Ummee Gallery

Ummee Gallery Your look our priority

Buy your affordable data bundle here
05/11/2022

Buy your affordable data bundle here

GRIN DM for the price
10/08/2021

GRIN
DM for the price

Your look, our priority
22/05/2021

Your look, our priority

22/05/2021

_____ MASARAUTAR MUCE _____
_______________________________

------ Littafi --- Na daya ------

-----🔛 -----

**★** PART (23) **★**

Post

By :---- Man Bash ----
.
.

KUMA SHINE TAKUN ƘARSHE
=========================

Lokacin da sultana ta tashi, bataga sultan ba miƙewa tayi ta zauna duk da jikin yanzu ya rage mata zafin sak**akon ruwan zafin da ta shiga, toilet ta ƙara shiga ta kara gasa kanta sannan ta fito ta ƙarasa gaban madubi ta zauna kallan kanta dake jiƙe da ruwa tayi, dryer da ɗauka ta Fara drying bashi, da sallama sultan ya shigo da abinci akan Tray kallan shi tai kafin ta ɗauke kai bata san su haɗa ido dashi murmushi yayi wai kunyar shi take yi, ƙarasawa gunta yayi ya karɓi dryer ɗin ya ajjiye sannan ya juyo da ita duk da haka yaƙi yadda su haɗa ido,
Nifa ban gane wannan sussunne kan ba ai yanzu babu wani kunya a tsakanina dake sultana munfa riga mun zama ɗaya, Kallan shi tayi ganin ita zai kallah yasa tayi saurin ɗauke kai ya riƙo haɓarta haba habibty dan Allah ki bari, miƙewa yai ya ɗauki dryer din ya fara mata yana mata hira ita dai daga uhmm sai uhm uhm ne nata amsar, bayan ya gama yaje ya ɗakko mata kayan da zata saka saida tayi kwalliyarta sannan ta ɗauki kayan ta shige toilet ya bita da murmushi, tana fitowa taga har ya haɗa mata tea ɗin ya zuba mata dankalin da komai da komai, zama tayi da kanshi yai feeding Nata,.
Bayan ya gama yace mata zaije suyi magana da waziri yace yana San za suyi magana da shi, kallan shi tayi wai yaya ba zakaje office bane? Aa fa nina ɗauki hutu zan huta ta matata ne ya faɗa yana murmushi itama murmushin tayi bari inzo muje daga nan zan wuce gun momy, tare s**a fita har ɓangaren momy ya raka ya gaida mom ɗin sannan ya wuce,.

Kallnta mom tayi ƴata kinfa gujeni kwana biyun nan, a'a wlh mom kawai dai kinsan jikin ne bamu daɗe da samun lafiya ba, daga kai mom tayi gaskiya ne, suna hira Hindu ta shigo da sallama, kallan ta mom tayi da murnushi zo ƴata kema ki zauna, zama tai tana murmushi, kallan mom Hindu tai mom plz ki faɗawa Abbah ya ƙira Hashim ya sakeni kawai ya barni anan ga cikin dake jikina mom ko ƙira fa bayayi, kallan tausayi mom tayi mata a'a abun baikai ga har sakiba zaizo za muyi magana kar ki kara zancen saki kinji, daga kai tayi tana goge hawayen face Nata sosai taba sultana tausayi har tasa ta ita mh ta zubar mata da hawayen.

Sultan ne da Hafiz a zaune kusa da abbah sai waziri dake lissafa abun da za'ai gobe na ɗaura shi a kan mulki, yanwancin komai Hafiz ne ya shirya, Bayan sun gama waziri ya tafi, Abbah ya kalli Hafiz, wai yaushe dana zai kai kayan aure ne yamun suruka, murmushi Hafiz yayi sai mun daidai ta da ita yarinyar da sauri sultan ya karɓa wani satin habib zaikai kayan bikinshi gidan su zulai mai zai hana tunda kawar matar habib ɗin ne muma mukai tare in yaso sai asa ranar tare, daga kai Abbah yayi hakan ma za'a yi zansa akawo kayan bikin da haka s**a yanke shawara, Bayan nan sarki ya kalli Hafiz ban number ɗin Hashim ɗin nan yazo ya sakar mun ƴata bana san rashin mutuci taya zai wani ajjiye mun ƴa haka wannan haukane, bashi number ɗin Hafiz yai ya karɓa,.
Suna gun yai dailing number ɗin bugu uku aka ɗaga,.
Da sallama sarki ya fara Hashim ya amsa, Ni uncle ɗin Hindu ne ina san kaban mahaifinka za muyi magana, sosai gaban Hashim ya faɗi Allah ya gani yana San Hindu Amman kawai haushinta yake ji saboda Abun da mahaifita yayi, to yace sannan ya miƙe ya nufi masarautar tasu da sallama ya shiga sannan yaba daddy ɗin nashi gashi zakuyi magana, karɓa yayi ya kara a kunne bayan sun gaisa Abbah yamai bayanin kanshi kuma ya gane shi, dama Hashim ne ya ajjiye Hindu a gida shi bai saketa ba sannan bai zo ya ɗauketa ba, abun tun baya damunta har ya fara damunta sannan gata da ciki kuma kasan ba'a san mace mai ciki da tunani shine nake tunanin ko zai faɗa mana abun da ya yanke ko sakinta zaiyi ko maidata saboda ta samu saukin zuciyarta, haƙuri Baban Hashim ya bashi dan tun ba yau ba yake fama da Hashim ɗin Amman wai sai yace yana bata punishment ita da ba ita tayi laifiba sannan ya shaida mai gobe zasu zo su tafi da ita da haka s**ai sallama, baban Hashim ya miƙa mai sannan yace ka shirya gobe zamuje ka taho da matarka, murmushi Hashim yai tare da faɗin Allah ya kaimu ,

