25/09/2026
đ¤˛đ ADDUâAR MU TA YAU
Ya Allah, a wannan rana mai albarka, mun zo gare Ka da zukatanmu cike da fata da tawakkali. Ya Allah, Ka gafarta mana dukkan zunubanmu, na bayyane da na Éoye, Ka yafe mana kurakuran da muka sani da waÉanda ba mu sani ba.
Ya Allah, idan akwai wanda yake cikin damuwa a cikinmu, Ka sauke masa natsuwa. Idan akwai wanda yake cikin baĆin ciki, Ka cika zuciyarsa da farin ciki. Idan akwai wanda yake fama da rashin lafiya, Ka ba shi cikakkiyar lafiya. Idan akwai wanda yake neman mafita, Ka buÉe masa Ćofar mafita daga inda bai zata ba.
Ya Allah, Ka albarkaci iyayenmu, iyalanmu da waÉanda muke Ćauna. Ka tsare su daga dukkan sharri, Ka ba su lafiya, tsawon rai cikin biyayya gare Ka, da kwanciyar hankali.
Ya Allah, kada Ka bar mu mu fita daga wannan Jumuâah sai Ka Éauke mana nauyin da ke kan zukatanmu. Ka sauĆaĆa mana abin da ya gagare mu, Ka kawo mana abin da muka dade muna jira, Ka amsa adduâoâin da muka yi cikin dare da waÉanda muka yi a Éoye.
Ya Allah, Ka sa mu kasance cikin bayinKa waÉanda idan s**a yi kuskure suke tuba, idan aka ba su niâima suke godiya, idan s**a shiga jarabawa suke haĆuri, kuma a kowane hali suke dogaro gare Ka.
𤲠Ya Allah, Ka sa Ćarshen rayuwarmu ya zama alheri, Ka haskaka kaburburanmu, Ka sauĆaĆa mana ranar da za mu haÉu da Kai, Ka shigar da mu Aljannatul Firdausi tare da waÉanda muke Ćauna.
Ya Allah, Ka karÉi adduâarmu, Ka biya mana buĆatunmu na alheri, Ka kuma ba mu abin da yake mafi alheri gare mu a duniya da Lahira.
Ya Allah, duk wanda yayi laking Kuma ya tura wannan adduâa zuwa ga âyan uwansa, Ka saka masa da mafificin alheri. Ka albarkaci rayuwarsa da iyalansa, Ka biya masa dukkan buĆatunsa na alheri, Ka yaye masa duk wata damuwa, Ka buÉe masa Ćofofin arziki da rahama, kuma Ka ba shi alheri a duniya da Lahira. đ¤˛â¤ď¸
Amin Ya Rabbal Alamin.
Sautus Sunnah