Jama,atu Ahbabu Rasulullahi SAW Funtua Branch Katsina State Chapter

  • Home
  • Nigeria
  • Funtua
  • Jama,atu Ahbabu Rasulullahi SAW Funtua Branch Katsina State Chapter

Jama,atu Ahbabu Rasulullahi SAW Funtua Branch Katsina State Chapter For Good Interaction With True Lover's Of Prophet Muhammad S.A.W. Hubbu Rasulullah is our mission
(1)

 MADINA TAYI KIRA✈️✈️✈️💓💓💓💯.ALHAMDULILLAH!!!Allah ya albarkaci Malamin mu SAYYADI MLM NURA ALIYU FUNTUA Da ziyarar Annab...
12/09/2025



MADINA TAYI KIRA✈️✈️✈️💓💓💓💯.

ALHAMDULILLAH!!!
Allah ya albarkaci Malamin mu SAYYADI MLM NURA ALIYU FUNTUA Da ziyarar Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam💗🤍💗 Wanda ALHAJI ABUBAKAR SADEEQ DAN GASKE ya biya musu su goma✈️ (10) ✈️a cikin wannan rana ta AYYAMUL-MUHAMMADIYYA DAY (2) Allah yasa Annabi yae farin ciki da zuwan su baki daya.

Muma Allah ya kira mu MADINA🕌🕋🕌 Bijahihi Nurul-Anwar Maulana Muhammadu Rasulullahi sallallahu alaihi wasallam badan halin mu ba Ya Allah 🤲🤲🤲.

  •Kalli Yadda Taron Masoya ANNABIﷺ S**a Halarci Taron Mauludin ANNABIﷺ Mai Taken Ayyamul Muhammadiyya Rana Ta Biyu, Wan...
11/09/2025




•Kalli Yadda Taron Masoya ANNABIﷺ S**a Halarci Taron Mauludin ANNABIﷺ Mai Taken Ayyamul Muhammadiyya Rana Ta Biyu, Wanda Ake Gabatarwa Akofar Gidan Sheikh Sharif Sani Janbulo Kuma Shine Yake Jagorantar Taron A Ranakun 17 Da 18 Dakuma 19 Gawantan Rabbi'ul Auwal, Ranar Asabar Kuma 20 Gawata Za'ayi Hawan Takutaha A Birnin Kano Insha Allahu.

©Jama'atu Media & Publication Nigeria.

 Fitowar Baba Sidi Ta Biyu A Rana Ta ƊayaAllah Yaqara Wa Annabi Daraja 💚✍️... Kamaladdeen Muhammad Fta
11/09/2025



Fitowar Baba Sidi Ta Biyu A Rana Ta Ɗaya

Allah Yaqara Wa Annabi Daraja 💚

✍️... Kamaladdeen Muhammad Fta

  •Kaitsaye Daga Filin Taron Ayyamul Muhammadiyya Ranar Farko Laraba 17/Rabbi'ul Auwal/1447H, Wuri Yayi Wuri Ana Jiran F...
10/09/2025




•Kaitsaye Daga Filin Taron Ayyamul Muhammadiyya Ranar Farko Laraba 17/Rabbi'ul Auwal/1447H, Wuri Yayi Wuri Ana Jiran Fitowar Baba Sharif Sani Janbulo(Hafizahullah)
.✍️ Kamaladdeen Muhammad

18 billion years:Day of Qiyama - Ina zaton mutane za su tsaya a filin Qiyama na tsawon shekaru biliyan goma sha takwas d...
10/05/2025

18 billion years:

Day of Qiyama - Ina zaton mutane za su tsaya a filin Qiyama na tsawon shekaru biliyan goma sha takwas da miliyan Dari biyu da Hamsin (18,250,000,000) kafin a fara yin Hisabi wa mutane abubuwan da s**a yi a lokacin da s**a rayu a duniya.
هَذَا يَوْمٌ عَسِرٌ
____________________________
Ranar tashin Qiyama rana ce me girma da kowa yake dakon zuwan ta. Za ayi doguwar tsayuwar da ba a taɓa yin irin ta ba, wannan tsayuwar tana daga cikin dalilan da yasa aka kira ranar da ranar Qiyama (Ranar Tsayuwa), mutane maza da mata, Yara da manya, Musulmi da waɗanda ba su ba, za su tsaya a filin Mahshar na sama da tsawon shekaru biliyan goma sha takwas, a lissafin shekaru irin na duniya.

