Unique hausa Novel

Unique hausa Novel Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Unique hausa Novel, Arts and entertainment, Kano, hotoro, Kano.

25/06/2026

*H I Y A A M*

Page 16: Last FP

Bright pens
Yota/001

Note: Akwai sanarwar a end of the page.

As I said, littafin HIYAAM daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne zuwa ga Nazeefah Sabo Nashe. Luv u all d tme😘

Wannan shafin naki gabaɗaya Maman Fati, alkairin Allah Ya kai miki har gadon baccinki😊

"Abbaaa!" Ana ta sake ƙwalla ƙiran sunan Babban Yaya a karo na biyu daga cikin ɗaki. Dukkansu kasa motsi s**a yi, b***e a samu wanda zai iya shiga ɗakin da Ana take wajan duba abin da yake faruwa da ita a ciki ɗin.

Babban Yaya har yanzu kan shi yana ƙirjin Innti hawaye na fita daga cikin idanunsa yana sauƙa a hankali, rawar da jikinsa yake yi ta tsananta, ya kuma kasa amsa tarin tambayoyin da Jaheed da Jadid suke masa.

Jaheed ne jiki na rawa ya ce "Ta ya Innti za ta rasu ta bar mu a lokacin da muke tsananin buƙatarta a kusa damu?" Ta girgiza kai ya ce. "Innti bata rasu ba, wasa ma take yi"

"Jaheed kuma mutuwa ta rasa wa za ta ɗauka sai Sahibarmu? Anya ta mutu kuwa?"

Cewar Jadid, jikinsa duka rawa yake yi.

"No, mu za mu riga Innti rasuwa fa"

Wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi Jadid ya sauke, abin da Jaheed ya faɗa ya saka ya ji wani irin relief na musamman yana sauka a zuciyarsa da jikinsa, tashin hankalin da ya nemi rikito masa ya ji ya ɗan yaye kaɗan. "Allahamdulillah!" Ya ce cikin sanyin murya. S**a zubawa Babban Yaya idanunsu na jiran furucin cewa Innti tana numfashi, Innti tana raye a duniya, kuma za ta cigaba da numfashinta cikin ƙoshin lafiya da farinciki, za ta cigaba da rayuwa, rayuwar da zai ba ta taɓa ganin cigaban da s**a samu a tasu rayuwar, rayuwar da zai ba ta damar ganin sauyin da s**a samu, za ta ɗauki Yaƴa da jikokinsu in sha Allah. Babban Yaya ya jima a yadda yake, da ƙyar yake iya jan numfashi da sauke wa, wani irin azababben ciwon kai na musamman tare da zazzafan zazzaɓi s**a saukar masa a lokaci guda. Tunda ya taɓa zuciyarta ya ji ba ta aiki, ya taɓa hannunta shima baya bugawa ya san Allah Ya ßauƙi rayuwar Innti a ranar juma'a, a kuma Sujjadar ƙarshe, ga azkar da Kur'anin da ta karanta nan a gefe guda kusa da kanta

Ya shiga tambayar kan shi, ya aka yi Innti ta rasu? Mene ya zama silar mutuwarta? Jini ta hanci da bakinta, ko guba Daada ya sa mata.

Ban da idanun su Jaheed, da yadda za su firgita babu abin da zai hana shi tashin gawar Innti ta faɗa masa silar mutuwarta.

Sannu a hankali ya zame jikinsa daga nata, ya kwantar da ita a saman laddumar ya ja Hijab ya rufe ta. "Babban Yaya Innti?" Yaya ya juya ya kalle su da nutsuwa da fahimtar daya arowa zuciyarsa da jikinsa, ba don bai firgita ko ya zauce ba, sai don a yanzu shine wanda suke kallo a matsayin Innti ɗin, dole ya zama jarumi. Ya riƙo hannayensu cikin ƙasa da murya wacce take fita da ƙyar ya ce "Na san ku Musulmai ne, kuma dukkan cikakken musulmi an san shi da imani da Allah, tare da Mala'iku da mazanni, tare da imani da ƙaddara me kyau ko kasin hakan. Duk wanda bai yadda da ƙaddara ba, kai tsaye yana faɗa da Ubangiji ne, kuma imaninsa yana da rauni" ya yi jim kafin ya ɗan rufe idanunsa, fishaa kuma ya buɗe su.

"Jaheed, Jadid mun rasa Innti k**ar yadda muka rasa Iftihal, kar ku yi kuka, domin yinsa yana saka mamaci cikin azaba, kar ku yi baƙin ciki, domin wanda ya halicci Innti shine ya ɗauki ranta, rayuwarta a wajansa ta fi wacce take yi a wannan gidan. Za ku iya cewa Allah don me ya yi muku haka? Idan ba Ubangiji ba, wane zai ɗauki ran uwa kuma ya ɗauki na ƴa a taƙin lokaci? Kuna da ikon question ɗinsa akan hakan? Ya k**ata mu yi farinciki, Iftihal ta yi shahada, ta rasu a cikin ruwa, Innti ta rasu yayin da take ganawa da ubangijinta, ranar juma'a kuma"

Ya ɗan fesar da iska "Akwai raɗaɗi tabbas, akwai ɗaci, ciwo ne kuma a zuciya ta tafi ta bar mu dashi. Mu yi mata addu'a, kar ku yi kuka, idan ya zama dole ku zubar da hawaye" kallon Babban Yaya kawai suke yi, sun ji me ya ce kuma sun gamsu, amma tambayar da suke da ita, yaushe za ta sake dawowa rayuwarsu a karo na biyu a matsayin uwa mahaifiya? Suna son sake fitowa daga cikinta, su sake rayuwa da ita.

"Bango ya faɗi Yaya" cewar Jadid.

Ya ɗora da "Ni ya k**ata na mutu ba ita..,"

"Shhha, ita Ubangiji ya yi niyya, domin ya gwada imanin da muke dashi, babu lokaci ina son a yi mata sallah a kaita gidanta yau"

Gabaɗaya zuciyoyinsu sun yi nauyin gaske, wani abu mai girma ya danne musu kirji, Jaheed da Jadid s**a nemi hawaye s**a rasa a idanunsu, rawa da kakkarwa da wata tsuma kawai jikinsu ke yi, basa ganin ko gabansu, su ka ji k**ar basu taɓa walwala ko farinciki a duniya ba, komai ya ƙare.

Wata sabuwar rayuwa suke hangowa, tare da wata sabuwar ƙaddara me girman gaske.

"Jeka faɗawa Maman....

Jadid ya gane me Babban Yaya yake nufi, k**ar an zare masa lakar jikinsa ya nufi gidansu Haysaam. Yaya ya miƙe ya nufi ɗakinsu. Yana shiga ya ja ƙofa ya rufe, wanwar ya faɗi a ƙasa ya dinga haɗawa jikinsa da bango, baya son yin ihu saboda kar su gane ya karaya ko kuma su yake hanawa kuka. Ya saka haƙori wajan datse harshensa, idanunsa s**a zazzago, ya ji wa kan shi rauni a harshe. "Innti me ya sa? Za ki tafi ki bar Ana? Ke da kanki k**e faɗin yadda take damuwa da ku ko kanta bata damu dashi ba, ke da kanki k**e faɗar taurin kai da rigimarta, Innti ba zan iya da rigimar Ana ba, ba zan iya ɗaukan wannan nauyin ba, Abbaa ba zai iya kulawa da Ana ba, ba tare da kina a kusa damu ba, Innti ba zan iya faɗawa Ana cewa bakya duniya ba, wallahi ba zan iya ba, ta ya zan rufe mata wannan maganar? Ta ya zan iya wannan?"

"Abbaaa....

