da jajircewa. Ya kuma buƙace su da su yi kyakkyawar mu'amala da ma'aikatan lafiya da kuma al'ummar da za su yi wa hidima.

Malam Lawan Ahmed Getso ya ƙara da cewa za a fara horas da ma'aikatan kan yadda za su gudanar da rabon maganin yadda ya kamata, sannan daga gobe da jibi za a tura kowannensu zuwa wurin aikin da aka ware masa domin fara gudanar da aikin.

A nasa jawabin, Kansilan Lafiya na Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Haruna Shera, ya bayyana cewa wannan aiki yana da matuƙar muhimmanci wajen kare lafiyar yara daga cutar zazzabin cizon sauro. Ya kuma yi kira ga waɗanda s**a samu wannan damar da su ɗauki aikin da muhimmanci tare da nuna ƙwarewa da amana. Ya jaddada cewa wannan dama ta samu ne bisa kulawa da jajircewar shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker, wajen tallafa wa al'ummar Kumbotso.

A jawabinsa, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker, ya yi wa mahalarta taron maraba tare da taya waɗanda aka zaɓa murnar samun aikin. Ya bayyana cewa idan aka kammala aikin kuma aka biya haƙƙoƙinsu, hakan zai zama wata hanya ta samun jarin da za su iya amfani da shi wajen bunƙasa rayuwarsu da ta iyalansu.

A ƙarshe, shugaban ƙaramar hukumar ya roƙi mahalarta taron da su ci gaba da mara wa Jam'iyyar APC baya tare da zaɓenta daga sama har ƙasa a babban zaɓe mai zuwa, idan Allah Ya kai mu.

Signed: ✍️
Alawiyya Wada Isah
Information officer
Kumbotso LG.

Aljana ta hana Jarumi Adam A zango zaman aure domin ya saki matarsa ta shida kuma 'yar uwarsa 'yar kannywood.Allah ya ky...
31/07/2026

Aljana ta hana Jarumi Adam A zango zaman aure domin ya saki matarsa ta shida kuma 'yar uwarsa 'yar kannywood.

Allah ya kyauta ya sa hakan ya zama alkhairi.
゚ ゚viralシ

"Sai Mun Share Tarihin Akidar Kwankwasiyya a Kano,Kamar Yadda Ake Gani Har Yanzu Muna Sanya Jar Hula, Amma Tamu Ta 'Yanc...
31/07/2026

"Sai Mun Share Tarihin Akidar Kwankwasiyya a Kano,Kamar Yadda Ake Gani Har Yanzu Muna Sanya Jar Hula, Amma Tamu Ta 'Yanci Ce, Ba Ta Kangin Bauta Ko Maguzanci Ba" – Kwamishina Kwamared Waiya..

Kwamishinan yada labarai da Al'amuran cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya shaida hakan ne domin mayar da martani kan yan Kwankwasiyya dake Ikirarin cewa sune silar nasarar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zama gwamna.

SANARWAR MANEMA LABARAIKumbotso LG30/07/2026Tsaro Ya Samu Tagomashi a Faɗin Ƙaramar Hukumar Kumbotso Ƙarƙashin Jagoranci...
31/07/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI
Kumbotso LG
30/07/2026

Tsaro Ya Samu Tagomashi a Faɗin Ƙaramar Hukumar Kumbotso Ƙarƙashin Jagorancin Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker

A ci gaba da ƙoƙarin haɓaka harkokin tsaro a Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Shugaban Ƙaramar Hukumar kumbotso Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker, ya gyara motocin jami’an tsaro guda tara domin ƙarfafa ayyukan tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙaramar hukumar.

Motocin da aka gyara sun haɗa da na ofisoshin ‘yan sanda guda bakwai, da na Civil Defence, Vigilante, da Hisbah, domin ba su damar gudanar da sintiri a lungu da saƙo da kuma yaƙi da masu aikata laifuka.

Da yake jawabi a wajen taron, Mai Bai wa Shugaban Ƙaramar Hukuma Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Usman Zakari, ya bayyana cewa bisa umarnin shugaban ne aka tattara motocin domin a tantance halin da suke ciki. Ya ce an tarar da su cikin mawuyacin hali, inda aka ja su zuwa wajen gyara, aka sake musu kwaskwarima tare da sanya sababbin tayoyi, gyaran injina da sauran muhimman sassa.