Kallan Abbah s**ai Abbah me s**ace? Gobe zasu zo su tafi da ita sosai Hafiz yaji dadi Amman ba zasu faɗa mataba haka s**a miƙe s**a je ɓangaren mom ɗin akai ta hira dasu,. Haka yau ta kasance musu duk a cikin jin daɗi suke,.

Da daddare hindu Na zaune akan gado chatting take wayarta Ta Fara ringing, Hashim ne saida gabanta ya faɗi kin ɗagawa ta8i haka yai ta ƙira so yake ya sanar mata gobe zasu zo Amman taƙi ɗagawa, hakan yasa jikinshi yayi sanyi lalllai tayi fushi dashi sosai,.

Da sallama sultan ya shiga ɗakin sultana, zama yayi ya miƙa mata ledar hannunshi ga wannan gobe ita zakisa muyi anko nida Matata, kuma gimbiya ya, murmushi tayi ta karɓa ya buɗe wata haddadiyar gown ce tayi bala'in yin kyau, kallan shi tayi tace tayi kyau yaya ina san rigar,
Hmm to taya zan gane rigar ta miki ya faɗa yana kallan ta, murmushi tayi kafin ta matsa kusa dashi ta bashi kiss, a'a fa habibty wannan bashine zai nuna ta miki ba, murmushi tayi kafin ta fara bashi hot hot kisses, duk ta rudar dashi gaba ɗayansu sun ma fita a haiyacinsu hakan yasa na rufe musu ƙofa nai tafiya ta dan nima bacci nake ji, 😜

Washe gari masarautar sun taashi da aiki dan yau ne za ai naɗin sarauta, yau sultan da wuri ya fice saboda yana da ayyuka a kanshi haka ma uban gayya Hafiz zan iya cewa shine ya haɗa komai saboda haka komai a gunshi yake, ɓangaren mom aiki ake tuƙuru haka ma a can ɓangaren sultana hmm abun da sai ni dana gani,💃💃

3:30 dai dai aka gama haɗe masarautar tayi mugun haɗewa, a gajiye sultan ya shiga bangaren nasu sultana dake kitchen tana haɗa abubuwa ganin shigarshi yasa tabarwa masu aikin tayi ɗakin shi a kan gado ta ganshi kwance, sannu ta faɗa tare da zama kusa dashi aikin kenan wani abun ma sai mun baka sarautar, murmushi yayi tare da jawota Jikin shi ai zaki dinga tayani? Ni!!! aa ina nan ina zaune Amman zan dinga kiranka ina maka kalaman soyayya murmushi yayi tare da bata kiss ya Miƙe Bari inje in yi wanka 4:00 Za'a fara kema kije ki shirya yanzu, Okay ta faɗa tare da miƙewa ta fice,.
Hafiz dake tafiya so yake ya haɗu da Zuwaira ya Bata kayan da zata saka dan suma anko zasuyi, k**ar daga sama ya hangota tana sauri zata je gida yau, dasauri yasha gabanta har ta tsorata hararar shi tayi kafa ban tsoro, sorry ya faɗa yana haɗe hannun shi gu ɗaya, murmushi tayi zan wuce, holding arm yayi to ni Na hanaki ne,? Murmushin ta kuma yi sannan tace faɗi abun da zaka faɗa, kayan ya ɗakko ya miƙa mata, kallan shi tayi maye wannan kuma, haɗe rai yayi shikenan ba zanwa Matata kyautaba saita tambaye ni na miye, shikenan ya faɗa yana shirin tafiya da sauri tasha gabanshi to yi hakuri tasa hannu zata karba ya riƙe hannun nata