Ya ji muryar Ana ta kira shi da wannan sanyin nata, da wannan silent voice ɗin nata

Ya juya kaɗan, sai ya ga har yanzu ba ta farka ba, amma sai kiran sunansa take yi. A hankali ya ja jikinsa ya matsa kusa da ita, sai ya ji tana surutai. "Abbaa kaga Iftihal ko, Abbaa wai ba za ta yi wasa dani ba da Innti za ta yi, Abbaa ka ga sun tafi sun barni suna mini dariya, Abbaa kalli kaya iri ɗaya zan saka. Nima ka siya mini irin kayansu ka ji"

"No" ya ce cikin sauri yana girgiza kai.

"Ba za ki saka irin wannan kayan ba, ba yanzu ba, ba nan kusa ba in sha Allah Shetty" ya riƙota jikinsa gabaɗaya ya rungumeta sosai k**ar zai mayar da ita ciki ya sake haifar ta haka yake ji, wata sabuwar soyayyar Ana ce me zafin gaske ta shiga huda zuciyar Yaya, wani irin hope, da wish tare da dreams me girma ne s**a shiga yawo a cikin zuciyarsa. Dole ya ɗauke Ana ya kaita inda ake buƙatarta, inda za ta yi farinciki da jin daɗi, amma ba za ta iya farinciki ba idan babu Iftihal da Innti a cikin rayuwarta. Dole ya shafe mata tunaninsu gabaɗaya a cikin kanta da zuciyarta, ta yadda za ta mance ta yi rayuwa dasu. Saboda nutsuwar zuciyarta zai yi hakan.

A hankali ya sumbaci goshinta, ya sake sumbatar gefen kuncinta, a nutse ya zura yatsun hannunsa guda biyar cikin nata ya haɗe su gam. "Rayuwarki ta zama tawa, Abbaa ya zama naki ke ɗaya, zan sadaukar da komai nawa saboda ki yi farinciki, sbd ke" ya yi shiru yana kallon fuskarta me kyau

Ya ɗora fuskarsa a saman tata ya ce

"Ina fatan ba zan zama mai laifi a gareki ba a sanda kika tuna matsayin Innti da Iftihal a rayuwarki, ina fatan ba za ki guji Abbaa ɗinki ba. Rayuwata taki ce Shetty, ina rayuwa dominki ne a gidan nan shettyyy"

Ya ƙanƙameta for a while.

A hankali ya kwantar da ita, ya miƙe ya nufi wajan wata jakarsa ya ɗakko turare ya dawo gabanta, ya haɗe hannayensa biyu sai ga wuta ta k**a ya saka turaren, ya fara shaƙa mata, cikin fitar hayyaci ta fara tari sosai ƙirjinta na ɗagawa sama, jikinta ya ɗauki rawa ta shiga girgiza, da ƙarfi ta yi ihu sai kuma ta kira sunan Allah, maganarta ta ƙarshe shine ambaton sunan Iftihal da Innti.

Jikinta ya ɗauki zufa ta wanke mata fuska ya miƙe ya fice. Yana fitowa Maman Haysaam da shi kan shi Yaa Sam da wasu matan maƙota suna shigowa cikin gidan, Maman Haysaam ta fashe da kuka tana salati.

Da aka sanar da Daada ƙin zuwa ya yi, sai Emama da Liya da Hanna ne s**a shigo, suna fashewa da kuka. "Baiwar Allah, mace mai haƙuri da kawaici Allah Sarki Innti" a cikin wannan lokacin Jaheed da Jadid da Yaya s**a sauƙewa Innti Kur'ani tare da Yaa Sam daya zama k**ar jininsu. Babban yaya da kan shi ya yi wa Innti wanka, ƙamshi sai tashi yake a jikinta, ya sha kuka saboda duk inda ya juya jikin Innti, shatin dukan Daada ne. Ya zubawa ƙasan cibiyarta idanu, saboda zanen wani tambari daya gani, ya rasa kuma wanne tambari ne wannan? Ya wanke ta tas, ya shirya ta, da aka zo tafiya da ita sai ya samu kan shi da riƙe gawar ya kasa saki, da ƙyar Yaa Sam ya zame hannun Babban yaya. Jaheed tun bayan maganar Babban yaya ko tari ya kasa, idanunsa ya bushe gabaɗaya bai san me yake ji a ransa ba. Bayan an yi mata sallah, sanda aka binne Innti Jadid ya yanke jiki ya faɗi a jikin Babban yaya babu numfashi haka Jaheed.

***
Asuba a tasha ta yi wa Ahlam, ta shiga motar da za'a kaita zuwa Banue state. Ta yi kuka har ta gaji idanunta sun kumbura sosai, amma taja ji this is the only way, da zata iya samun damar cika burinta, zata samu damar amsa sunan cikakkiyar ƴar jarida kuma ƴar gwagwarmaya. Ta san Engineer dole zai yi baƙinciki, amma tana hango farincikin da zai yi idan ya ganta ciki matsayin da za ta taka. "Liman?" Ta ƙira sunansa a hankali tana dafe ƙirjinta, ta so Md, ta ƙaunaci Md, kuma tana fatan rayuwa dashi ta har abada, za ta dawo tabbas.

Ta lumshe idanunta, tana sauraran waƙar “Im coming home" tare da binta a hankali.

6:00 motar ta ɗaga tare da barin tashar, Ahlam ta ji k**ar rayuwarta ta bari a kano kacokan, dukkan wani farinciki da jin daɗi sannu a hankali ta ji suna yin ƙaura a jikinta.

Yana daga bakin ƙofar hannunsa riƙe da casbaha ya ce "Wai Jiddah tashin baby ne haka?" Daga cikin ɗakin Anty Jiddah ta ce

"Abban Mufeed, Ahlam bata ɗakin fa"

"What?" Ya ce yana shigowa da sauri.

Aunty Jiddah ta ce "Wallahi, shigo ka tayani ganin ikon Allah, har banɗaki bata ciki fa"

Engineer ya shiga duddubawa, ya fita waje ya shiga kiran sunan Ahlam amma shiru, duk inda suke expecting ganinta bata nan. Da aka mira me gadi yana duba gate ya ganshi a buɗe, gaban Engineer ya faɗi, hankalinsa ya tashi sosai. "Abban Mufeed ko dai kidnapers ne s**a shigo s**a ɗauke Ahlam, da za ta kwanta bacci sai da ta yi mini sai da safe fa. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Engineer ya ce "Kidnapers?"

Ya girgiza kai "Kuma su ɗauki iya baby kawai? Duk mutanen gidan sai ita kawai?"

"Abin ne da ɗaure kai, amma ka ƙira Asad ka ji, ko suna tare da ita da" ya kalle ta ya ce

"Jiddah, kin san me k**e nufi, by this time ki ce wai Ahlam na tare da wani? Gabaɗaya yaushe aka idar da sallar Asuba ne?" Ta ce

"Naga mijinta ne, ba abin mamaki bane" Ance ba'a ƙin ta mutum sai ya juya zuwa cikin gidan kai tsaye ɗakinsa ya shiga ya nemi inda ya ajjiye wayarsa, number Md kuma Liman ya nemo, a ringing ɗin farko ya ɗauka k**ar me zaman jiran ƙiran ya ce "Wify, ina kika ajjiye wayarki kika ɗauki tasa?" Jin hakan ya saka Engineer dafe kan shi da ƙyar ya ce "Asad, Engineer ke magana" Liman ya yi ƙasa da murya ya ce "Afuwan Yaya, good morning ya hanya?"

"Allahamdulillah. Nace Ahlam fa?"

"Ahlam" Liman ya maimaita a kan harshe, ya kuma kasa bawa Engineer amsar tambayar da ya yi masa domin bai fahimta ya san by now shi da ita ai suna tare a hanyar Abuja.

Engineer ya ce "Asad, why? Ai ka bari a yi bikinmu me ya sa zaka ɗauki yarinya ka tafi da ita? Har ta kwana a wajanka, this is wrong" again, Liman shiru ya yi saboda wani shock da tsoro kuma da ya ratsa masa cikin zuciyarsa. A hankali ya ce "Wajena?"

