04/04/2026
Muna ba wa Sheikh Jingir shawara ya yi ƙoƙari ya kawo gwamnatin Muslim-Muslim a Plateau a matakin Gwamna wataƙila zai iya musu amfani, amma a matakin ƙasa kam shi ma ya san ba wata amfani ta kusa ko ta nesa da yake yi musu a matsayin shugaba! Muslim-Muslim da Jingir yake kira cutarwa ce ta wajen rage darajar ƙuri'un ƴan Arewa a kan wanda ake so a zaɓa!
"Wani abu a kan matar sarki, da da ido da ta gani..."
Ga shi dai Tinubu ya zo har Plateau bai kira sunan Jingir ba, bai je gidansa ba, bai nuna akwai sa ba, bai masa jajen jama'arsa ta s**a mutù ba, bai masa jajen jikansa da ya rasu a satin ba– Bugu da ƙari, bai je Zamfara ba, bai je Katsina ba, bai je Maiduguri ba, bai je, bai je, bai je.....
Ba wai ba ma ƙaunar Jingir ba ne, amma ko matar Fir'auna da s**a ce za su riƙe Annabi Musa cewa ta yi "wataƙila zai amfanar da mu", haka lokacin da za a sayi Annabi Yusuf, aka ce "Wataƙila zai amfanar da mu". Haka dai in ka bi Ƙur'ani za ka yi ta gani. Amma shek Jingir kawai kai Muslim-Muslim ta kowani hali ba tare da amfani ba wannan ba daidai ba ne kuma ba za mu daina magana ba har sai shek Jingir ya fahimce mu kuma ya sauya ra'ayi da gaggawa! Ana kishin Musulunci ne a inda zai amfanar ba wai haka kawai ba. Shi muke so ku gane amma kun kasa ganewa!
Za mu ji meye zai ce yau a kan wannan lamari, duk walaƙanci dai an nuna masa jiya, ya rage wa shek Jingir ya fahimci abin da muke nuna masa tun ba yau ba, ya gane manufarmu, ba shi ne ba ma so ba, a'a, tunaninsa ne ba ma so...
Su kuma mabiyan malam mun bar su da halinsu, amma alhamdu LILLAH yanzu su ma sun fahimci cewa Muslim-Muslim in ba manufa to shirme ne, muna fata sauran ƴan kaɗan da ba su gane ba su ma su gane! Burinmu shi ne gyarawa ba wai ɓatawa ba!
Muna jiran me zai ce yau, in bai ce komai ba ma za mu ji, in ya ce ma za mu ji. Cewarsa da rashin cewarsa duk karatu ne, kuma za mu biyo da sharhi!
Allah ya mu wanye lafiya.