09/07/2026
*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*
*DAGA: KANKARA STUDENTS UNION (KASU) NATIONAL BODY*
*Karkashin Jagorancin: COMR. SALIM SHUAIBU GARBA*
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh,
Kungiyar Daliban Karamar Hukumar Kankara wato *KASU National Body*, tana sanar da cewa za ta Sanya yara marayu, da ‘ya’yan da iftila’in matsalar tsaro ya shafa, da kuma marasa karfi ‘yan asalin Karamar Hukumar Kankara baki daya zuwa makarantun primary, secondary, da islamiyya.
Wadannan yara a halin yanzu suna fuskantar matsala wajen samun ilimi saboda yanayi. Wasu ba su iya zuwa *Makarantar Boko* ba, wasu kuma *Islamiyya* ta tsaya musu.
Don tabbatar da cewa babu dan Kankara da zai fice daga makaranta saboda talauci ko rashin iyaye, ko matsalr tsaro.
Muna kira ga dukkan ‘ya’yan Kankara masu hannu da shuni, ‘Yan kasuwa, Manyan Mutane, da dukkan wanda Allah ya horewa da su *bada gudummawa* domin taimakon wadannan al’umma.
Taimakonku na iya zama: Kudi, Littafi, Uniform, jikka, (Na addini da na Boko) kayan tsaftace jikin mata (sanitary pads), ko duk wani abu da zai taimaka.
Tare za mu dawo da hasken karatu ga ‘ya’yanmu.
*Domin karin bayani da bada gudummawa, tuntubi lambobin da ke jikin wannan FLYER.*
Allah ya saka da alkhairi. Allah ya maido mana zaman lafiya.
*Signed:*
*Comr. SALIM SHUAIBU GARBA*
*Shugaban, KASU National Body*