Ya ɗora da "ta ce za ku je Abuja, har ta nemi izinin tafiya a wajena, Yaya ya zan ɗauke ta ta kwana a wajena, bayan a gida nake rayuwa ban taɓa yi nini a hotel ba. I thought ma ita ta kira da lambarka" Engineer ya ce

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

"Lafiya menene ya faru?"

"Asad, bamu da yan'uwa a Abuja, ba mu da kowa a Abuja, asalinmu ƴan Maiduguri ne, a sanadin boko haram muka rasa ƴan'uwanmu, Ahlam ba ta da kowa da za ta ziyarta idan ma akwai suna rayuwa ba mu san ina suke ba, Ahlam ita ta rage mini, nima ita kawai nake da ita, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ko wani abu ya faru ne wanda ban san dashi ba? An shigo har gida an sace mini baby, su waye wannan? Me ta yi musu? Ina baby take yanzu wanne hali za ta shiga ne don Allah?" Liman ya yi shiru.

A hankali ya ce "Bari na zo gidan Yaya"

Ya kashe wayar.

Engineer da ƙyar ya ja jikinsa zuwa cikin gidan ya zauna saman kujera kan shi a ƙasa, wasu hawaye masu zafi s**a shiga bin fuskarsa, duk yadda yake tunanin abin da fasalta shi a zuciyarsa ya kasa fahimtar cewa she run away from the house, zuciyarsa ta cunkushe ta shiga buga masa. Anty Jiddah ce take sakkowa daga saman bene wajan faɗin "Engineer ga abin da Ahlam ta bari akan gadonta, tabbas gudawa ta yi, amma yarinyar nan ba ta kyauta mana ba, idan auren ne ba ta so me ya sa ba za ta faɗa ba, sai ta ɗauki hanya ta gudu ta bar gida? Haka aka ba ta tarbiyya ko haka shine mafita a gare ta, ina za ta? Ina take fisabilillahi?" Ya amsa takadda har biyu, ɗaya an saka sunan Yaya a jiki ɗaya kuma Liman, wanda yake nuna tabbacin bashi da ikon dubawa b***e ya karanta. A hankali ya buɗe tasar ta fara karantawa inda ta fara rubutun da; "Yaya zan tafi ba tare da yadda da izininka ba, saboda na san ba za ka amince mini ba, kai ba kawai Yaya bane a wajena, kai ne uwa kuma uban da nake gani ƴan'uwana gabaɗaya. Ina son ka sosai ina gudun ɓacin ranka, na kuma amince da auren da ka yi mini saboda ina son Asad sosai Yaya, zan kuma dawo gare ku a kai ni gidansa na aure na yi rayuwa k**ar yadda kowacce take yi a gidan mijinta. Ina da buri sosai akan aikina, ina son aikin jarida Yaya ina jin ƙaunar aikin a jinin jikina, ina son na kawo sauyi a harkar jarida musamman a ɓangaren mata Yaya. An yi taron karrama ƴan jarida ban fuskanci komai ba sai baƙinciki da baƙinciki, na yi kukan da zuciyata ta kusa samun matsala, ban taɓa takaicin nakasar da nake da ita ba sai yau. Na tafi Yaya, zan dawo a lokacin dana amsa sunan ƴar jarida cikakkiyar, zan dawo idan na samu ɗaukakar da nake fata, zan dawo da abin mamaki kuma bazatar da duniya za ta yi mamaki da ita. Kar ki yi mummunan tunani a kaina, zan tsare kaina da mutuncina ba zan taɓa yin abin da zai taɓa ƙimata da taka ba. Ka yi haƙuri Yaya ka yafe mini kuma ka yi mini addu'a, ka bawa mijina haƙuri ka rarrashe. Ahlam Abdallah Kurmi"

Tun kafin ya gama karantawa idanunsa yake zubar da hawaye, ya ji k**ar ya samu matsala da zuciyarsa da kuma jikinsa, ya yi shiru yana sauraran bugun da zuciyarsa take. Aunty Jiddah ta saki salati tana fashewa da kuka. "Ahlam me ya sa za ki mana haka, duk irin abin da za ki fuskanta ba gwara kin zauna kusa damu ba?"

Muryarsa mai sanyi ta sauka a cikin parlourn yana yin sallama, shine na farko sai Mu'allim da yake bayansa, hannunsa manne da kanuna yana sanye shadda mai ruwan duhu data amshi jikinsa sosai ya rame ya sake haske. Liman kuma tattausar Jallabiya ce a jikinsa wacce ta yi kwance a fatar jikinsa, tunda ya je masallaci Baffa ya ja su jam'i ya dawo gida ya ji wannan tashin hankalin kasa motsi ya yi, da ƙyar ya iya faɗawa Al'ameen, duk da Al'ameen ɗin babu lafiya shine ya yi ƙoƙarin yin driving nasu zuwa.

"Barka da asuba" cewar Mu'allim yana miƙawa Engineer hannu su ka yi musabaha ya gaida Anty Jiddah. Liman kasa magana ya yi

"Gashi, saƙon da ta bar maka"

Liman ya amsa ya buɗe, shima a nutse ya fara dubawa da; "To my one and only Zauj, Mr Asad Hafiz Hafiz Hafiz. Na rubuta maka wannan a lokacin da bani da wani zaɓi bayan abin da nake jin zan aikata shi ne daidai. Na rubuta maka wannan a sanda zuciyata ta cika da so da ƙaunarka, yes, ka fahimci ina son, kusan kai ne confidence ɗina a Bright Fm, ina tsintar kaina cikin tsananin kishi idan na ganka tare da Yussy... Na maka ƙarya na ce zan ji Abuja haƙiƙanin gaskiya ba mu da kowa a can, na yi haka ne kar na tafi da haƙƙinka na fita ba tare da izininka ba. Abin da Yussy ta mini zai iya saka mini ciwon zuciya, na kasa haƙura na kuma kasa mancewa. Na ji sanarwa BBC a jiya da Hausa France International RFI suna neman wani sabon tarihi da za su wallafa a ranar Hausa ta duniya, na tafi zuwa ga neman abin da zai dace da su, ina da tabbaci za su buƙata kuma duniya za ta san dani a wannan rana, ta HAUSA INTERNATIONAL DAY. Wallahi Liman i so much love you, I love you with all my heart and soul, I love you to the Extra Liman. Zan kare maka kaina da mutuncina, za ka same ni yadda kowanne miji yake samun matarsa, ba zan taɓa kallon wani namiji a bayanka ba, ina fatan kafin na dawo zaka soyayyata a cikin zuciyar danginka, ina fatan daga nan har na dawo na tsaya a gabanka mijina ba za ka taɓa kallon wata mace da irin kallon da kakewa Halimatul Sadiya ba. A ranar dana dawo a wannan rana ba zan kwana gidan kowa ba, sai gidan mijina Mr Asad Hafiz Hafiz fa, a gadonsa zan kwana rungume a jikinsa. I love You Md, Liman, Asad. I'll be back sooner or later bye. Ur wife Ahlam"

Ya naɗe takaddar ba tare da ya ce komai ba, wannan shirun kuma har gwara ya ce wani abu ko babu yawa. Engineer ya ce "ka yi...,"

"No need Yaya, i can wait for her"

Ya yi shiru yana jan numfashi da sauƙewa yana jin zuciyarsa ta yi masa nauyi sosai.