Ya ƙara da cewa motocin yanzu sun dawo cikin tamkar sababbi kuma za su taimaka sosai wajen shiga lungu da saƙo domin gano masu aikata laifuka da kuma tabbatar da doka da oda. Haka kuma ya bayyana cewa wannan shi ne farkon irin waɗannan ayyukan da shugaban ke shirin aiwatarwa.

Shi ma Daraktan Kuɗi da Mulki na Ƙaramar Hukumar Mustafa Uba Minjibir ya bayyana cewa Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker ya yi koyi da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wajen bai wa harkokin tsaro muhimmanci. Ya ce wannan aiki ba ƙarami ba ne, kuma akwai wasu manyan tsare-tsare na ƙarfafa tsaro da za a aiwatar nan gaba a ƙarƙashin jagorancin shugaban.

A nasa jawabin, DPO na Kumbotso Division CSP Nasiru Mahmud ya bayyana wannan rana a matsayin ranar farin ciki ga jami’an tsaro. Ya ce sun daɗe suna fatan a gyara motocin amma hakan bai samu ba sai yanzu. Ya yi alƙawarin cewa jami’an tsaro ba za su ba shugaban kunya ba wajen amfani da motocin domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma tabbatar da cewa gyaran da aka yi wa motocin ba gyara kaɗan ba ne, domin yanzu kowace mota tana cikin ingantaccen yanayi da za ta iya yin doguwar tafiya ba tare da wata matsala ba.

Hakimin Kumbotso, Alhaji Lamiɗo Sunusi, ya jaddada muhimmancin tsaro ga cigaban al’umma, yana mai cewa idan babu tsaro, ko neman abin masarufi zai zama ƙalubale. Ya yabawa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan gagarumin aiki, yana mai cewa ya sauke nauyin da Allah Ya ɗora masa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A jawabinsa, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Ali Musa Ɗanmaliki Hardworker, ya ce ya yi matuƙar farin ciki da kammala gyaran motocin jami’an tsaro, musamman ganin cewa rashin abin hawa ya daɗe yana hana su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki nauyin gyara da inganta motocin ne domin samar da ingantaccen tsaro a faɗin ƙaramar hukumar. Ya bayyana cewa wannan shi ne mataki na farko, kuma ba shi ne na ƙarshe ba, domin gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da duk abin da suke buƙata domin tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban ya kuma bayyana cewa kafin zuwan gwamnatinsa an daina gudanar da tarukan tsaro na yau da kullum, amma yanzu ana gudanar da taron tsaro a kowane wata tare da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki. Ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro, yana mai cewa matsalolin tsaro sun ragu matuƙa a faɗin Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

A ƙarshe, shugaban ya miƙa godiyarsa ga masu sarautun gargajiya, musamman Hakimai, Dagatai da Masu Unguwanni, bisa irin haɗin kan da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙaramar hukumar.

Signed ✍️
Alawiyya Wada Isah
Information Officer
Kumbotso LG.

PRESS RELEASEKumbotso LG23/07/2026Na’ibawa Lemon Market Traders Benefit from Mosque Renovation and Sand Filling Project ...
24/07/2026

PRESS RELEASE
Kumbotso LG
23/07/2026

Na’ibawa Lemon Market Traders Benefit from Mosque Renovation and Sand Filling Project Under the Leadership of the Chairman of Kumbotso Local Government

As part of his commitment to community development, the Chairman of Kumbotso Local Government, Hon. Ali Musa Danmaliki Hardworker, has inaugurated the renovation of the mosque at the Na’ibawa Lemon Market, alongside a sand-filling project aimed at improving the environment and creating a more conducive atmosphere for worship and commercial activities.

Speaking on behalf of the mosque committee, Malam Isah stated that for over thirty years, the market had never witnessed such a significant intervention from any local government chairman. He noted that Hon. Ali Musa Hardworker has demonstrated that he has not forgotten his roots, being a son of the market himself. He expressed profound appreciation and prayed for Allah to grant the Chairman good health, wisdom, and continued success.

Similarly, the Market King, Alhaji Abubakar Adam, commended the Chairman for undertaking such a rewarding project and prayed that Allah would bless him abundantly and grant him the strength to continue serving humanity.

Earlier, the Market Chairman, Safiyanu CK, described the occasion as a historic day for the traders, emphasizing that since the establishment of the market, no local government chairman had paid such attention to their needs until the administration of Hon. Ali Musa Hardworker.

In his remarks, the Councillor representing Na’ibawa Ward, Hon. Shehu Ɗanyaro, assured the traders that the project marks only the beginning of many developmental initiatives planned for the market, stressing that the Chairman remains committed to improving the welfare of his community.