Da sauri ta kalleshi, marairaicewa yayi wai Zuwaira hannun ma ba zaki bari in riƙe ba, Hafiz babu kyau ne yau inda muna da aure ai bazan hanaka ba, sakinta yayi yana murmushi Allah ya bashi uztajiya, wannn zakisa muyi anko kinji, ɗaga kai tayi sannan ta kalle shi, zan tafi Ok ya faɗa har ta juya zata tafi ua kira ta Zuwaira inaaa sanki, murmushi tai, nima ina sanka da Gudu tabar gun ya bita da murmushi,.
Ɗakin Hindu yaje yaga tana cin Ɗan wake taɓe baki yai masu ciki da kwaɗayi ya faɗa, gashi wannan kayan zaki saka kinji ko? Kallan kayanta tai Ok naji kowa da nashi mijin yake anko ni kuma bani da kowa, murmushi Hafiz yayi dan kuwa Hashim ne ya sashi ya siyo musu kaya iri ɗaya da ita Amman yace kar ya faɗa mata,.

Sosai gun ya ciki da mutane, zuwan su sultan da sultana, da Hafiz ake jira kawai sai su habib,.

Dakin sultana sultan ya shiga ya gama shirin sarka take sakawa, karɓa yayi ya saka mata tare da ja mata alkabbar sannan s**a fito motocin sune da bayi masu take musu baya, Hafiz ya gani da Zuwaira sai Zulai da habib duk sunyi anko, nan take nafisah ya fado mata taji ina ma tana gun da haka s**a k**a hanya,.
Hashim dake ɗakin Hafiz yana shiryawa dan Sun daɗe da zuwa yace suyi gaba zasu biyo su daga baya, yana gamawa ya nufi ɗakin hindu ya shiga parlor ba kowa, hakan yasa yayi ɗakinta ya tura ƙofar tana kwance akan gado, kawai bata jin daɗin fitar ita ɗaya zata je shi yasa ya yanke shawarar sai An kusa gamawa zata je, hawayen fuskanshi ya goge kafin ya ƙarasa kan gadon dake tayi zurfi a cikin tunaninta bata san ya shiga ba saiji tai an rumgumeta da sauri ta ɗago tana kallan shi, k**ar a mafarki, da sauri take san zare jikinta Amman yaki sakinta sorry, Hindu kiyi hakuri zuciya ce, da ƙyar da komai ya shawo kanta ta haƙura sannan ya tayata ta shirya kallan kayanshi tayi Irin Nata nan yayi mata hayani, haka s**a nufi gun, kowa yaji daɗi da s**a shirya,.
Anan aka naɗa sultan akan sarauta kowa ya shaida, bayan an gamane sultan Na karbar kyauta ya riƙo hannun sultana yana mai cewa zo kiga wani Abu, binshi tayi s**a shiga taron, tun daga nesa ya hango wata k**ar Nafisa, saida s**aje daf da ita, da murna Sultana ta ƙarasa gunta s**a rungume juna kafin suna kallan yaushe gamo, nan nafisa take nunawa sultana mijinta wanda ya kasance aboki ga Hafiz, sosai sultana tayi murna da hakan, haka aka gama komai kowa ya k**a hanyar gida inda Hashim ya tafi da matar shi nafisa ma s**a koma ,.
Haka rayuwa ke tafiya komai yana tafiya with years, months, weeks, days, minutes, seconds har gashi Allah ya kawo mu wannan lokacin,

BAYAN WASU SHEKARU,

Sultana ce zauna a parlour tana duba jarida, da guda yaran s**a faɗa kanta, momy mun dawo daga wanjen grandma, ajjiye jaridar tayi tana kallansu to sannu ku da zuwa ya kuka baro grandma ɗin taku, tana lafiya, yaran da ba zasu wuce shekara bakwai bakwai ba suke faɗa mata yadda s**a tadda mom, da sallama sultan ya shigo da kaya a hannun shi, washhh ya faɗa tare da zama wannan yaran naki ne s**a barni da ɗiban kaya, murmushi tayi tare da faɗin sannu Bari in bawa jakadiya sai ta kai masu ɗaki, kayan su teddy ne da kayan wasan yara, ɗauka tayi ta sauƙa ƙasa taba jakadiyar kafin ta dawo suna gun sultan sun dameshi, ganin hakan yasa ta ƙarasa gunsu, ku tashi kuje kuga kayan wasan ku, da gudu s**a miƙe s**a fice, ta bisu da murmushi, riƙo hannunta sultan yayi zaunar da ita yayi yana mai cewa gaskiya in zaki sake ban yara mata zaki ban masu k**a da ke kiga fa Ashraf da Ashrim dani suke k**a, murmushi tayi to shikenan karka damu ta faɗa tare da jan haancinshi, ashhh ya faɗa hakan yasa tasa dariya ka fiya raki Yaya sultan, kawo in miki kiji inba zafi, da saauri ta miƙe tare da gudu shima yabi bayanta,.