"Bani da wata mata a duniya sama da Halimatu, zan jira ta, zan jira ta jira na iya adadin da za ta ɗauka kafin ta dawo Yaya"

"Amma Asad....,

"No please, na fahimci uzurinta, akwai wauta da ƙuruciya a tattare da ita. Ka yi addu'a za ta dawo da nasarar da take fata, ina addu'ar Ubangiji Ya sa ta je a sa'a. Ni na san ba za ta iya jurewa ba tare da ta yi notifying ɗina ba, zan jira ranar daga sanda ta neman a sannan zan yi tracking numberta zan bita zuwa inda take" ya yi ƙasa da kan shi a hankali ya miƙe tare da k**a hannun Al'ameen da yake jingine da jikin Liman ɗin yana riƙe da hannunsa ya ce

"And please, kar ka yi cigiyarta, saboda tana da ɗaukakar da zuwa gaba zai iya taɓa ɗaukakar data samu. Thank you Yaya"

Engineer yana jin tausayin kanshi, amma ganin Liman ya ji k**ar shi ne abin tausayi, yana son Ahlam sosai yana ƙaunarta Allah ya bashi haƙuri da juriya kawai. Anty Jiddah ta kawowa Engineer shayi ya ce "Ga tea ɗin"

"Bana jin yunwa Hawwa'u"

Ta yi shiru na wani lokaci.

Wayarta ce ta fara ringing, ganin sunan matar abokin mijinta ya saka ta ɗauka ta ce "Firdausi ina kwana ya kwanan yaran?"

Ta cikin wayar Firdausi ta ce "Alhamdlh Jiddah, daman akan maganar ƴar aikin da kika ce kina so ce, ga wata an samu, ba su jima da zuwa Kano ba, wai ƴar gudun hijira ce daga Barno shine na ce bari na kira ki" Jiddah ta yi jim ta juya ta kalli Engineer ta ce "Firdausi zan kira ki zuwa anjima, amma batun aikin nan k**ar na fasa ɗauka fa, idan na yanke shawara za ki ji ni in sha Allah" kashe wayar ta yi, ta shiga lallashin Engineer daya lumshe idanunsa yana ta kokawa da numfashinsa ya kasa jure rashin Ahlam a kusa dashi. Wayarsa ya ɗauka ya kunna data ya shiga page ɗinta ko zai ga ta yi update na wani abu, madadin hakan sai ya ga vedion Ahlam ne tana kuka sosai kanta a ƙasa, wacce ta yi posting ta saka caption na. "Ƴar jarida Ahlam Abdallah Kurmi, a wajan taron ƙarshen shekara na karrama ƴan jaridu. Tana yin kuka saboda bata samu award na Outstanding Journalist ba"

Vedion ya je viral, ya samu a ƙalla viewes wajan 5M. Ga sharing da comments k**ar hauka, ya miƙe da ƙyar yana shirin fita daga gidan ya yanke jiki ya faɗi a tsakiyar parlourn.

***
TIVLAND 1976

Haan ya kasa yadda da maganar da Kaka yake yi na cewa sun rasa Anum da Jarumi. Ya yi cikin gidan da sauri, har lokacin iska me ɗauke da guguwa na tashi yana ɗaukan mutane sosai. Sanda ya shiga sai ya ga cikin inda su ka yi gininsu a gaɓar kogin ya tsira ya shiga yana duba inda Dooshima ya ɓoye Anum da Jarumi. Cikin sa'a ya ga ramin ƙasan ya buɗe, daga Anum har jarumi babu me numfashi a ƙirji haka ya ɗaƙƙo su yana kiran sunan Kaka da ƙarfin gaske, kwantar da su aka yi a gefe aka shiga yi musu magani. Anum ta riga farfaɗowa a gigice ta shiga girgiza Jarumi tana kiran sunansa, wata soyayya ce me ƙarfin gaske a tsakaninta da Jarumi, soyayyar da ko iyayensu basa yi wa hakan. Kaka ya sauke numfashi ya ce "Uwa"

"UWA MAMA kina ina? Ki kawo mana ɗauki ki, maganarki muke jira, furucinki muke jira"

Haan ya ce "Kaka anya ba za mu fita neman uwa mama ba? Yaushe za mu jira zuwanta? Yaushe za ta zo garemu? Tana ina? Tana kusa da mu ko tana nesa da mu? Tana duniya ko ba a haife ta ba? Ya k**aninta suke Kaka?" Kaka ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce "Haan, ba a faɗa mana suffarta ba, haruffan sunanta kwai aka bamu, sunan Uwa Mama za a iya samun a haruffan A, ko H, ko F, Mama tana ɗauke da Tsav ne, Tsav wani tsohon tunani ne na gargajiya a al’ummar Tiv wanda yake da alaƙa da:bikon asiri, sihiri, ƙarfin ruhaniya,ko wata baiwa da ake ganin mutum yana da ita ta ɓoye.
A fahimtar gargajiyar Tiv: ana ganin wasu mutane suna da “Tsav” a jikinsu wanda zai iya ba su ikon yin abubuwa na al’ajabi ko cutarwa, waɗannan mutane su kan su basu son suna da wannan baiwar ba, wannan baiwar ita mu Tubabe muke so da buƙata"

Haan ya ce "Yanzu kaka yaya za mu yi?"

"Dole mu jira bayyanar Uwa mu roƙi Aondo ya kawo mana ita, bana son Akombo ya sake yin fushi damu Haan, wannan shine"

Dare ya yi, cikin dare s**a farka da wani sabon tashin hankali, gabaɗaya gonakin da suke noma a ciki wuta ta k**a a cikinsu, komai ya ƙone tas, ga gawarwakin mutane da s**a gani zube. Sati ya shuɗe haka watanni babu Dooshima babu labarinsa, hankalin Anum ya tashi sosai, kaka ne ya shafe mata tunanin Dooshima tas kanta da zuciyarta, ta mance ta dinga kallon Haan mahaifin Jarumi a matsayin nata uban.

Sojoji s**a dawo, a wannan lokacin babu tashin hankali. S**a kalli kaka s**a ce

"Ya muke ciki daki ne?"

Kaka ya ce "Mun amince da sauyin da za ku kawo mana, ina roƙan Aondo ya baku damar dawo mana da Dooshima da aminci"

Sojan ya ce "Dooshima? Bai dawo ba?"

"Kun sake shi ne?"

Sojan ya kalli Haan ya ce "Me zai saka mu riƙe shi? Baya wajanmu, tun a lokacin ai mu ka saka a kawo shi kan iyaka damu"

Uji da Terhemba s**a kalli juna.

A 1976 aka sake ƙafa tsarin Mulki na TOR TIV aka naɗa Kaka matsayin shugaban Tubabe. Wannan mulkin ya baƙanta ran Imande family sosai, aka yi shagali akai Swange dance Kwagh-hir (wasan kwaikwayo da al’adar Tiv) Tsarin Tor Tiv, ba sai ka mutu ba, akwai adadin da ake ɗauka a yi juyin mulki zuwa wani family, don haka Imande s**a matso ƙwarai mulkin ya ƙare daga hannun Ikur family. Kaka ya mutu, nan take aka ɗauki muƙami aka bawa Terhemba.

Haan yana ɗaya daga cikin dattawan masu zartarwa duk da haka ya zama ɗan kallo, ya bada shawara akan yadda Terhemba ya fara sawa na kawo masa mata yana lalata budurcinsu akan neman Uwa Mama da yake. Jarumi yana da shekaru goma a duniya, ya fara kulawa da Tor Tiv da dukkan zuciyarsa, duk rikicin da za a kawo musu yana ɗaya daga cikin jaruman da suke kare tubabe. Ya zama zakaran gwajin dafi wajan faɗa da wasa da kibbau, yana da sha'awar wasan ruwa, kodayaushe yana gefen ruwa ƙafafunsa a ciki, ga wata soyayyarsa da aka ɗorawa jama'a, duk inda aka ce ga Jarumi nan sai an cika. Murmushinsa ya fi maganarsa yawa sosai.

