30/07/2026
SANARWAR MANEMA LABARAI
DARAKTAN SASHEN SADAWAR DA YADA LABARAI TA UBEC TA ZIYARCI KANO SUBEB DOMIN ƘARA ƘARFAFA HAƊIN GWIWA A FANNIN SADA ZUMUNTA TA ZAMANI
Daraktan Sashen Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kula da Ilimin Bai-Daya na Ƙasa (UBEC), Hajiya Zainab, ta jaddada aniyar hukumar wajen ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Sashen Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na Hukumar Ilimin Bai-Daya ta Jihar Kano (Kano SUBEB), domin inganta hanyoyin sadarwa na zamani da kuma ci gaban ilimin bai-daya a Najeriya.
Daraktar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta kai ziyarar aiki zuwa Sashen Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na Kano SUBEB, domin ƙarfafa haɗin gwiwa da musayar ilimi da ƙwarewa.
Hajiya Zainab ta bayyana cewa, manufar ziyarar ita ce ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin biyu, musayar dabaru da sabbin hanyoyin sadarwa, tare da raba kwarewa da kyawawan dabarun sadarwa na zamani tsakanin hukumomin SUBEB da UBEC.
Ta yaba wa ma’aikatan Sashen Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na Kano SUBEB bisa ƙwarewarsu da jajircewarsu wajen wayar da kan al’umma da kuma tallata ayyuka da nasarorin Kano SUBEB da UBEC ta hanyar kafafen yaɗa labarai da hanyoyin sadarwa na zamani.
Hajiya Zainab ta kuma bayyana cewa, tana da yakinin cewa ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin UBEC da Kano SUBEB zai taimaka wajen ƙara wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen gwamnati, ayyuka da nasarorin da ake samu a fannin ilimin bai-daya a faɗin ƙasar nan.
Da yake jawabi tun da farko, Daraktan Sashen Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na Kano SUBEB, Malam Balarabe Danlami Jazuli, ya bayyana cewa sadarwa ta zamani muhimmin ginshiƙi ne wajen isar da manufofin gwamnati, shirye-shirye, ayyuka da nasarorin da ake samu ga jama’a cikin lokaci da ingantacciyar hanya.
Ya ce, kafafen sadarwa na zamani sun sauya yadda ake yaɗa bayanai, inda suke bai wa hukumomi damar isar da saƙonni ga ɗimbin jama’a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
Daraktan ya yaba wa Babban Daraktan Hukumar Ilimin Bai-Dayan ta Jihar Kano, Malam Yusuf Kabir, bisa irin goyon bayan da yake bai wa Sashen Sadarwa da Hulɗa da Jama’a, yana mai cewa duk da cewa sabon sashe ne da aka kafa, Shugaban Hukumar ya kasance yana tafiya da sashen a dukkanin muhimman ayyukan Hukumar.
Ya bayyana cewa wannan goyon baya ya taimaka wajen ƙara wa sashen ƙarfi da damar tallata manufofi, shirye-shirye, ayyuka da nasarorin Hukumar a fannin ilimin bai-daya.
Malam Balarabe ya ƙara da cewa Kano SUBEB ta kafa tare da gudanar da kafafen sadarwa na zamani na Hukumar a shafukan sada zumunta daban-daban, ciki har da WhatsApp, Facebook, YouTube, Instagram, LinkedIn da kuma shafin yanar gizo na Hukumar, domin tabbatar da isar da bayanai cikin gaggawa da kuma ƙara kusantar Hukumar da jama'a.
Ya kuma bayyana cewa Sashen na da kyakkyawar alaƙa da gidajen rediyo da talabijin da sauran kafafen yaɗa labarai na cikin gida, inda yake shirya shirye-shiryen labarai da wayar da kai ta rediyo, talabijin da kafafen yanar gizo.
Ya ƙara da cewa Sashen na wallafa mujallar Kano SUBEB mai suna “Tushen Ilimi” a kowane zangon shekara, tare da sauran wallafe-wallafe domin sanar da jama’a kan ayyuka da shirye-shiryen Hukumar.
Daraktan ya kuma roƙi Daraktar Sashen Sadarwa da Hulɗa da Jama’a ta UBEC da ta isar da buƙatar Kano SUBEB ga Babban Sakataren UBEC, na ganin an ƙarfafa dukkan Hukumomin Ilimin Bai-Dayan Jihohi (SUBEBs) su kafa sassan Sadarwa da Hulɗa da Jama’a masu cikakken aiki.
Ya kuma nemi a samar da wani takamaiman tallafin kuɗi daga Asusun UBEC Matching Grant ko Counterpart Fund domin tallafa wa ayyukan sadarwa a jihohi, yana mai jaddada cewa ko da ƙaramin tallafi ne, zai taimaka matuƙa wajen inganta ayyukan sassan sadarwa da hulɗa da jama’a.
Hajiya Zainab ta jagoranci tawagar ma’aikatan UBEC da s**a haɗa da Mista David Aphan, Mrs. Tahoma, Mr. Madaki, da Abdullahi Umar daga Ofishin UBEC na Yankin Kano.
Ziyarar ta kasance wata muhimmiyar dama ga hukumomin biyu wajen ƙara ƙarfafa alaƙar ƙwararru, musayar sabbin dabaru da ra’ayoyi, tare da sake tabbatar da aniyar haɗin gwiwarsu wajen inganta ilimin bai-daya ta hanyar ingantacciyar sadarwa da dabarun yaɗa bayanai na zamani.