21/01/2026
💫KOWA YAKI JI💫
PAGE 2️⃣1️⃣
Wani irin kakari na shiga saboda tsananin shaƙar daya min, ina ta ƙoƙarin sa hannu na ɓanɓare hannun shi daga wuyana, kalmar daya faɗa ce ta rusa duk wani kuzari na da ƙarfin gwiwata.
"Salmah kije na sake ki saki ɗaya, kuma ki ajiye min yarana ki fita ki barmin gida, duk inda zaki kije."
Ya ƙarasa maganar tare da hankaɗa ni baya, na faɗi ƙasa, ya tsallake ni tare da nufar ɗakin sa ya banko ƙofar da ƙarfi.
Gaba ɗaya ji nayi duniyar na juya min, komai ganin sa nake tamkar a mafarki, tun lokacin daya furta kalmar saki komai ya kunce min iya kalmar na sake ki saki ɗaya ce kawai ke amsa amo a kunne na.
Ban taɓa kawowa raina cewa duk rintsi Haidar zai sake ni ba, na ɗauka ko ba komai zai tausaya min dan yafi kowa sanin bani da inda yafi gidan shi.
Ina zanje? na tambayi kaina. "Ban sani ba" na bawa kaina amsa a fili. har lokacin na kasa tantance komai ina zaune k**ar wadda aka dasa.
Bansan adadin lokacin dana ɗauka anan zaune ba, sai ga Haidar ya ƙara ftowa, da alama wanka ya sake dan ya canja kayan shi sai baza ƙamshi yake, hannun sa riƙe da mukullin motar shi.
Sai da ya watsa min wani Mummunan kallo, tukun cikin kakkausar murya ya nuna ni da hannu "Wallahi Wallahi na dawo gidan nan na tarda ki, sai na baki matuƙar mamaki babu komai tsakanina dake yanzu ki tattara ki bar min gidana, kuma na faɗa miki karki ɗaukar min yaro ko ɗaya ki aje min yarana zan bawa wadda zata kula min da su."
Idanuna gaba ɗaya sun soye babu alamar kuka ko kaɗan, sai zuciyata dake min wani irin azababben zafi sai bugawa take k**ar zata faso k'irjina.
Fuskar Haidar kawai nake kallo na kasa janye idanuna sam, hatta tsoron shi da nake ji sai na nemi shi na rasa kwata kwata, ina kallo ya tsallake ya fice yana tafiya cikin izza da ƙarfi irin na cikakkun maza masu ji da kansu.
A hankali na ɗauke kaina daga bakin ƙofar farlon, jin ƙarar tashin motar shi alamar ya fita.
Na sauke idanuna akan su Salim da tun fara abin s**a takure waje guda saboda tsorata.
Har lokacin N