Watarana aka wayi gari rikicin manoma da makiyaya ya ɓarke, Jarumi ƙoƙarin kare al'ummar Tiv yake, koda wasa baya taɓa zubar da jini, ko Fulani ya gani yana basu hanya. Rikicin ya yi tsanani domin jar da Junkun a kawo musu hari. Bayan komai ya lafa jikinsa duk jini ya nemi Anum ƙasa da sama ya rasa babu ita babu alamar ta, ba ƙaramar ɓarna Fulani s**ai musu ba.

Jarumi ya yi kukan rashin Anum ya sake zama shiru shiru a wannan lokacin kuma dukkan Tiv s**a amshi addinin kiristanci, aka fara daina gargajiya mutane s**a fara zuwa cuci, aka gina makarantu da kasuwanni. Amma duk da haka wasu ba su daina gargajiya ba, k**ar yadda ba su watsar da tsafi ba. A wannan lokacin Terhemba da Uji da Haan su ka yi tafiya, sanda s**a tashi dawowa babu Haan sai gawarsa da ta ƙone sun yi tsari kuma shi kaɗai ne ya rasu. Maraici kota ina ya rufe jarumi.

Shekarar 1976 tana da muhimmanci sosai a tarihin yankin Tiv. Najeriya a 1976 A lokacin soja ne ke mulkin Najeriya. Shugaban ƙasa shi ne Olusegun Obasanjo (bayan mutuwar Murtala Muhammed a Fabrairu 1976).Babban Abin Da Ya Faru a 1976 1. Local Government Reform (Gyaran Ƙananan Hukumomi) A 1976 gwamnatin soja ta yi babban gyara: an ƙarfafa ƙananan hukumomi, an tsara shugabancin gargajiya,
an ba sarakuna rawar hukuma. A yankin Tiv:
an ƙara ƙarfafa matsayin: Tor Tiv da kuma:
Tiv Traditional Council.

Ba a kafa Benue State ita kaɗai ba tukuna.
A lokacin: Benue-Plateau State ce.

Sai a 1991 aka raba: Benue State da Plateau State Benue ta zama jiha mai zaman kanta

Inda Tiv s**ai rayuwa ya zama River Benue.

***
Sannu a hankali take juya kanta da yammacin, mafarkin da ta yi a yau na rashin Anum ya sake saka mata nauyin zuciya. Da ƙyar ta buɗe idanunta da s**a kumbura sosai, kwananta huɗu kenan a haka, hakan ya yi daidai da kwana uku da rasuwar Innti.

"Abbaaa" ta ce a hankali tana yi masa murmushi me kyau, domin a fuskarsa ganinta ya sauka, kanta a kan cinyarsa yana gyara mata sumar kan da a kullum baya rabuwa da gyara mata. Jadid ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Finally, gudan jinin Abbaa ta farka" sai ta masa murmushi.

Jaheed da yake ta firfita wuta idanuna cike da hayaƙi yana ƙoƙarin dafa taliya ya ce

"Sannu da turmushe wa Abbaa cinya"

Ana ta miƙe a hankali ta kalli Abbaa shima kallon ta yake, ta tsorawa cikin idanunsa ido sai ta shagwaɓe fuska ta ce "Abbaa wai haka?" Ya girgiza kai ya ce "Ko goyo k**e so zan miki shi har ki sake yin wani baccin"

Jadid ya kasa dauriya ya ce "Ba ki tambayi Iftihal da Innti ba" ta yi shiru alamar tunani zuciyarta ta buga da gaske kanta ya sara ta ɗan rirriƙe kanta ta ce "Su waye haka?"

Su ka yi shiru suna kallon ta, Jadid ya juya yana share hawaye. Sai ta juya idanunta ta ce "Nifa ban san so ba, Allah da gaske"

Daidai nan Yaa Sam ya yi sallama yana ganinta zaune kusa da Babban Yaya ya ja idanunsa ya lumshe yana jan numfashi da saukewa. Su Jaheed s**a gaishe shi, idanunsa akan Ana ya amsa. Ta gaishe shi ya ce "Ya jikin nakin?" Ta juya idanunta ta ce

"Abbaa wai ya jikina bani da lafiya ne?"

Bai amsata ba, bata da sukuni yanzu komai ta ce Abbaa. "Ya ƙarin haƙuri kuma?"

"Waye ne ya rasu kuma? Daada? Allah Ya sa shine ya mutu Allah Ya sa babu shi a raye"

Babu wanda ya san meke faruwa da Ana sai Abbaa gabaɗaya ya shafe mata tunanin Iftihal da Innti. Yaa Sam ya yi musu sallama ya fita Ana ta yi kwanciyarta akan cinyar Abbaa yana ƴan wakoƙinta deep down tana jin kewa me zafin gaske, tana jin k**ar bayan ita akwai wasu daban da suke tattare da ita. Jaheed ne ya yi musu girki s**a ci, da dare ya yi a ɗaki ɗaya s**a kwanta, Jaheed da Jadid shimfiɗa ɗaya, Ana tana shimfiɗar Babban Yaya ta shige jikinsa sai bacci take.

Idanunsa biyu, suna haka Daada ya shigo a yadda ya saba shigowa, duk s**a farka har Ana ta fito. "Ki shirya gobe zan kai ki wajan Alhaji Baita, a madadin ƴar'uwarki dana saka a c**a, ya ce dole sai na biya shi"

Ana ta sheƙi da dariya ta ce "Ko ba biya ba"

Ta san c**ar, fresh komai yake kanta matsayin Innti da Iftihal da kasancewar su a gidan duk ta mance bata ma san so ba.

Daada yayo kanta Abbaa ya shiga tsakiya, shi dai ya san yana ɗora hannunsa akan Daada tsaf za'a ɗauke shi babu rai, kuma hukuncin zai hau kan shi, duk abin da zai raba shi da Ana baya so. Kuma har yanzu yana riƙe da umarnin Innti akan Daada.

"Muddin kaga ban bawa Baita ita ba, ka ɗauka bana raye a duniya ne wallahi"

Sannu a hankali Ana ta fara tuna irin mak**ancin wannan maganar da ya yi a baya. Rawar da zuciyarta take yi, ya haddasa wa jikinta amsar ta yin da zuciyar ke yi masa. “kuɗi ya fi mini komai akan ta, farincikin da nake ciki idan na ga jaka guda, ya fi mini kallon ta, matsayin ɗiyar cikina, ba ita ba, hatta uwarta zan iya sadaukar da ita muddin za a cika lalitata da kuɗi wallahi”

Sannu a hankali, maganganun s**a shiga dawo mata tare da kai komo a cikin kanta. Suna yi wa ƙwaƙwalwarta tuni!

“Bani da ko sisi, ina kuma buƙatar sulalla na gaji da zama da dattin aljihu, na shiga c**a, na kuma yanke shawarar sanya Ayshatul-Iftihal a cikin c**ar, idan na ci za ta cigaba da rayuwa a gidan nan, akasin hakan na sadaukarwa da Alhaji Baita ita akan c**ar”

Sai ta ji daren na yi mata nisa, tuna cewa Alhaji Baita ya bawa shekaru Sittin baya. Kaddarar wasu mutanen na zuwa cif da cif k**ar sune s**a zanawa kansu taswirar rayuwar, tun daga farko har ƙarshe fari tas take, k**ar yadda rayuwar Nadiyaah ta kasance, komai na rayuwarta k**ar ita ce da kanta ta zaɓawa kanta yadda za ta wakana. Wasu kuma raba dai-dai suke yi, daga farko farinciki irin mai mantar da mutum wani abu kan iya faruwa dashi na ƙaddara, sai daga baya reshe ya juye zuwa mujiya, kwatankwacin rayuwar Ahlam Abdallah Kurmi. Wasu mutanen k**ar dare biyu haka rayuwarsu take ciki saboda ƙaddarar da ta yi musu ƙulli, babu farinciki ko kaɗan k**ar yadda ta kasance a rayuwar; ANA. Wasu mutanen kuma gabaɗaya ƙaddararsu a baibai ba su fahimci kansu ba, b***e su fahimci ƙaddararsu har su yi maganinta. A ɓangaren Batty hakan lissafin yake a rigar Biya gidan Dikko.