Su habib sunsha biki dan har su Zulai Nada ciki hindu ma ta haihu lafiya abunta,. Gashi sultana ma ta haihu ƴan biyu s**aci sunan, baban sultan da Baban sultana,.

Tammat bi'hamdullah, wassalatu wassalamu alaa Rasulullah, ﷺ wasshukuru lillahi da'iman sarmadan ilaa yaumi yuba'asu ibaad Ameen ya rabbil Aālameen 🤲. 🤲. 🤲.

Abin da muka faɗa dai-dai Allah ka fimu sanin sa domin kaine ka bamu YARDA da AMINCI har muka kai ga bigiren faɗar sa, Allah kayi mana kyakkyawan SAKAMAKO NA ALKHAIRI,
Tarukan kura-kuran mu kuma Allah ka yafe mana su badan halin mu ba, ka kuma AMFANAR damu tarukan ALKHAIRAN dake cikin wannan littafin,
Allah ka yarje mana biyayyar mahaifa kar kasa mu kasance cikin marasa Albarka a Rayuwar mu Ameen 🤲

Littafin MASARAUTAR MUCEI yazo da Uslubai masu tarin yawa, yakai mai karatu anaka hasashen Mai kafi fahimta a cikinsa? Wane
abu na alfanu ka tsinta daga cikinsa? Sannan Meye ra'ayinka a kan makomar labarin?
Yi cikakken Bayani Akan littafin MASARAUTAR MUCE Musamman JIGON Littafin
ta haka ne zamu gane abin da ka fahimta a tsawo wata gudan nan da mukayi muna yin post ɗin sa, domin a halin yanzu aski ya riga da yazo gaban goshi.

LAIFIN DAƊI ƘAREWA to Masha'Allah gani Na koro Amman lokaci ya koreni sai dai mu haɗu A cikin LITTAFI Na gaba Bayan sallah

ALHAMDULILLAH............................. A NAN NAKAWO ƘARSHEN WANNAN 👉 LITTAFIN MAI SUNA 👑MASARAUTAR MUCE👑 HAR KULLUN MAGANATA GUDA ƊAYA CE WATO

FRIENDS A GASKIYA BANSAN IYA YAWAN GODIYAR 👍 DA ZAN NUNAMA D'UNBIN MASOYANA BA, 💓

NAGODE ƘWARAI DA SO 💕 DA ƘAUNAR 💘 DA KUKE NUNA MIN

ALLAH YABARMU TARE........*
THANKS ALOT ALL MY FANS.....LOVE YOU SO MUCH❤

Godiya ta musamman ga duk ƴan GROUP ɗin nan 🏯 Musamman mah masu yi mana Addu'ar fatan Alkhari,

To mun gode Sosai Allah ya saka da Alkairi, da zumunci,✋ da Son da kuke nuna mana.💔

Again Jinjina 👍 Gareku Masu yimin Addu'ar samun cigaba a cikin Rayuwata da kuma yimin fatan Alkhairi 🌾 A haƙiƙanin gaskiya kuna cikin RAINA BAZAN MANTA DA KU BA Na gode kwarai Allah ya ƙara ɗaukaka 👏

To My fans sai kunjini a sabon Novel 📚 nan gaba Bayan Sallah mai suna........."

Zamu fara yin post din sa In Sha'Allah Nan bada jimawa ba.⛅ ku dai kawai kuci gaba da kasance tare da Ni------------------------------
------------------------------
-------------------------wato :- Man Bash ---------------
------------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----



Domin samun LITATTAFAN HAUSA kuma Complete to ba wuya Abin da zakuyi kawai shine
Kushiga wannan shuɗin rubutun na ƙasa , sai kuyi like Na wannan page ɗin ba sai na Rantse muku ba dan duk littafin da muka fara sai mun gama shi har karshen sa matuƙar muna samin cmmnts sosai a littafin kar ku manta da sunan page ɗin

(wato)👇

👉Hausa Novels Only
👉Hausa Novels Only
👉Hausa Novels Only
👇👇👇👇
👉Hausa Novels Only
👉Hausa Novels Only
👉Hausa Novels Only

Address

Maiduguri Road.
Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ummee Gallery posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share