~ Manzon Allah (S.A.W) ya tabbatar da za a tsaya na tsawon shekaru dubu Hamsin (50,000 years, irin shekarun da Allah yake lissafi dasu) irin shekarun lahira.

~ A cikin Al-Qur'ani Allah ya bamu Ma'aunin da yake lissafin shekaru dashi, a wajen sa shekaru dubu ɗaya na duniya sune kwana ɗaya a lissafin wajen Ubangiji. Sai anyi shekaru dubu 'daya anan duniya Allah yake rubuta shi a matsayin kwana ɗaya a wajen Sa, hakan yana nuna mutane za su tsaya a gaban Ubangiji sama da shekaru biliyan 18.

~ A cikin Suratul Hajji, Surah ta 22, a Ayah ta 47, Allah yace:
وإن يوما عند ربك كألف سنة مما تعدون

Meaning:

“Tabbas, haƙiƙa kwana ɗaya a wajen Ubangijinka kamar shekaru dubu ne irin waɗanda kuke lissafawa (a nan duniya).”

~ Idan ka buga lissafi za ka ga cewa muna da kwanaki 365 a kowace shekara (at most), hakan yana nuna shekaru dubu ɗaya a wajenmu shi ne kwana ɗaya a wajen Allah, sai ka buga:

~ 1,000 × 365 = 365,000 years.
Wato sai mun shekara dubu 365,000 a nan duniya kafin Allah ya lissafa shekara ɗaya a wajenSa.

~ To sai kace 365,000 thousands years times 50,000 wato yawan shekarun da Bayi za suyi a tsaye a gaba Ubangiji irin shekarun lahira, ko a takaice:

365,000 × 50,000 = 18,250,000,000 yeears, irin na duniya.

~ Wannan tsayuwa ce kawai da mutane za suyi a gaban Allah, ba zaman gidan Aljannah ba ce da aka ce waɗanda s**a shiga za su zauna har abada, shekarun tsayuwa da Hisabi ne kawai wannan.

~ Allah da kansa a cikin Surah ta 25 a Ayah ta 26 yace:

الملك يومئذ الحق للرحمن وكان يوما على الكافرين عسيرا

Meaning:

“Mulki a wannan ranar ya koma ga Allah Mai Rahama gaba ɗaya, wannan ranar za ta yi wahala wa kafirai.”

~ A cikin Suratul Qamar, Ayah ta 8 Allah yace:
مُهْطِعِينَ إِلَى الدَّاعِ يَقُولُ الْكَافِرُونَ هَذَا يَوْمٌ عَسِرٌ

Sai dai duk da waɗannan wahalhalun su Muminai ba za su ji azabar tsayuwar ba, Manzon Allah (S.A.W) yace:

~ “Na rantse da wanda raina yake a hannunsa (Allah kenan) za a sassauta wa Muminai wannan ranar, za su ga tsayuwar kamar ba ta wuce kamar mutum ya yi Sallar Farilla ya sallame ba.”

~ Wato Muminai ba za su ji wahalar tsayuwar shekaru Biliyan 18 ɗin nan ba, za su ga kamar sun tsaya ne na tazarar da ba ta wuce ka yi sallah ka yi sallama ba ko ƙasa da haka.

والذي نفسي بيده إنه ليخفف على المؤمن حتى يكون عليه أخف من صلاة مكتوبة

~ Wato mafi tsanani dai Muminai za su ga kamar minti 15 s**a yi a tsaye, yayin da kafirai za su ga sun shafe shekaru Biliyan 18 a wajen.

A cikin "Al-Mustadrak" na Imamul Hakim, Manzon Allah yace:

"Tsawon ranar Qiyama a wajen Muminai bai wuce kamar tazara ko (interval) ɗin dake tsakanin Sallar azahar da La'asar ba.”

~ Sheikh Muhammad Nasir yace wannan Hadisin Sahihi ne (8,193)....
يوم القيامة على المؤمنين كقدر ما بين الظهر والعصر

~ A wannan Hadisin, Allah zai sassauta wa Muminai za su ga kamar tsayuwar awanni biyu ko biyu da rabi kawai s**a yi.
Amma a zahiri 50,000 thousands years irin na lahira s**a yi, wato 18 Billion 250 million years.

~ Allah ya sanya mu cikin waɗanda za a sassauta musu wannan tsayuwar.
Tsayuwa ko na awanni 18 ne ba ƙaramin tashin hankali ne ba, b***e shekaru Biliyan 18 har ma da shekaru Miliyan 250.