Ta ɗaga jajayen idanunta cikin ƙunci da raɗaɗin zuciya ta ce "Allah Ya nuna mana gobe, ko gawata ko ta Babana..," Sai ta yi shiru. "Ko ta Alhaji Baita"

Gabaɗaya s**a kalle ta banda Yaya.

Bayan sun koma bacci, wannan sanyin da yake ratsa jikin Yaya shine ya fara, ya yi iya ƙoƙarinsa wajan hana hakan faruwa amma ya kasa. Sannu a hankali sanyin ruwan kogin ke ratsa jikinsa alamar baya tare da Ana a yanzu ɗin.

Itama data farka bata ganshi ba, babu kowa sai ita, fresh tunaninta ya dawo ta ƙwala kiran sunan Innti da Iftihal a gigice, ta dinga kuka da ihu ta bigirma ta rarrashi kanta. Hijab ta ɗauka ba ta ganin ko gabanta ta shiga Napep ta ce Hisba Headguater.

Tana zuwa ta kalli wani mutum ta ce

"Shugaban ƴan Hisba nake son gani"

Ya kalle ta sosai, yarinya ce bata fi 17 years ba. Ya ce "Baya nan ki bada bayanin abin da k**e so za a sanar dashi ko?" Ana ta girgiza kai ta ce "Matsalata ai bata ƙananun ma'aikata bace, shugaban Hisba ɗin nake son gani da kan shi, akwai abin da zan faɗa masa wanda sirrina ne, kuma na yi masa wasu tambayoyi" ya dinga kallon ta da mamaki yace "Ikon Allah, ƴar ke ɗin nan ce k**e da matsala, ko auren dole za a yi miki?"

Wani irin jirkitaccen kallo Ana ta yi masa.

"Malam ba wasa na zo ba, keep a joke aside please. Ina shugaban Hisba ɗinku yake?"

Ya ce "Me k**e buƙata a wajansa?"

"Ƙarar mahaifina na kawo. Ina so ya kawowa rayuwata ɗauki, k**ar yadda ka ce haka ɗinne, auren dole za a yi mini kuma bana so, domin ni ba matar tsoho bace, ina so ya shiga tsakanina da mahaifina. Ni na yarda zan yi aure idan ana buƙatar hakan, amma idan shugaban Hisba ɗin naku ya amince zai aure ni. Auren rufin asiri kafin na samu wanda nake so" ta yi shiru tana sauke ajjiyar zuciya har ta juya ta dawo tace

"Oops, ka faɗawa shugaban Hisbar taku, na kawo ƙara idan bai ɗauki mataki ba, dukkan abin da ya samu da faru da rayuwata shine sila kuma shine sanadi, ga number wayata"

Ta bada number Yaa Jaheed.

Tana fita ya saki dariya kawai ya cilla number a bakinsa ya taune tas.

***
BIYA.

Yana kwance bakin ruwan yana rawar ɗari hannunsa dafe da ciki da kan shi, idanunsa rufe ruf dasu. Gabaɗaya hankalinsa yana kan Ana da tunanin halin da take ciki, ko yatsarsa ya kasa motsawa. Ya yi namijin ƙoƙarin ɗago hannunsa ya ware takaddar da Innti ta rubuta kafin ta rasu, kyakkyawan rubutunta ne ta ce "Yaya ban sani ba ko za ku dawo ku same ni, zuciyata ta yi mini nauyin dana kasa tantance abin da yake damuna, idan na tuna na yi saɓon Allah wajan yin biyayya ga Daada sai na ji k**ar zuciyata za ta fashe. Na sani babu biyayya ga mutum wajan saɓa wa Ubangiji, amma na biyewa Daada mun aikata son rai. A jiya na sake jin wa'azi,"Lā ṭā‘ata li makhlūqin fī ma‘aṣiyatil Khāliq." Ma'ana: "Babu biyayya ga wani halitta idan biyayyar za ta jawo saɓa wa Mahalicci." Yaya ya zan yi da hakƙin Iftihal, na yi lafila na roƙi zaɓin Ubangiji, ina da yaƙinin ya amsa kuma ya gafarta mini. A yau da safe na fahimci ina yi wa Daada biyayya ne saboda ban san wacece ni ba, bani da alaƙa dashi ta kusa ko ta nesa b***e ta jini, ina tunanin tsoron gaskiya ta bayyana ku tambayi wacece ni ko asalina, ban sani ba, kuma zai iya korata ya ƙwace mini ku"

Sai ta yi sakin layi ta ce "One day I may die without saying goodbye to you but I'll never forget to say thank you, because you hold most lovely part of my life. Ina rubutu wannan a lokacin da tunanina ya dawo na san wacece ni, ina tsoron na sake mancewa, zan tafi da raɗaɗin sabon Ubangiji da na yi, Yaya an ce; Ana biyayya ga mutane ne a cikin abin da ya dace da shari'ar Allah. Idan umarninsu ya saɓa wa umarnin Allah, to a ƙi bin umarnin cikin ladabi da hikima, domin biyayyar Allah ita ce tafi kowace biyayya. Muddin ina raye kuma na cigaba da mance kaina zan ta aikata saɓon Ubangiji wajan yi wa Daada biyayya, na riƙo zaɓin Ubangiji"

Ta sakin layi.

"Na bar maka Ana duniya da lahira, ta amsa sunanta da naka, Aysha Muraad Ana. Ka kula mini da ita don girman Allah Abbaa, asalina ba musulma bace, daga baya na musulunta. Sunana.... Sunana.... Sunana"

Ta rubuta sunana sau wajan biyar kafin tace

"Sunana ANUM"

"Laaa kaɗo, ka dawo kai ne?"

Muryarta Batty ta sauka a cikin kan shi, ya yi saurin rufe idanu yana damƙe hannunsa.

"Ina ta nemanka shine ka gudu ka barni, ko kana tsoran na cinye ka ne? Ni fa mayya ce"

Babban Yaya ya yi wa Batty shiru.

Ta washe bakinta ta ce "Kyakkywa ne kai, kalli gashin fuskarka me kyau, kuma kana wanka kullum kana ta ƙamshin abinka ko?"

Ta miƙa hannu ta shafin kwantaccen sajen gefen fuskarsa "Innalillahi, laushi" ta faɗa tana yin saurin ɗauke hannunta ta ce "Kai"

Ta zungure shi, ko motsi bai ba, "baka magana?" Ta zabga uban tagumi

"Allah sarki kurma ne, sunana Batty"

Ya yi mata burus sai ta sunkuya dai-dai fuskarsa ta zaro harshe ta ce "In cinyeka na lashe ka" harshenta ta taɓa tsinin hancinsa.

***

Suna zaune da yawa. Ɗaya daga ciki ya ce "Idan mu ka yi wasa Sayyadi Baffa zai ɓata mana sabuwar gwamnatin da muka kafa, ya zama dole mu ɗauki mataki akan shi, k**ar yadda muka ɗauka akan Hafizz Hafizz Baffa, a shekarun baya shi da ƴarsa Diyanaah Hafiz Hafiz Baffa, ba za mu zuba idanu ya rusa mu ba, kuma dole adadin musulmai a ƙasar nan ya yi ƙasa, kun san ba za su taɓa zaɓar Jonathan ba, suna da kishin musulunci" a hankali ya numfasa kafin ya ce

"Ba iya Baffa ba, hatta Major sai mun ɗauki matakin gaske a kan shi, za su iya zame mana matsalar gaske a tattare da tafiyar nan?" A hankali ya jinjina kai kafin ya ce

"Ya batun wannan maganar da aka yi?"

Madubi ya ce "Tana nan, an gama jadawalin su ɗari ne cif Yaranka ya daɗe" ya yi shiru.

