Engr. Abdullahi Ado

Engr. Abdullahi Ado I was born in Tagwaye, living in Tagwaye

07/05/2026

MU KIYAYI ZALUNCI

Abubuwa goma (10) da azzalumi (mai zalunci) zai gamu da su a duniya da kuma lahira:

A DUNIYA
1. Rashin kwanciyar hankali (tashin hankali a zuciya)
Zuciyar azzalumi ba ta samun nutsuwa saboda tsoron sakamakon zalunci.
2. Ƙiyayya daga mutane
Jama’a suna tsanarsa, ba sa ƙaunarsa ko girmama shi.
3. Faduwar martaba
Duk da iko ko dukiya, mutunci yana raguwa a idon mutane.
4. Rashin albarka a rayuwa
Dukiyarsa da rayuwarsa ba su da albarka, ko da suna da yawa.
5. Hukunci ko azaba a duniya
Sau da yawa Allah yana jarrabtar azzalumi da bala’o’i ko tozarci kafin lahira.

A LAHIRA
6. Tsananin hisabi
Za a tsaurara masa lissafi saboda zaluncinsa.
7. Mayar da hakkokin wadanda aka zalunta
Za a karɓe masa lada a ba wa waɗanda ya zalunta, ko a ɗora masa zunubansu.
8. Fushin Allah
Allah yana fushi da azzalumi, kuma wannan shi ne mafi muni.
9. Azabar kabari
A kabari zai gamu da wahala saboda ayyukansa.
10. Shiga wuta (Jahannama)
Idan bai tuba ba, makomarsa ita ce azaba mai tsanani a wuta.

Manzon Allah( saw )yace : “ku kiyayi zalunci domin duhu ne ranar alƙiyama”

Zalunci ba ya dorewa, kuma duk wanda ya aikata shi zai ga sakamakonsa ko a duniya ko a lahira. Adalci shi ne ginshikin rayuwa mai albarka.

Ya Allah ka tsare mu zalunci Kada mu zalunta ko a zalunce mu.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ✍️

07/05/2026

NDLEA uncovers underground drug caves, hideouts in Kano

The National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA), Kano State Strategic Command, says it has uncovered a network of caves and underground tunnels used as drug hideouts in the Rimin Kebe area of the state.

Read full story in comments section

06/05/2026
29/04/2026
Rayuwa bata da tabbas domin jiya ta wuce,yau muna ciki,gobe kuma tana tafe babu wanda yasan haqiqanin abinda zata zo das...
19/04/2026

Rayuwa bata da tabbas domin jiya ta wuce,yau muna ciki,gobe kuma tana tafe babu wanda yasan haqiqanin abinda zata zo dashi sai Allah s.w.a.

Assalamu alaikum warahmatullah. 'yan uwa barkanmu da wannan lokaci. Ina son mu yawaita cewa "Kullum kwanakin mu raguwa s...
08/04/2026

Assalamu alaikum warahmatullah. 'yan uwa barkanmu da wannan lokaci. Ina son mu yawaita cewa "Kullum kwanakin mu raguwa sukeyi ba qaruwa ba". Kuma za'ayi mana hisabi game da abinda muka aika. Lokaci baya jiran kowa

Address

Masallaci Street Unguwar Malam Gambo Tagwaye
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Engr. Abdullahi Ado posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category