Allah yace game da ranar tsayuwar, masu laifi da tauye mudu, da sabon Allah:
أَلَا يَظُنُّ أُولَئِكَ أَنَّهُمْ مَبْعُوثُونَ لِيَوْمٍ عَظِيمٍ يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ

~ Cosmologists sun ce sun fahimci yanzu haka duniya ta kai shekaru Biliyan 17 zuwa 18 da halittar ta.

Nan gaba idan anje lahira za ayi tsayuwar da ya wuce shekarun da duniya ta yi a halicce, wannan duk ba a zo maganar shekarun da za a yi a Aljannah ko wuta ba da aka ce har abada.

~ Dukkan Aiyukan da muke yi, Sallah, Azumi da sauran su sune aiyukan da idan an karɓe su acikin records ɗin mu za a sassauta mana wannan doguwar tsayuwar.

~ Manyan abubuwan tsoro a wannan tsayuwar guda hudu ne:
1. Babu zama sai tsayuwa a kan babbar yatsar ƙafa guda ɗaya.
2. Babu cin abinci babu shan ruwa.
3. Babu inda mutum zai taka ya je b***e ya motsa ƙafar.
4. Sannan babu wanda yasan ina zai je idan an zo an yi Hisabin, wuta ko Aljannah...

~ Duk duniya babu wanda zai iya roƙon Allah ayi haƙuri a sassauta wannan tsayuwar sai Manzon Allah (S.A.W), mutane za su je wajen Annabi Adam, zai ce ba zan iya ba, sai a dunguma aje wajen Annabi Nuhu, Ibrahim, Musa da Isah (A.S) duk ba za su iya ba, sai Muhammad Bin Abdullah (S.A.W)...

~ Ya Allah ka yafe mu, ka sassauta mana a nan duniya da kuma wancan rana ta Hisabi.

Allah kayi mana Alfarma mu samu kanmu cikin waɗanda za a sassauta musu wannan Azaba.
✍️:

Repost:
April — 10th, 2023.

Abdul-Hadee Isah Ibraheem

06/05/2025

Kai ko makahon da baya gani in yaji xance Annabi Muhammadu S.A.W yasan ba irin sauran halitta bane shi
S🌹A🌹W

Lokacin ƙuruciya, muna ganin wanda ya fi ƙarfi shi ne gaba da kowa, ana jin tsoronsa da ba shi girma. Bayan mun ƙara gir...
28/04/2025

Lokacin ƙuruciya, muna ganin wanda ya fi ƙarfi shi ne gaba da kowa, ana jin tsoronsa da ba shi girma. Bayan mun ƙara girma, sai muka fahimci mai karatu ya fi mai ƙarfi. Duk ƙarfinka in ba karatu, ƙarshe ka ƙare a ɗan aikin mai ilmi. Yanzu da muka fahimci rayuwa, sai muka fahimci mai kyawun halaye da iya mu'amala da tsarkin zuciya, yana sama da kowa har a wajen Allah. Duk ilminka in ba kyan hali, ba amfani

IMAM HASAN AL-BASRI (RA): TUSHEN TASAWWUF DA HASKEN RUHIYYAA tarihin Musulunci, akwai wasu mutane da Allah Ya zaba su ka...
28/04/2025

IMAM HASAN AL-BASRI (RA): TUSHEN TASAWWUF DA HASKEN RUHIYYA

A tarihin Musulunci, akwai wasu mutane da Allah Ya zaba su kasance fitilu a cikin duhu, masu haskaka zuciya, masu koya mana hanyar kaiwa ga Allah cikin hikima da ladabi. Daya daga cikin fitattun malamai masu tsarkakakkiyar zuciya shi ne Imam Hasan al-Basri (RA).

WANENE IMAM HASAN AL-BASRI?

An haife shi a shekara ta 21 bayan Hijira, kuma ya taso a cikin sahabbai. Ya koyi addini kai tsaye daga manyan sahabbai kamar Sayyidina Ali (RA), Anas bn Malik (RA), da sauran su. Iliminsa ya gauraya da hankali, hikima, da tsoron Allah. Daga cikinsa ne aka samu asalin ginshikin tasawwuf.