"A faɗawa Baita ya rufe bakin jama'a daga abin da yake shirin faruwa a garin nan"

Madubi ya ce "An gama"

***
Al'amarin ya yi wa Ana zafi, ga rashin Abbaa, su Jaheed kuma idan sun fita nema sai dare suke dawowa gida. Ta ɗauki ciki takadda ta rubuta tarihin rayuwarta tas, komai da komai har batun Iftihal da Innti. Ta ɗora da "Wannan saƙon naka ne shugaban Hisba, na zo baka nan wannan takaddar ta zama shaida, rayuwata idan ta lalace akwai saka hannunka, kuma kai ne sila, ka zo ka aure ni kafin mahaifina ya rusa rayuwata, babu isasshen lokaci, duk wanda ka cewa gidan Daada a unguwar Kankarofi ya sani ga number wayar Yaya nan" ta ninke takaddar ta sake komawa Hisb Headquarter, cikin sa'a ta samu Ansar ya bata haƙurin Shugaban baya nan, amma zai bashi in sha Allah"

Cikin rashin sa'a da saurin da Ansar yake yi, sai ya saka takaddar cikin jerin wasiƙun da aka riga aka karanta su a ofishin Baffa.

Sanda ta dawo gida dare ya yi kuma kai tsaye ɗakin Yaa Sam ta shiga ta same shi yana ta tattare kayan da zai tafi interview da su, ta durƙushe a wajan ta fashe masa da kuka k**ar ranta zai fita ta ce "Yaa Sam ina Abbaa, ban ga Abbaa ɗina ba. Daada ya ce zai kai ni gidan Alhaji Baita ba zan jure ba"

"Nanaah, za ki iya aurena?"

Yaa Sam ya yi furucin lokacin da take durƙushe a cikin shagon nasa a tsakiyar daren. Kasa magana ta yi, ba ta da zaɓi face abin da ya zaɓa mata. "Nanaah...........

Ya kira sunanta da ƙyar ganin ta ƙi tashi ya saka hannunsa wajan ɗagota tsaye, ƙafafuwanta rawa suke sosai tana ƙoƙarin sake zubewa a wajan, sai ya taro ta ya jinginata da jikinsa ya tallafo haɓarta yana kallonta da nasa rinannun idanun wanda suke raba pain ɗin a tare ya ce. "Tun da ba ki da wani saurayi give me a chance, ki bani dama na zama mijinki Nanaah, ki bani dama" a hankali take kallon shi ta kasa cewa komai, ta rasa kalma ko ɗaya a bakinta.

Ya cure girarsa ya ɗage ɗaya ya ce "Na sani, na sani kalma ta soyayya ba ta taɓa kilmawa a tsakaninmu ba, amma ina jin soayyarki a zuciyata bani da ƙwarin gwiwar faɗa miki tunda na san mene burinki. Ki bani haɗin kai wajan tallafar rayuwarki na aure ki, ko zuwa gaba idan kin samu wanda k**e so sai na sawwaƙe ko?" Ta yi masa ƙuri da idanunsa.

"Amma kai abokina ne, Yayana kuma"

A nutse da kamewa ya ce "Kuma mijinki zuwa gobe da yamma, ki amince mini"

"Amma ni bana sonka da aure fa"

"Wannan ba zai zama matsala ba, idan ina sonki wadatar, kuma I will keep my promise na sakinki idan kin samu wanda k**e so ko?" Kamar ta yadda k**ar bata yadda ba.

"Da gaske kake?"

Ya jinjina kai tare da faɗin "Yeah. In sha Allah" "Na amince Yaa Sam"

"Dame?" Ya tambaya a hankali yana jin wani sanyi yana lulluɓe jininsa tare da saukar masa da kasala a jikinsa. "Da auren naka"

A tsayin shekarun da ya yi da ita bai taɓa sha'awar riƙe ko da hannunta bane, ko da ya riƙe bai riƙe da wata manufa ba, da gaske kallon jinjira yake mata k**ar yadda yake yawan ce mata "My ƙwailata" ko kuma "Jaririyar babarta" ya ji akasin hakan a yanzu, har bai san yaushe ya taka kusa da ita ba, b***e ya san yaushe ya jawo ta jikinsa ya rungume ba, sai jin goshinsa ya yi a saman nata numfashinsa na sauka a saman fuskarta ta watsa idanunsa cikin nasa itama. Da rawar murya ya ce "Ni talaka ne Nanaah, amma zan fifitaki za ki yi farinciki a tare da wannan talakan, a tare dani, mudin kin kasance tare dani. Ki mini alƙawarin za ki jira ni, ki mini alƙawarin za ki saurari dawowata?" Idanunta cike da hawaye ta ce

"Na yi maka Yaa Sam, zan jira ka"

Yana ta kallon idanunta ya ce "Adadin yaushe jiran naki zai ɗauka Nanaah?"

Jikinta ne ya saki saboda ta san shi kaɗai ne hope ɗinta tsanin da za ta cika burinta laɓɓanta na rawa ta ce "Adadin sanda zan koma ga Ubangiji Yaa Sam, ina nan ina jiranka ba zan ƙarya alƙawari ba, zan ta jiranka ka dawo da wurwuri ka ji ko?"

"In sha Allah" ya ɗora da;

"Rufe idanunki" ta yi k**ar ba za ta rufe ba, sai kuma ta ja idanun ta rufe. Iska ta ji ya wura mata a kunne tare da kiran sunanta tun na yarinyarta “Jerryna" sai kuma ta ji alamar saukar laɓɓansa akan nata, jikinta ne ya shiga rawa jin abin da ba ta taɓa tunani ba, ba ta ma kawo shi cikin kanta ba.

Kissing ɗinta yake slowly yana riƙe da ita, idanunta lumshe hawaye na tsiyaya.

Ya sake ta yana murmushi "Na samu aiki, Interview zani, da an gama zan dawo a goben in sha Allah kin ji my wife to be"

Kallon shi kawai take yi kafin ta juya ta koma gida. Jaheed na ta rarrashinta yana cewa Abbaa neman aiki ya tafi. Bayan gari ya hawaye Jaheed ya fita shago Jadid ya je wajan inda ya samu aiki. Tun safe take sunturi a gidan Maman Haysaam har yamma babu labari. Daga ƙarshe Walid ne a gigice ya shigo yana cewa an tare motar ɗaliban University da s**a tafi Interview Abuja a hanya, an ƙone motar tas da mutanen cikinta su wajan ɗari kuma duka zaratan maza. Ana ta yanke jiki ta faɗi.

Sanda ta farka a wani ɗaki a ganta daban kuma dare ya yi, ta shiga juyawa tana tunanin Ina ne nan ɗin? Muryar Daada ta ji yana cewa "Ai Baita na samu damar ɗauke yarinyar, tunda ka bani ƙalanin da zan yi arziƙi ai an gama burina na zama attajiri"

Ya yi shiru sai ya ce "Ba dai ka ce dana amshi budurcinta shikenan ba?"

"Gwara ka kashe ni ko ka yi mini aure da ka aikata mini abin da kake niyya" a kiɗime ta faɗi hakan tana saka hannu wajan kakkare ƙirjinta. "Ko ka siyar dani matsayin baiwa, na san zaka samu abin da kake so Daada"

Ƙafafuwanta ne s**a gaza ɗaukan gaggar jikinta, ta kalli kwalbar dake hannunsa wacce ta tabbatar ta giya ce, ta sake kallon wani jan zare da kan zakaran dake ajjiye an buɗe bakinsa, da ƙyar ta fusgi numfashi wanda ya kasa sauka a maƙoshinta hatta iskar dake cikin ɗan ƙaramin ɗakin a gurɓace take shaƙarta, ganin yana tunkaro ta idanunsa sun yi jawur saboda azabar buguwar da ya yi da yadda abin da yake ji yana addabar sa tsayin kwanaki da s**a gabata da zuciyarsa ta fara kwaɗaita masa ƴar cikin nasa, wannan rana ta zame masa ranar da zai jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya, ko ma ya ce tsuntsaye uku masu lafiya. Ya ɗan laso gefen bakinsa yana kallon ta da miskilayen idanunsa masu tasiri.

