13/03/2026
Hindi grammar
Menene Postposition?
A Turanci muna da Prepositions (kamar in, on, with, to) wadanda ke zuwa kafin suna. Amma a Hindi/Urdu, wadannan kalmomi suna zuwa ne bayan suna, shi ya sa ake kiran su Post-positions.
Ga manyan "postpositions" guda biyar da ya kamata ka sani:
Mein (เคฎเฅเค): A ciki (In)
Par (เคชเคฐ): A kan (On)
Ko (เคเฅ): Zuwa/Ga (To)
Se (เคธเฅ): Daga/Da (From/With)
Ka / Ke / Ki (เคเคพ/เคเฅ/เคเฅ): Na/Ta (Of)
2. Menene Oblique Case?
Wannan shi ne babban darasin. A duk lokacin da daya daga cikin wadannan "postpositions" din (mein, par, ko, da sauransu) ya biyo bayan suna (noun), shi wannan sunan dole ne ya canza fasali. Wannan canjin shi ake kira Oblique Case.
Ka'idar Canjin (Ga maza/Masculine nouns masu karewa da -a):
Idan kalma tana karewa da sauti "-a" (kamar Angna, Larka, Kamra), idan aka sanya mata postposition, wannan "-a" din yana komawa "-e".Misalai Masu Yawa a Cikin Jimla
Domin ka kara fahimta, ga yadda canjin yake bayyana a aikace:
Daki (Kamra):
Direct: Yeh kamra bada hai. (Wannan dakin babba ne.)
Oblique: Woh kamre mein hai. (Yana cikin dakin.) โ Ba a cewa "Kamra mein".
Yaro (Larka):
Direct: Larka khel raha hai. (Yaron yana wasa.)
Oblique: Larke ko bulao. (Kirayi yaron.) โ Ba a cewa "Larka ko".
Kaza/Kudi (Paisa):
Direct: Mere paas paisa hai. (Ina da kudi.)
Oblique: Ek paise se kya hoga? (Me zai yiwu da kwabo daya?) โ Ba a cewa "Paisa se".
4. Waษanne kalmomi ne BA SA canzawa?
Ba kowace kalma ce take canzawa zuwa "-e" ba. Ga rukunin da ba su cika canzawa ba ko da akwai postposition:
Mata (Feminine Nouns): Kalmomin mata masu karewa da "-i" ba sa canzawa.
Misali: Larki (Yarinya) -> Larki ko (Ga yarinyar). Ba ta komawa "Larke".
Maza (Masculine) wadanda ba su karewa da "-a":
Misali: Ghar (Gida) -> Ghar mein (A cikin gida). Ba ya komawa "Ghare".
Taฦaitaccen Rahoto
Ka tuna wannan dabarar:
Suna (mai karewa da -A) + Postposition = Canji zuwa -E.
Idan babu postposition, kalmar tana nan a asalin ta (Angna). Idan akwai postposition, tana komawa (Angne).