TAUFIQIN DA YA BAR WA DUNIYA:

Imam Hasan al-Basri ya kafa ginshiƙan tasawwuf ta hanyoyi kamar haka:
1. Tsoron Allah (Khawf) da KaunarSa (Mahabbah):
Ya kasance yana cewa:
“Mu ba mu daga cikin mutanen da idan aka ambaci Allah sai zuciyarsu ta motsa, mu ne mutanen da idan aka ambaci Allah sai numfashinsu ya tsaya.”
2. Guje wa Duniya (Zuhud):
Yana yawan cewa:
“Na ga wasu mutane, duniya a wurinsu kamar matacciya ce, ba su da sha’awar ta.”
3. Kira ga gyaran zuciya da tawali’u:
Yana cewa:
“Ka kalli zuciyarka a kowane lokaci. Idan ta zame maka shugaba mai aminci, to kai cikin tsira kake.”

MALAMAN DA S**A GADA TAFIYARSA:

Bayan wafatinsa, manyan malamai sun gina akidarsu ta tasawwuf bisa tafiyarsa, daga cikinsu:
• Rabi’atu’l Adawiyya (RA): Ta cigaba da fikrarsa akan “kaunar Allah domin Allah”, ba don Aljanna ko tsoron wuta ba.
• Junaid al-Baghdadi (RA): Ya yi fice wajen tsarkake ilimin sufanci cikin tauhidi da tsantseni.
• Imam Al-Ghazali (RA): Ya hada fiqh da tasawwuf, ya karfafa cewa:
“Ilimi ba zai amfane ka ba, har sai zuciyarka ta tsarkaka daga soyayyar duniya.”

BAITOCIN SUFAYA:

Wasu daga cikin baitocin da s**a bayyana ruhin wannan tafiya suna cewa:

“Ka dinga tunanin Allah har hankalinka ya daina tunanin duniya.”
— Imam Shafi’i

“Ka tsaya cikin nutsuwa a gaban Ubangijinka, kamar yadda bawan da ya san girman Ubangijinsa ke tsaya.”
— Rumi

HUJJA DAGA AL-QUR’ANI:

Allah Yana cewa:

“Ya ayyuhan naasu ittaqu rabbakum…”
— (Suratul Hajj: 1)
Wannan kira ne ga dukkanmu, amma malamai irin su Hasan al-Basri sun fi bayyana yadda tsoron Allah da soyayyarSa ke canza rayuwar mutum.

Tarihin Imam Hasan al-Basri darasi ne ga duk mai neman tsarkake zuciya. Malamai da s**a zo a bayansa sun gaji wannan fitila, s**a kai tasawwuf ga zurfafa ilimi da kyawawan dabi’u. Sufanci ba bidi’a ba ne tafiya ce cikin zurfin fahimta da soyayya ga Allah.

Ya Allah Ka sa zuciyarmu ta zama tamkar zuciyar bayinka masu tsoronKa. Ka bamu rabon zama cikin masu bin tafarkin Manzon Allah da irin koyarwar Imam Hasan al-Basri (RA) da masu nemanKa da gaske.

- Sheikh Basheer

  Allah ba dan halin mu ba,Ka kira mu Madina,muje muyi gaisuwa ga Shugaba Sallallahu alaihi wasallam 👏👏👏💯
11/04/2025



Allah ba dan halin mu ba,Ka kira mu Madina,muje muyi gaisuwa ga Shugaba Sallallahu alaihi wasallam 👏👏👏💯

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِيُرِيدُونَ أَن يُطْفِئُوا نُورَ اللَّهِ بِأَفْوَاهِهِمْ وَيَأ...
07/04/2025

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ

يُرِيدُونَ أَن يُطْفِئُوا نُورَ اللَّهِ بِأَفْوَاهِهِمْ وَيَأْبَى اللَّهُ إِلَّا أَن يُتِمَّ نُورَهُ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُون
AMADADIN
JAMA'ATU AHBABU RASULILLAHI (S.A.W)
Masarawa State Branch
Karkashin jagorancin
Alh. Idris Lafiya (Jagora)
Nafacikin gayyatar
Yan'uwa Musilmai
Zowa gagarimin taron
MAULID NABI (S.A.W)
Wanda
IMAMUL AHBABU RASULILLAH (S.A.W)
Sheikh Sharif Sani Janbulo (H)
Zai gabatar kamar haka👇