"Zan cika buri na ne a kanki tun da wancan damar ta shige ni Ana, ni ubanki ne ba zan taɓa cutar dake ba, ko na raɓe ki babu damuwa ai, kuɗi zan samu, kuma kema zan saka ki ne a turɓar arziƙi, rayuwar da muka yi baya zata zama tarihi, za ki zama sarauniya, me isa da kuma iko. Zan ƙirƙirar miki wata sabuwar duniya wacce babu kowa a cikinta daga ni sai ke, sai daula da farinciki irin wanda arziƙi ke samar wa kowa" ya ɗaga kwalbar ya tuttula abin da ya yi saura a ciki "ƙyasss" ya saki wata ƙyasa me warin data saka ta saurin ɗauke kanta zuwa gefe, ya kusantoto yana me ƙarewa surar jikinta kallo ban da ƙirjin da ta saka hannu ta kare.

Ya miƙo hannunsa zai riƙota ta yi saurin zillewa zuwa gefe. "Na tsaneka Daada....,"

Ta kasa ƙarasa sauran maganar da ta yi niyya saboda wani abu daya tukare mata a tsakanin wuyanta da maƙoshinta ta kasa yin koda ƙwaƙƙwarar numfashi wajan da kuma saukewa. A hankali ta ɗago kanta wanda s**a rine da ja asalin blue eyeballs ɗinta ya rine baka ganin komai a cikinsu wanda ya shige tsana me munin gaske, damuwa wacce bata da magani, kaɗaici wanda babu wani mutum da ya isa ya cike mata gurbin kaɗaicin da take ji yana mamaye ilahirin ƙofofin zuciyarta yana sauƙa a gangar jikinta. Ta watsa masa rinannun idanun ta ce. "Wai me kake nema dani ne Daada, me ya sa ka ɗakko ni daga gida ka kawo ni nan?" Ya ɗora hannunsa ɗaya a ƙugunsa yana sake bin sassan jikinta da kallo.

Murya ba ta fita ya ce "Kin kwanta mini na kuma kwaɗaito dake, ki bani haɗin kai"

"Haɗin kai?" Ta maimaita a raunace raunin daya shiga rarraba zuciyarta in to peaces ba tare data sani ba. "Haɗin kai na mene?"

Ta sake nanata tambayar a karo na biyu.

"Na sanki a matsayin ɗiya mace.....,"

"Ka ɓata mini rayuwa kenan?"

Ta yi saurin tare numfashin da tambayar da ita kanta ta kusa jikkita mata tunani. "Ubana ya yi mini fyaɗe ko kuma me?" Ta ƙara ruɓanya masa tambayar, bai gama tattaro abin da zai ce ba, duk da bashi da abin cewa ya sani ɗin face cimma burinsa wanda yake tsaye a kan shi kai da fata, ya ji ta jefe shi da wata tambayar. "To idan na samu ciki fa?"

Ta yi wani irin murmushi ta sakin numfashi, numfashin daya saukar mata har zuwa fuska. "Cikin ubana? Ubana ya yi mini ciki?"

"Eh, Yes." Ya bata amsa sai kuma ya ce

"Kin ga is normal thing a wannan zamanin, ni zan nema miki mijin aure idan hakan k**e gudu, ɗan kuma mata nawa ke haihuwa suna yar da babyn a ƙwata ko bola ko dai a cilla shi a masai ko kuma a murɗe masa kai"

"Anya kai ne ubana ne na jini? Kai ka haifan"

"ANA!" Ya kira sunanta da ƙarfin gaske. Ita kanta sai a lokacin ta san cewa ita ta yi wannan furucin ta dai ji saukar maganar ne k**ar zubar ruwan sama, k**ar yadda zuciyarta ke gudu daidai da gudun ruwan, daidai kuma da bugawar lokacin daya sauya komai ya lalata komai daga cikin komai ɗin har da abin da ubanta yake buƙata a gare ta. Duk da bashi da ƙarfi haka ya tattaro abin da ya yi masa saura a jikinsa ya raromota zuwa gare shi, ta yi saurin durƙushewa a wajan tana faɗin. "Ka ji tsoron Daada, ka da ka lalata mini rayuwa, Yaa Sam nake jira zai aure ni, ya ce zai aure ni zai tafi dani. Ka ji tsoron Allah Daada...,"

Rikitowar da ya yi jikinta ya saka numfashinta ɗaukewa cak, idanunta ya rufe ruf babu abin da take gani sai duhu da ƙucin dake lulluɓe da zuciyarta.

Wani ihu ta kurma saboda wani irin raɗaɗi da azabar da ta ji a zuciyarta kafin ya cimma burinsa, wanda ya tilasta mata dawowa daga tunanin hirar da s**a yi da Yaa Sam a daran jiya, a haukace ta saka ƙarfi wajan ture Daada daga jikinta, ta yi nasarar hakan ta miƙe a lokacin da idanunta ya sauka akan wasu wuƙaƙe biyu da suke gefe, shima Daada ya ga wuƙaƙen k**ar ya san abin da take shirin yi ya miƙa hannunsa, a kusan tare kowanne daga cikin su ya ɗauki wuƙa ɗaya, ta ja ta tsaya ita ko ganinsa da kyau ba ta iya yi ta fita daga cikin hayyacinta. "Gwara na kashe ki da ki hanani abin da na yi niyya" ya yi kanta da wuƙa yana zuwa ta ɗaga wuƙar ta luma masa a ciki daidai lokacin da itama ya caka mata wuƙar a ciki s**a yi rakas, lokaci guda s**a faɗi gefe jini yana malala a ɗakin, shi ko motsin kirki bai yi ba, saɓanin ita data motsa kaɗan ta shiga ƙiran sunan Allah da salati fuskarta ɗauke da murmushi da kuma hawayen da suke fitowa daga cikin idanunta a hankali kuma ta shiga lumshe idanun lokaci guda komai nata ya tsaya cak.

LAST FREE PAGE.
ƘARSHEN SHAFIN KYAUTA NA LITTAFIN HIYAAM.

Idan kana son cigaban labarin, kana son shiga paid group. Za ka biya 1k kacal ta wannan account ɗin.

0116886423 Union bank Na'ima Sulaiman S

Ko kuma 8164069385 Opay Na'ima shu'aibu Sulaiman.

Duk account daba na Na'ima ba, to ba na littafin HIYAAM bane ba ruwana. Ka tura shaidar biya ta wannan number.
08164069385.

NOTE. Littafin HIYAAM book 1 2 3 ne. Free ɗin nan ba wai book 1 bane, an cire pages ɗinne a cikin book 1. Littafin HIYAAM 1500 ne, daga yau zuwa 1 ga watan July muna tsarin discount akan 1k kacal. Muna shiga 2 ga wata ya koma 1500.

Bani da ducoment ongoing ne, me buƙatar ducoment ya jira a kammala. Kuma 2k ne in sha Allah.

Idan an yi payment da yawa a WhatsApp za mu yi paid book ɗin, idan ba'ayi ba, a Telegram za yi.

Akwai tsarin posting a AREWAPEN. Ku yi searching sunan Littafin ku yi following account ɗina domin samun notification idan an yi update.

Ina fatan za ku bani haɗin gwiwa ku biyo ni a wannan littafin babu danasi a siyan shi in sha Allah. Duk abin da kake zato akan shi ba haka bane. Follow me.

Bright pens na godiya har kullum.
KEEP READING HIYAAM 2026 BOOK.

Sai mun haɗu daku a paid group.

Address

Kano, Hotoro
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Unique hausa Novel posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share