Also speaking, the Party Chairman, Malam Rufai Manaja, said Hon. Ali Musa Hardworker has demonstrated integrity, accountability, and exemplary leadership. According to him, any leader who works to develop the community where he was raised deserves to be regarded as a role model.

The Vice Chairman of Kumbotso Local Government, Hon. Sulaiman Dauda Basarake, described the event as a joyous occasion for the people of Na’ibawa. He highlighted the importance of the market in providing employment opportunities for young people and commended the Chairman for fulfilling a long-awaited aspiration of the traders.

In his address, the Chairman of Kumbotso Local Government, Hon. Ali Musa Danmaliki Hardworker, assured the traders that the project is only the beginning, as his administration has more developmental projects planned for the market. He also expressed gratitude to the traders, particularly those who supported him and prayed for him during his years as a trader in the market. As a mark of appreciation, he honored his former mentor, Malam Umaru, by presenting him with the traditional title of Uban Gida during the event.

The Chairman further expressed concern that despite the substantial revenue generated by the market, previous administrations had neglected its development. He reaffirmed his administration’s commitment to providing the market with the infrastructure and attention it deserves.

Signed ✍️
Alawiyya Wada Isah
Information Officer
Kumbotso Local Government

 Adam ya fadi hakan ne yayin da Sanata hanga ke yunkurin barin tsarin kwankwasiyya. Me zaku ce?       ゚viralシ
14/07/2026

Adam ya fadi hakan ne yayin da Sanata hanga ke yunkurin barin tsarin kwankwasiyya.
Me zaku ce?
゚viralシ

PRESS RELEASEKumbotso LG14 July 2026Kumbotso Local Government Chairman Launches Distribution of Subsidized Fertilizer to...
14/07/2026

PRESS RELEASE
Kumbotso LG
14 July 2026

Kumbotso Local Government Chairman Launches Distribution of Subsidized Fertilizer to Farmers

The Chairman of Kumbotso Local Government, Hon. Ali Musa Danmaliki (Hardworker), officially flagged off the distribution of subsidized fertilizer to farmers across the local government area.

Speaking at the event, the Director of personnel and management of Kumbotso Local Government, Malam Mustafa Uba Minjibir, commended the Chairman for allowing the committees responsible for the exercise to carry out their duties independently, while providing only necessary guidance and corrections in line with the directives of the Governor of Kano State, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

He further expressed confidence that Kumbotso Local Government would serve as a model among the 44 local government areas of Kano State in ensuring a transparent, fair, and accountable distribution process. He emphasized that there would be no favoritism or hidden agenda, and that the fertilizer would reach genuine farmers under the Chairman’s commitment to justice and fairness.

The APC Chairman in Kumbotso, Malam Rufai Manaja, also expressed appreciation to Governor Abba Kabir Yusuf for his unwavering commitment to the welfare of the people of Kano State. He urged all beneficiaries to make proper use of the fertilizer to enhance agricultural productivity across the area.

In his remarks, the Chairman of the Community Reorientation Committee (CRC), Maraki Kyauren Yamma, thanked the Governor for making the fertilizer available at an affordable price. He noted that the initiative would boost agricultural production and contribute to reducing the cost of food across the state. He also stated that the Local Government Chairman had assured him that the distribution would be conducted without favoritism, strictly in accordance with the Governor’s directives.

The Councillor for Agriculture, Malam Mohd Ali, explained that the fertilizer distribution is being carried out in line with established guidelines. He stressed that all beneficiaries must make their payments directly at the bank, as payment by bank transfer would not be accepted.

In his address, the Chairman of Kumbotso Local Government, Hon. Ali Musa Danmaliki (Hardworker), began by expressing gratitude to Governor Abba Kabir Yusuf on behalf of the people of Kumbotso Local Government for introducing the initiative to support farmers.

He also cautioned members of the distribution committee to adhere strictly to the Governor’s directives, warning that anyone found engaging in misconduct or violating the approved guidelines would face appropriate disciplinary action.

The Chairman reaffirmed that he would not tolerate favoritism or bias, stressing that the fertilizer must reach deserving and genuine farmers.

He further reiterated that no one should pay money into any individual’s personal account. All payments must be made directly at the designated bank, as this remains the approved procedure for the exercise.

Signed

Alawiyya Wada Isah
Information Officer
Kumbotso LG✍️

14/06/2026

Hira da jarumar kannywood Nafisa Abdullahi.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JARIDAR ZAMANI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category