1. Litinin: 09/Shawwal/1446h =7/4/2025
Unguwar Magajin Malam Lafia
Lokaci: 8:00pm

2. Talata: 10/Shawwal/1446h =8/4/2025
(A) Garin Gandun Sarki, daura da Federal University Lafia
Lokaci: 4:00pm

(B) Garin Agyaragu, Lafia L.G.A.
Lokaci: 8:00pm

3. Laraba: 11/Shawwal/1446 =9/4/2025
North Bank na Garin Makurɗi, Benue State
Lokaci: 8:00pm

4. Al-hamis: 12/Shawwal/1446 =10/4/2025
(A) Garin Bakin Rijiya, Lafia
Lokaci: 4:00pm

(B) Garin Doma Kofar Gidan Sarki
Lokaci: 8:00pm

5. Juma'a: 13/Shawwal /1446 =11/4/2025.
(A) Garin Shabu Kokona L.G.
Lokaci: 10:00am
(B) Garin Nasarawa
Lokaci: 8:00pm

6. Asabar: 14/Shawwal/1446 =12/4/2025
Masallacin Idi na Garin Keffi
Lokaci: 8:00pm

7. Lahadi: 15/Shawwal/1446 =13/4/2025
Tudun Wada Keffi
Lokaci: 8:00pm

Insha Allah al-farmar Annabin Rahma (S.A.W)

Daga nan za'a shiga Garin Suleja, Niger State
Ranar Litinin 16/Shawwal 1446 =14/4/2025
Ai Kwana Daya
Sai Kaduna State
Ranar Talata 17/Shawwal/1446 =15/4/2025

Allah ya karawa Annabi (S.A.W) Daraja Wasila da Fadhila Fil Jannati

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ

Kar ka yi kuskuren mantawa da waɗannan ababe a wajen addu'oinka na goman ƙarshe:1. Mutuwa da Imani 200%: ka yi addu'a Al...
21/03/2025

Kar ka yi kuskuren mantawa da waɗannan ababe a wajen addu'oinka na goman ƙarshe:

1. Mutuwa da Imani 200%: ka yi addu'a Allah ya sa ka mutu kana mai imani da Allah ɗaya, shi kaɗai baya da abokin tarayya, ka nemi tsari daga shirka, mutuwa ba Imani shi ne mafi muni a rayuwar duniya.

2. Lafiya 150%: Ka roƙi Allah lafiya, domin wallahi idan ka samu jarabawar lafiya duk abin da ka mallaka rayuwar duniya zai Iya salwanta wurin nemanta. Lafiya dukiya ce babba.

3. Neman tsari daga sharrin mutum da aljan 150%: Mutumin da kake ɗaukar nauyinsa, a wannan lokaci za a iya haɗa baki da shi a nemi rayuwarka ko kassaraka. Mutum abin tsoro ne.

4. Mata tagari ko miji nagari 100%: Idan baka yi aure ba, ka roƙi mata tagari, ko ki roƙi miji nagari, wallahi kurkure a wurin zaɓar abokiyar zama ko abokin zama zai illata rayukar da kashi 80% kuma kuskure ne mai wahalar gyarawa.

5. Ayi fatar gamawa da Iyaye lafiya 100%: Idan aka samu akasi alaƙa ta lalace tsakaninka da Iyaye to nasarar rayuwa sai dai ka ji labari.

6. Ka nemi tsari daga Talauci 70%: Saboda girman munin talauci har kafirci zai iya jefaka.

7. Ka yi addu'ar Allah ya baka maƙwabci nagari 60%: Zama da mummunan maƙwabci jaraba ce mai girma gaske.

8. Ka roƙi ƴaƴa nagari 60%: Kana iya rayuwa mai kyau da aminci amma ƴaƴanka su hana maka ƙarshen rayuwa cikin aminci da salama, su jawo maka musibu iri iri da ɓacin rai. Ƴaƴa nagari zinari ne.

9. Ka yi addu'ar samun Ubangida mai tausayi da jinƙai 50%: Akwai uwayen gida azzalumai da kansu kaɗai s**a sani, ba taimako ba jinƙai. Aiki a ƙarƙashinsu jarabawa ce mai girman gaske.

10. Ka yi addu'ar samun aminci a cikin ƴan'uwanka 50%: Su kansu jarabace mai girman gaske. Idan baka yi sa'ar ƴan'uwa nagari ba. Har maƙiya suna iya zama kuma a cikin sauƙi zasu iya maka illa. Ko bayan rayuwarka, iyalinka a hannusu zasu koma. Ƴan'uwa nagari suna da muhimmancin a rayuwa.

Allah ya karɓa mana

Abubakar Umar

SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM 🙏🙏🙏💯.
08/03/2025

SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM 🙏🙏🙏💯.

Address

Kasuwar Mata Street
Funtua

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jama,atu Ahbabu Rasulullahi SAW Funtua Branch Katsina State Chapter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Establishment

Send a message to Jama,atu Ahbabu Rasulullahi SAW Funtua Branch Katsina State Chapter:

Share