26/05/2020
NASIHAR WATA UWA GA DANTA AZAMANIN INTERNET.
Daga malama Aisha isah.
Wata 'uwa tayiwa danta wasiyya azamanin fitinar internet, ya cancanta a rubuta ta da ruwan zinari.
Tace ya dana, kasani goggle, da Facebook da twitter da sauran kafofin sadarwa na zamani wani teku ne mai zurfi, mazaje sun tozartar da halayensu nagari acikinshi!! Sun kuma jefa hankulansu acikin wannan rafi.!!
Daga cikin wadanda s**a nutse akwai matasa, da masu furfura. Tabbas halittu da yawa sun bata acikinsa.
Ya dana.!! Kayi hattara sosai, ka kasance acikin sa kamar kudan zuma, bata dirawa akan kowane abu sai mai tsafta da tsarki. Kaima ya dana karka duba wani shafi face mai kyau wanda zaka amfani kanka a karon farko sannan ka yada ga sauran mutane.
Ya dana.!! Karka yarda kazama kamar kuda, yana fadawa a abu mai kyau da marar kyau, yayita yada cuta batareda yama tantance ba.!!
Ya dana.!! Internet kamar wata katuwar kasuwa ce, kuma babu wanda zai dinga raba kayansa kyauta, kowanne yanaso wani sakamako ya biyo baya.
Daga cikin masu kasa kaya a wannan kasuwa akwai masu burin bata tarbiya.
Akwai mai son raba tunani da akidarsa na banza.
Daga cikinsu kuwa akwai masu kokarin gyara tarbiya da saita al'umma akan daidai.
Don haka kada ka gajiya ya dana ka nemi abokai nagari acikin wannan kasuwa.
Ya dana.!! Kafin kayi comment ko like din wani Abu kayi tunani, shin zai yardar da Allah ko zai gadarma fushinsa.
Ya dana.!! Kada ka yi cikakken yadda akan zahirin abinda kagani daga mutane a internet.
Akan samu mai wayo amma shine mafi sakarcin mutane.
Akan samu kyakkyawa amma shine mummunan mutane.
Akan samu mai karamci amma shine mafi rowan masu rowa.
Akan samu jarumi alhalin babban matsoraci ne.
Saidai wanda Allah T yayiwa rahama, to ka kasance cikin wadanda Allah yayiwa rahaman.
Ya dana.!! Kaji tsoron mutane masu aro sunaye, haqiqa akwai mutane masu aro sunaye da shiga rigar manyan mutane, wasu kuma suyi amfani da sunan mata alhalin maza ne, wasu matan suyi amfani da sunan maza alhalin mata ne. Idan kaga kalan wadannan mutane masu aron suna kagudu daga garesu, saboda suma basu yadda da Kansu ba, ya za'ayi kuwa kai ka yadda da wanda bai yadda da kansa ba.
Ya Dana.!! Kashedinka karka ari sunan kowa, domin Allah yasan abinda ke boye da wanda aka bayyana.
Ya dana.!! Kada ka munana wa wanda ya munana maka, shi abinda gareshi yake fitarwa, kai karka yadda abinda ke gareka yazama mummuna irin nasa, kowace kwarya ai abinda ke cikinta take zubarwa.
Ya dana.!! Ka kula da abinda kake rubutawa, kana rubutu ne suma mala'iku suna rubutu, Allah T kuma yana saman bakwai yanaji yana gani.
Ya Dana!! Mafi girman abinda nafi jiye maka tsoro a tekun internet shine kallon haram!! Da kallon fajirci da karkatattun mutane, idan kasamu kanka ka'iya kubuta daga sharrin wadannan, to kayi farinciki ka amfana da mutanen kirki kaima ka amfanar kuma kayada addinin ka, idan kuma kakasa kubuta daga sharrin fajirai da fandararru, to kagudu daga duniyar internet irin gudun da zakayi idan yunwatacciyar kura ko damisa ta rutsaka.
Ya dana.!! Kasani mafi nasaran da shaidan keci a wurin dan Adam a lokacin gafala ne da sha'awa, kuma gafalan da sha'awan sune ginshikan internet...
Babban abinda yakamata kasani shine wadannan kofofin sadarwa ba'a yisu don su gafalar dakaiba anyisu ne donsu amfaneka.
Don haka kayi amfani dashi karka yadda shi yayi amfani dakai.
Ka gina dashi, kada ka yarda shi ya rusa ka.
Ya Dana.!! Ka sanya internet yazama hujja gareka ba hujja akanka ba, kazama mai amfani da amfanarwa ba mai cutarwa da cutuwa ba.
Muna rokon Allah dacewa Ameeeeeeeeeen.